| Hausa
NIJERIYA
3 minti karatu
Hare-haren sama na sojojin Nijeriya sun kashe 'yanta'addan ISWAP 21 a Borno
Binciken rundunar ya gano wasu 'yanta'adda ɗauke da makamai suna tafiya a wata hanyar daji a arewa maso gabashin garin, lamarin da ya sa aka kai musu hari ta sama, inda aka kashe mutum bakwai, ciki har da wasu daga cibiyar ƙera bama-bamai ta ISWAP.
Hare-haren sama na sojojin Nijeriya sun kashe 'yanta'addan ISWAP 21 a Borno
Rundunar sojin Nijeriya ta ce an kashe wasu mayaka 12, yayin da wasu biyar suka samu munanan raunuka. / Others

Rundunar sojin Nijeriya ta ce dakarunta sun kashe ‘yanta’addan ƙungiyar ISWAP 21 tare da jikkata 10 a wasu hare-hare da suka kai a Jihar Borno da ke arewa maso gabashin ƙasar.

Hare-haren, waɗanda rundunar sojojin sama ta haɗin gwiwa ta kai ƙarƙashin aikin rundunar Operation HADIN KAI, sun gudana tsakanin 16 zuwa 17 ga Nuwamban 2026, inda aka kai hari kan wasu wurare da ake zargin ‘yanta’addan ISWAP suna amfani da su a Monguno da kudancin Tafkin Chadi.

A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar a ranar Laraba, 18 ga Nuwamba, ta ce an gudanar da hare-haren ne bayan samun bayanan sirri da ke nuna cewa ‘yanta’addan ISWAP na shirin kutsawa yankin Monguno.

Binciken sa ido na rundunar ya gano wasu ‘yanta’adda ɗauke da makamai suna tafiya ta wata hanyar daji a arewa maso gabashin garin, lamarin da ya sa aka kai musu hari ta sama, inda aka kashe mutum bakwai, ciki har da wasu da ke aiki a cibiyar ƙera bama-bamai da ake dasawa a kan hanyoyi (IED) ta ƙungiyar.

Masu AlakaTRT Afrika - Wasu da ake zargi ’yan ISWAP ne da iyalansu sun miƙa wuya ga sojojin Nijeriya

A wani hari na daban da aka kai a Arinna da ke kudancin Tafkin Chadi, sojojin Nijeriya sun ce sun kashe ‘yanta’addan ISWAP da dama, lamarin da ya zama babban koma-baya ga tsarin shugabancin ƙungiyar.

Rundunar sojin ta ce Abba Bomma, wanda ya kware wajen kera abubuwan fashewa a kungiyar ISWAP, ya samu mummunar rauni tare da wasu 'yanta'adda hudu.

Kazalika wasu manyan 'yanta'addan ISWAP, ciki har da Mallam Sharki da Abu Saad, na cikin wadanda hare-haren jiragen saman suka kashe.

Rundunar sojin ta ce an kuma kashe wasu 'yan ta'adda 12 tare da jikkata wasu biyar sosai a harin. Haka kuma, an lalata babura da dama mallakin kungiyar.

A cewar rundunar, hare-haren biyu sun yi sanadin kashe 'yan ta'addan ISWAP 21 tare da jikkata wasu 10 sosai.

Kazalikam ta ce hare-haren sun raunana tsarin shugabancin ƙungiyar, tare da tarwatsa cibiyar  ƙera bama-bamanta, da kuma rage ƙarfinta kai hare-hare a yankin.

Kwamandan rundunar ayyukan soji a yankin ya ce za su ci gaba da matsin lamba kan kungiyoyin masu dauke da makamai har sai an dawo da zaman lafiya da harkokin yau da kullum a yankin na arewa maso gabashin Nijeriya.

Ya kuma bukaci mazauna yankin da su ci gaba da bai wa

Ya kuma bukaci mazauna yankin da su ci gaba da bai wa jami'an tsaro sahihan bayanai cikin lokaci domin taimakawa ayyukan yaki da ta'addanci.

ISWAP, wadda ke da alaka da kungiyar ta'addanci ta Daesh, na ci gaba da zama babbar barazana ga tsaro a arewa maso gabashin Nijeriya, musamman a jihar Borno da yankunan da ke kewaye da tafkin Chadi.