| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Nijeriya ta kama mutum takwas bisa zargin safarar hodar iblis zuwa Turai ta Hamadar Sahara
Hukumar NDLEA ta ce ta kama waɗanda ake zargin ne a yayin samamen da ta gudanar bisa bayanan sirri a Legas da Kano tsakanin ranakun 30 da 31 ga Oktoba.
Nijeriya ta kama mutum takwas bisa zargin safarar hodar iblis zuwa Turai ta Hamadar Sahara
NDLEA / Nigeria NDLEA

Hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Nijeriya ta kama mutum takwas da ake zargin suna cikin wata ƙungiyar safarar hodar iblis daga Legas ta Kano, zuwa Turai ta hamadar Sahara, ta Jamhuriyar Nijar da Libya.

Hukumar NDLEA ta ce ta kama waɗanda ake zargin ne a yayin samamen da ta gudanar bisa bayanan sirri a Legas da Kano tsakanin ranakun 30 da 31 ga Oktoba.

Samamen ya fara ne da kama wani mutum mai shekara 57 mai suna Okwudiba Ifeanyichukwu Damian a wani otal da ke Legas.

Daga bisani, ya fitar da ƙwayoyin hodar iblis 74 masu nauyin kilogiram 1.65 ta bayan gida, a cewar hukumar.

Washegari, jami’an hukumar sun kama wasu mutum huɗu a sashen jiragen cikin gida na filin jirgin saman Legas, yayin da suke shirin hawa jirgin da zai kai su Kano.

Mutum biyar ɗin da aka kama a Legas sun fitar da ƙwayoyin hodar iblis 399 masu nauyin kilogiram 8.655 baki ɗaya.

Bayanan da aka samu daga samamen Legas sun taimaka wa jami’an hukumar wajen gano wasu mutum uku a filin jirgin saman Kano. Binciken na'urar hoton cikin jiki ya nuna cewa su ma sun haɗiye ƙwayoyin hodar iblis.

A cewar hukumar NDLEA, mutanen takwas sun fitar da ƙwayoyin hodar iblis 634 masu nauyin kilogiram 13.795 gaba ɗaya cikin kwanakin da suka shafe a tsare.

Waɗanda ake zargin sun shaida wa masu bincike cewa sun shirya jigilar miyagun ƙwayoyin ta mota daga Kano, ta Jamhuriyar Nijar da Libya, zuwa Turai.

Legas na daga cikin manyan cibiyoyin safarar hodar iblis a Afirka ta Yamma, inda masu safarar miyagun ƙwayoyi ke amfani da ita wajen jigilar hodar iblis daga Kudancin Amurka zuwa kasuwannin Turai.