| Hausa
WASANNI
2 minti karatu
Masu adawa da Infantino sun yi barazanar gudanar da gasar kofin duniya ba a karkashin FIFA ba
Yayin da saɓani tsakanin shugaban FIFA, Gianni Infantino, da hukomomin ƙwallon ƙafa na nahiyoyin duniya ke ƙaruwa, wata barazana ta ɓullo game da gasar kofin duniya.
Masu adawa da Infantino sun yi barazanar gudanar da gasar kofin duniya ba a karkashin FIFA ba
Zuwa yanzu Gianni Infantino ya shekara 10 yana jagorantar FIFA, tun daga 2016.

Hukumar ƙwallon ƙafa ta nahiyar Turai, UEFA, ta fara haɗa gwiwa da hukumomin ƙwallon ƙafa na sauran nahiyoyi domin tursasa wa shugaban hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya, FIFA ya yi murabus.

UEFA da abokan ƙawancen da ke adawa da shugaban FIFA, Gianni Infantino, sun yi barazanar ƙaddamarwa tare da gabatar da gasar kofin duniya ba a ƙarƙashin FIFA ba, kamar yadda aka saba cikin kusan shekaru 100 da suka wuce.

Rahotanni sun ambato shugaban UEFA, Aleksander Ceferin tare da jami’an hukumar ƙwallo ta nahiyar Amurka, CONCACAF da ta nahiyar Asiya, suna ƙoƙarin tursasa wa Infantino ya yi murabus.

Wannan ya tabbatar da yadda sabon ƙawancen da aka ƙulla a duniyar ƙwallo yake girmama domin kawar da Infantino.

Sharaɗin da suka saka wa Infantino shi ne ya ajiye aiki, sakamakon yunƙurin da ya yi na sayar da hannun-jarin gasar kofin duniya ga ‘yankasuwa, duk da cewa ya janye bayan samun kakkausar suka.

Mai shekaru 56, Infantino ya shekara 10 yana shugabantar FIFA, kuma a halin yanzu yana neman sabon wa’adin jagoranci a zaɓen watan Maris na baɗi.

Gangamin tursasawa

Matuƙar Infantino ya dage kan ci gaba da mulki har ma ya nemi sabon wa’adi, to ƙawancen zai duba yiwuwar shirya nasa gasar duniya nta maza, wadda ita ce babbar gasar duniya wadda ake gudanarwa duk bayan shekaru huɗu, ƙarƙashin inuwar FIFA.

Tuni dai da ma UEFA take da wani shiri na ƙaddamar da wata gasar ƙasashen duniya da za ta yi gogayya da gasar Kofin Duniya. Hakan ya samo asali ne a 2017 lokacin da suka ƙuduri aniyar aiwatar da wannan tunani.

Bugu da ƙari, masu adawa da Infantino suna shirya wata dabarar ta ƙauracewa tarukan Majalisar FIFA da kwamitocinta, tare da ƙin lamuncewa da duk matakan da aka ɗauka.

Zuwa yanzu bayan da Infantino ya yi amai ya lashe, hukumomin ƙwallo na ƙasashe 15 kacal ne suka nuna goyon baya gare shi cikin jimillar ƙasashe 211 mambobin FIFA.

Hasali ma, hukumar ƙwallo ta Ingila ta bi sahun takwararta ta Wales wajen janye goyon baya ga Infantino, gabanin zaɓen shugabancin FIFA na baɗi.

A yanzu Ingila da sauran hukumomin ƙwallon za su ƙaurace wa gasar Kofin Duniya mai zuwa idan har shirin Infantino ya samu karɓuwa a taron, cewar UEFA.

Haka nan akwai batun ɗaukar matakin shari’a kan jami’an FIFA idan matsalar ta ci gaba da yin ƙamari.

Rumbun Labarai
Messi na shirin buga wa Argentina wasansa na ƙarshe
Masu ruwa da tsaki a ƙwallon ƙafar Nijeriya na taron tattauna hanyoyin kawo gyara
Falconets ta Nijeriya ta lallasa New Caledonia da ci 10-1, ta kai zagayen gaba a gasar Kofin Duniya
'A Maroko za a yi wasan ƙarshe na Kofin Duniya na 2030', in ji shugaban hukumar ƙwallon kasar
'An yi wa Arsenal fasha a wasansu da Aston Villa', in ji hukumar gasar Firimiya
NFF ta naɗa Eguavoen a matsayin kocin wucin-gadi na Super Falcons
An manta da Raphinha da Pedri cikin 'yanwasa 30 da za su iya lashe kyautar Ballon d'Or
Barcelona ta miƙa ƙoƙon-bara wajen masu zuba jari don neman kuɗin gyaran filin wasa
Turkiyya ta kuma lashe kofin gasar volleyball ta mata ta nahiyar Turai
An yanke wa Tiger Woods hukuncin haramcin tukin mota tsawon shekaru 5 saboda tuki cikin maye
Muhimman batutuwa game da ritayar Messi daga tawagar Argentina
Sakon Lionel Messi na yin ritaya daga buga kwallo a matakin kasa-da-kasa
"Jikina ya fara sakwarkwacewa" in ji Djokovic, bayan an fitar da shi daga Gasar US Open ta bana
Shugaban Hukumar Ƙwallon Ƙafar Nijeriya Musa Gusau ya yi murabus
Ɗanwasan Kamaru Carlos Baleba ya koma Man Utd daga Brighton
Habasha ta shiga takarar ɗaukar nauyin gasar AFCON ta 2028
An sayar da ƙwallon da Maradona ya ci Ingila da hannu a kan $3.35M
Ɗan Nijeriya Semi Ajayi ya taimaka wajen yi wa Man Utd dukan wulaƙanci a farkon Gasar Firimiya
Cristiano Ronaldo ya fara kakarsa ta 25 da ƙwallonsa na 977 a tarihin wasansa
EFCC ta fara binciken Hukumar kwallon kafa ta Nijeriya, NFF