| Hausa
WASANNI
3 minti karatu
FIFA ta gaza hukunta Isra'ila kan karya dokokinta, a cewar hukumar Kwallon Kafa ta Falasɗinu
Sanarwar Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Falasɗinu ta zo ne a daidai lokacin da wani rahoton jaridar The Athletic ya nuna cewa Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Ingila za ta janye goyon bayanta ga shugaban FIFA, Gianni Infantino da ke neman sake tsayawa takara.
FIFA ta gaza hukunta Isra'ila kan karya dokokinta, a cewar hukumar Kwallon Kafa ta Falasɗinu
Infantino, mai shekaru 56, ya riƙe muƙamin shugabanci FIFA ne tun daga watan Fabrairun 2016 kana yana neman sake tsayawa takara a shekara mai zuwa.

Hukumar Kwallon Kafa ta Falasdinu (PFA) ta ce FIFA ta gaza aiwatar da dokokinta kan Isra'ila, tana mai zargin hukumar da rashin ɗaukar mataki na tsawon shekaru duk da cewa Tel Aviv ta durƙusar da harkokin ƙwallon ƙafa a Falasɗinu.

A wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin, PFA ta ce an kashe 'yanwasa da kocina da alƙalan wasa da jami'ai da kuma mambobin ƙungiyar kwallon kafa ta Falasɗinu fiye da 1,013 a lokacin kisan ƙare-dangi da Isra'ila ta aikata a Gaza, yayin da aka lalata filayen wasa da wuraren horas da ‘yanwasa da muhimman ababen more rayuwa na ƙwallon kafa.

PFA ta kuma soki FIFA saboda gaza ɗaukar mataki kan ƙungiyoyin ‘yan kama-wuri-zauna na Isra'ila a yankin Falasɗinu da ta mamaye.

Ta ce har yanzu ba a warware ƙorafe-ƙorafen da ta yi fiye da shekaru 15 ba.

"Shiru, idan ana aikata kisan ƙare-dangi kai-tsaye, yana nufin haɗa baki," in ji PFA, tana mai ƙari da cewa hukumar ƙwallon ƙafa ta Falasdinu "ba za ta iya ci gaba da ɗaukar alƙawuran da ba a cika su ba."

A bara, FIFA ta ce ba za ta haramta wa Isra'ila shiga gasar ƙasa da ƙasa ba saboda "ba za ta iya magance matsalolin siyasa ba," sanarwar da ta janyo suka mai zafi.

Masu AlakaTRT Afrika - UEFA ta sha alwashin ƙaurace wa FIFA idan aka ci gaba da shirin sayar da Gasar Kofin Duniya

Masoya ƙwallon ƙafa sun zargi FIFA da nuna sonka wajen ƙin haramta wa Isra'ila shiga harkokin ƙwallon ƙafa, yayin da a ɓangare guda ta haramta wa Rasha nan-take shiga gasanni saboda yaƙin da take yi a Ukraine.

Hukumar Kwallon Kafa ta Ingila za ta janye goyon bayanta ga Infantino

Yayin da matsin lamba ke ƙaruwa kan Gianni Infantino, jaridar The Athletic ta ruwaito cewa hukumar ƙwallon ƙafa ta Ingila za ta janye goyon bayanta ga sake zaɓen shugaban na FIFA.

A sanarwar da Hukumar ƙwallon ƙafa ta Ingila (FA) ta fitar, ta nuna rashin jin daɗinta ga Infantino bayan da ya yi watsi da yunƙurinsa na sayar da hannun-jari na kashi 21 cikin ɗari na harkokin kasuwanci da shirye-shiryen wasannin FIFA ga masu zuba jari da ke zaman kansa.

"Lokaci ya yi da za a yi cikakken nazari da garambawul ga jagoranci da kuma shugabancin FIFA don tabbatar da cewa ana gudanar da wasannin duniya cikin gasikya, don amfanin dukka ƙasashe mambobi 211 da kuma kula da martabar ƙwallon ƙafa na tsawon lokaci, ‘‘ a cewar sanarwar FA.

Infantino, mai shekaru 56, na riƙe muƙamin shugabancin FIFA ne tun daga watan Fabrairun 2016, sannan a yanzu yana neman sake tsayawa takara a shekara mai zuwa.

Ya tsaya takara ba tare da hamayya ba a 2019 da 2023.

Masu AlakaTRT Afrika - Masu adawa da Infantino sun yi barazanar gudanar da gasar kofin duniya ba a karkashin FIFA ba

Ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na Wales da Serbia duk sun sanar a ranar Litinin cewa za su janye goyon bayansu ga Infantino a hukumance.

"Muna so mu tunatar da ku cewa mun bai wa Mista Infantino goyon baya a rubuce a ranar 25 ga Mayu na wannan shekarar, amma bayan nazari kan abubuwan da suka faru waɗanda suka taba ƙimar FIFA da shugabanta a baya, wannan ita ce kawai matakin da ya dace da kuma mai ma'ana mu ɗauka," in ji Hukumar Kwallon Kafa ta Serbia (FSS).

Dole ne a gabatar da sunayen 'yan takarar da ke son kalubalantar Infantino kafin ranar 18 ga Nuwamba.

 Ana sa ran shugaban CONCACAF kuma mataimakin shugaban FIFA na yanzu Victor Montagliani zai yi amfani da damar da yake shi wajen maye gurbin Infantino.

Rumbun Labarai
Messi na shirin buga wa Argentina wasansa na ƙarshe
Masu ruwa da tsaki a ƙwallon ƙafar Nijeriya na taron tattauna hanyoyin kawo gyara
Falconets ta Nijeriya ta lallasa New Caledonia da ci 10-1, ta kai zagayen gaba a gasar Kofin Duniya
'A Maroko za a yi wasan ƙarshe na Kofin Duniya na 2030', in ji shugaban hukumar ƙwallon kasar
'An yi wa Arsenal fasha a wasansu da Aston Villa', in ji hukumar gasar Firimiya
NFF ta naɗa Eguavoen a matsayin kocin wucin-gadi na Super Falcons
An manta da Raphinha da Pedri cikin 'yanwasa 30 da za su iya lashe kyautar Ballon d'Or
Barcelona ta miƙa ƙoƙon-bara wajen masu zuba jari don neman kuɗin gyaran filin wasa
Turkiyya ta kuma lashe kofin gasar volleyball ta mata ta nahiyar Turai
An yanke wa Tiger Woods hukuncin haramcin tukin mota tsawon shekaru 5 saboda tuki cikin maye
Muhimman batutuwa game da ritayar Messi daga tawagar Argentina
Sakon Lionel Messi na yin ritaya daga buga kwallo a matakin kasa-da-kasa
"Jikina ya fara sakwarkwacewa" in ji Djokovic, bayan an fitar da shi daga Gasar US Open ta bana
Shugaban Hukumar Ƙwallon Ƙafar Nijeriya Musa Gusau ya yi murabus
Ɗanwasan Kamaru Carlos Baleba ya koma Man Utd daga Brighton
Habasha ta shiga takarar ɗaukar nauyin gasar AFCON ta 2028
An sayar da ƙwallon da Maradona ya ci Ingila da hannu a kan $3.35M
Ɗan Nijeriya Semi Ajayi ya taimaka wajen yi wa Man Utd dukan wulaƙanci a farkon Gasar Firimiya
Cristiano Ronaldo ya fara kakarsa ta 25 da ƙwallonsa na 977 a tarihin wasansa
EFCC ta fara binciken Hukumar kwallon kafa ta Nijeriya, NFF