Ana fama da karancin kayayyakin abinci da ruwan sha a Gaza sakamakon hare-haren Isra'ila. / Hoto: Reuters

1550 GMT — Yunwa da kishirwa na yi wa Falasdinawa 500,000 barazana

Falasdinawa dubu 500 ke cikin barazanar yunwa da kishirwa a biranen da hare-haren Isra’ila ke kara karuwa, kamar yadda gwamnatin Gaza ta bayyana.

Gwamnatin ta Gaza ta ce jama’ar birnin na cikin bala’i sakamakon dagangan Isra’ila ke kai hare-hare kan ababen more rayuwa da ke da alaka da abinci da ruwa.

Mai magana da yawun birnin, Hosni Muhanna ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu a ranar Asabar cewa karancin man fetur yana kawo cikas wurin kwasar wadanda suka samu rauni da kuma jigilar gawawwaki.

1025 GMT — Isra'ila na ci gaba da zafafa hare-hare a Gaza bayan Amurka ta ki amincewa da kudurin

Isra’ila ta ci gaba da zafafa kai hare-hare a Gaza bayan Amurka ta yi fatali da kudurin da aka gabatar ga Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya wanda zai bayar da dama a tsagaita wuta a hare-haren da Isra'ila take kaiwa Gaza.

Hamas da hukumomin Falasdinu sun yi Allah wadai da wannan matakin na Amurka a daidai lokacin da ma’aikatar lafiya ta Gaza ta sanar da cewa mutum 17,487 suka mutu a Gaza, akasari mata da yara.

Haka kuma wani hari da Isra’ila ta kai a kudancin birnin Khan Yunis ya kashe mutum shida, inda wasu biyar suka mutu a wani hari na daban a Rafah, kamar yadda ma’aikatar ta tabbatar a ranar Asabar.

AA
AFP
AP
Reuters