Yaran Falasɗinawa da hare-haren Isra'ila suka raba da matsugunansu a Gaza kenan yayinda suke tafiya a kusa da sansanin 'yan gudun hijira na Kerem Shaom da ke Rafah. / Hoto: AP

An samar da tantunan a gaɓar tekun Gaza da ke da tsayin kilomita 16, wanda hakan ya sanya wuraren hutawa suka zama kamar kufai. Iyalai na haka ramuka don samar da masai. Iyaye na neman abinci da ruwa, yayin da yara ƙanana kuma ke yawon bola da gine-ginen da suka rushe don ɗiban katakon da aka lalata su kai wa iyayensu su dafa abinci.

A makonni uku da suka gabata, hare-haren Isra'ila a Rafah sun kori kusan Falasɗinawa miliyan guda daga kudancin Gaza inda suka warwarstu a yankuna daban-daban.

An riga an raba mafi yawa da matsugunansu a lokuta daban-daban a tsawon watanni takwas da Isra'ila ta ɗauka tana kai hare-hare Gaza, wanda hakan ya rikita yankin zuwa ga abinda majalisar Dinkin Duniya ta kira rikicin yunwa.

Yanayin ya munana saboda mummunan ƙarancin abinci da ake fuskanta, da kuma yadda abinci da man fetur isasshe ba ya isa ga Majalisar Dinkin Duniya da sauran ƙungiyoyin bayar da agaji. Kusan za a ce Falasɗinawa da kansu suke kwashe iyalansu tare da neman abinda za su ciyar da su.

"Yanayin ya tsananta. Kana da mutane 20 a tanti ɗaya, babu ruwa mai tsafta, babu lantarki. Ba mu da komai," in ji Mohammad Abu Radwan, malamin makaranta da ke cikin wani tanti tare da matarsa da yara shida, da ma sauran danginsa.

"Ba zan iya bayyana yadda na ke ji ba, kana cikin rasa wajen zama a koyaushe kana kuma rasa 'yan uwanka," in ji shi. "Duk wannan abu na rusa ƙwaƙwalenmu."

Abu Radwan ya gudu daga Rafah bayan da Isra'ila ta fara kai hare-hare a garin a ranar 6 ga Mayu inda bama-bamai suka faɗa kusa da gidansu da yake zaune.

Shi da wasu 'yan gidansu su uku sun biya $1,000 ga masu kekunan dawaki don su auɗke su zuwa Khan Younus, yanki mai nisan kusan kilomita 6, inda a nan ma sai da suka kwana a waje kafin su samu damar tattara kayan da suka haɗa tantin kwana. Sun kuma haka masai a kusa da tantin, suna rataya barguna da tsoffin kayan sa wa don kare kansu.

Iyalai na sayen katako da tamfo don samar da tanti, wanda na iya kaiwa har $500, ban da igiya da ƙusa da kudin dakon kayan, in ji Ƙungiyar Bayar da Agaji ta Mercy Corps.

Da yawan mutane a Gaza ba sa samun albashi na tsawon watanni, kuma 'yan kuɗaɗen da suka tara sun kare. Ko waɗanda suke da kuɗin ma a bankuna ba sa iya cira saboda babu tsabar kuɗi a yankin. Da yawa na komawa amfani da kasuwar bayan fage dake karbar har kusan kashi 20 ladan aika kuɗi zuwa asusun banki, su kuma su karbi tsaba.

A yayin da hakan ke afkuwa, jerin gwanon motocin bayar da agaji na MDD da sauran ƙungiyoyi dake raba kayayyaki kyauta sun ragu sosai a lokacin yaƙin, in ji MDD.

Alƙaluman baya-bayan nan da suka fito daga Hukumar Jin Ƙai ta MDD OCHA a ranar Juma'a na bayyana cewa suna karɓbar motocin abinci 53 a kowacce rana. Ana kuma bukatar a kalla motoci 600 kullum don yaƙar barazanar yunwa a yankin, in ji USAID.

A makonni uku da suka gabata, mafi yawan taimakon da ke zuwa yana shiga yankin daga bangarori biyu a arewacin Gaza ta hanyar teku da Amurka ta samar. Sai kuma hanyar shiga yankin ta kudu, Rafah daga Masar da Kerem SHalom daga Isra'ila, waɗanda dukkan su ba sa aiki a yanzu haka.

Shigar da man fetur ya ragu sosai zuwa ga kashi ɗaya cikin uku na abin da ya kamata a dinga kaiwa, in ji OCHA. Wanda ake samun ana ajiye shi don amfani a asibitoci da gidajen burodi da rijiyoyi da motocin bayar da agaji.

