| Hausa
TATTALIN ARZIKI
3 minti karatu
Ghana ce ƙasa ta takwas mafi girman tattalin arziki a Afirka, ta biyu a Yammacin Afirka - Mahama
Jimillar kuɗaden da tattalin arzikin Ghana ya samar na (GDP) ya kai kusan dala biliyan 114 a shekarar 2025, matakin da ya sanya ƙasar zama ta takwas mafi girman tattalin arziki a Afirka, sannan ta biyu a yankin Afirka ta Yamma, in ji shugaba Mahama.
Ghana ce ƙasa ta takwas mafi girman tattalin arziki a Afirka, ta biyu a Yammacin Afirka - Mahama
Ghana ta zama ƙasa ta takwas mafi girman tattalin arziki a Afirka, sannan ta biyu a Yammacin Afirka, a cewar Shugaba John Mahama. / TRT Afrika Hausa

Shugaban ƙasar Ghana, John Dramani Mahama, ya bayyana cewa ƙasarsa na samun ci gaba wajen zama ɗaya daga cikin ƙasashen da tattalin arzinkinsu yake girma a Afirka, yana mai danganta hakan da raguwar hauhawar farashi, da ƙarin ajiye kuɗaɗen waje da kuma farfaɗo da amincin masu zuba jari.

Da yake jawabi a wajen buɗe taron zuba jari na Ghana na shekarar 2026, wanda aka gudanar a birnin Accra a ranar Litinin, 16 ga Nuwamba, Mahama ya ce sauye-sauyen tattalin arzikin da aka aiwatar sun taimaka wajen dawo da daidaiton manyan ma'aunan tattalin arziki tare da sanya ƙasar da yake yakin Yammacin Afirka a kan turbar samun ci gaba mai ɗorewa.

Ya ce jimillar kuɗaden da tattalin arzikin Ghana ya samar na (GDP) ya kai kusan dala biliyan 114 a shekarar 2025, matakin da ya sanya ƙasar zama ta takwas mafi girman tattalin arziki a Afirka, sannan ta biyu a yankin Afirka ta Yamma.

Kazalika, a cewar shugaban, Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF) ya yi hasashen cewa kuɗaɗen GDP na Ghana zai kai dala biliyan 128.64 kafin ƙarshen shekarar 2026, yayin da ake sa ran tattalin arzikin zai bunƙasa da kashi 5.7 cikin ɗari.

Masu AlakaTRT Afrika - Asusun adana zinari na Ghana ya kai ton 31.37 a watan Afrilun 2025

Shugaba Mahama ya ce hauhawar farashi a Ghana ta ragu sosai, daga kashi 23.5 cikin ɗari a watan Janairun 2025 zuwa kashi 5.5 cikin ɗari a watan Oktoban 2026, abin da ya taimaka wajen rage matsin tattalin arziki ga 'yan kasuwa da masu sayayya.

Ya kuma bayyana cewa ajiyar kuɗaɗen waje na ƙasar ta kai dala biliyan 12.05 a watan Satumban 2026, adadin da zai iya biyan kuɗin shigo da kayayyaki daga ƙasashen waje na tsawon watanni 4.5.

A cikin watanni takwas na farkon shekarar 2026, Ghana ta samu rarar cinikayya ta dala biliyan 8.86, yayin da ma'aunin kasafin kuɗin farko na gwamnati ya samu rarar kashi 1.6 cikin ɗari na GDP.

A cikin watanni takwas na farkon shekarar 2026, Ghana ta samu rarar cinikayya ta dala biliyan 8.86, yayin da ma'aunin kasafin kuɗin farko na gwamnati ya samu rarar kashi 1.6 cikin ɗari na GDP.

Shugaban ya ƙara da cewa kuɗin ƙasar Cedi, ya kara ƙarfi da kashi 40.7 cikin ɗari aka dalar Amurka a shekarar 2025, sannan ya ci gaba da kusan kashi bakwai cikin ɗari a watan Satumban 2026 idan aka kwatanta da makamancin lokacin a bana.

Bayanan Babban Bankin Ghana sun kuma nuna cewa tattalin arzikin ƙasar ya bunƙasa da kashi 6.4 cikin ɗari a zangon farko na shekarar 2026, sakamakon ci gaban da aka samu a ɓangarorin ayyuka da masana'antu.

Masu AlakaTRT Afrika - Ghana ta kaddamar da sabuwar takardar kudi ta Cedi