Kungiyar bayar da agaji ta Amurka mai suna Anera na shan wahala wajen rarraba kayan taimako saboda babu mai a motocin da suke ɗauke da kayan, in ji Steve Fake, kakakin kungiyar.

'Ba ka iya tafiya'

Mafi yawan masu guje wa Rafah sun kwarara zuwa yankin bayar da agaji da Isra'ila ta ware wanda ke a al Mawasi, wani yankin gaɓar teku mara albarka. An faɗaɗa yankin zuwa arewa da yammacin Khan Younus da kuma tsakiyar garin Deyr al-Balah, dukkan su biyun sun cika da mutane.

"Kamar yadda muke gani, babu wani aikin jin ƙai a wannan yanki," in ji Suze van Meegan, shugabar ayyuka a Gaza ta Kungiyar Kula da 'Yan Gudun Hijira ta Norway, wadda ke da ma'aikata a al Mawasi.

Mafi yawan yankin bayar da agajin jin kan ba su da ɗakunan dafa abinci ko kasuwannin sayar da kayan abinci, babu asibitoci dake aiki, sai wasu 'yan kaɗan da ke ayyuka a fili ba tare da gini ba da kuma 'yan tantunan da ke duba marasa lafiya suna ba su 'yan magunguna idan har suna da su, in ji Mercy Corps.

"Magana ake yi kawai ta lokaci kafin mutane su fara galabaita saboda ƙarancin abinci." in ji ƙungiyar.

Yankin Muwasi gabar teku ce da ba ta da albarkatun ruwa ko magudanan ruwa. A yayin da ake zubar da bayan gida a kusa da tantunan, sannan ga bola a wajen, mutane da dama na shan wahala daga cututtukan ciki irin su gudawa da ciwon hanta, da ma cututtukan fata, in ji Mercy Corps.

Wani ma'aikacin jin ƙai da ya gudu daga Rafah ya ce ya yi sa'a ya iya kama gidan haya a Deyr al-Balah. "Ba za ka iya magana ba" a garin akwai tantuna da dama, in ji shi, a yayin da yake magna tare da neman a ɓoye sunansa saboda ƙungiyarsa ba ta ba shi damar magana ba.

Mutane da dama da yake gani a kan tituna na fama da cutar hanta ko shawara, kuma akwai mummunan wari da doyi dake fitowa daga kwatami da tarin bola.

Yaƙin Isra'ila a Gaza da aka fara a ranar 7 ga Oktoba bayan harin da Hamas ta kai, ya yi sanadiyyar mutuwar Falasdinawa sama da 36,000, mafi yawan su mata da yara kanana, kamar yadda ma'aikatar Lafiya ta Gaza ta sanar.

Kungiyoyin agaji sun yi gargaɗi na tsawon watanni cewa hari kan Rafah na iya ƙara rura wutar bala'i da halin da ake ciki a Gaza.

Ya zuwa yanzu, hare-haren isra'ila na ci gaba tun makonni uku da suka gabata, daga gabashin Rafah zuwa gundumar tsakiya.

Wani hari a ranar Lahadi ya faɗa kan sansanin Falasɗinawa a yammacin Rafah, harin ya janyo gobara da kashe akalla mutane 45, kamar yadda jami'an lafiya suka sanar.

Hotunan da tauraron ɗan adam ya ɗauko a makon da ya gabata sun nuna daɗuwar tantuna a gabar tekun, tun daga arewacin Rafah zuwa wajen Deyr al Balah.

Tamer Saeed Abul Khayr ya ce yana fita waje da karfe 6 na safe kowacce rana don neman ruwan sha, yana dawo wa da rana zuwa tantin da ke Khn Younus inda shi da kusan gomman mutane ke rayuwa.

Yaransa guda uku a ke da shekaru tsakanin 4 zuwa 10 na fama da rashin lafiya a koyaushe, amma ya ce ya zamar masa dole ya aika su nemo kiraruwan dafa abinci, duk da yana tsoron kar su je su gamu da bam ɗin da aka dasa a gidajen da aka rusa.

Mahaifinsa da shekaru suka cimma na yin wanka da bokiti, kuma baul Khayr na biyan kudin mota a koyaushe don kai shi wankin koda asibiti.

"Itacen girki na da tsada, ruwa na da tsada, komai ma ya tashi, " in ji matarsa Leena Abul Khayr. Ta yi ajiyar zuciya tana mai cewa "Ina tsoron wata rana zan farka ya zama na rasa yarana, mahaifiyata, mijina da iyalina."

TRT World