Harin na Isra'ila ya rusa gidan tare da lalata gidajen da ke maƙotaka . / Hoto: AA

Talata, 10 ga watan Disamba, 2024

1102 GMT — Adadin mutanen da suka rasa rayukansu a hare-haren da sojojin Isra'ila suka kai a Gaza tun daga ranar 7 ga watan Oktoban 2023, ya karu da 28 a cikin sa'o'i 24 da suka wuce, inda yawan ya kai 44,786.

A cikin wata sanarwa da Ma'aikatar Lafiya ta Falasdinu a Gaza ta fitar, an bayar da bayanai dangane da hare-haren da Isra'ila ke kai wa Gaza tsawon kwanaki 431.

An bayar da rahoton cewa, mutume 28 ne suka rasa rayukansu kana wasu 54 kuma suka samu raunuka sakamakon kisan kiyashi hudu da sojojin Isra'ila suka yi a sassa daban-daban na Gaza cikin sa'o'i 24 da suka gabata.

An yi kiyasin cewa adadin mutanen da suka rasa rayukansu a hare-haren da Isra'ila ke kaiwa Gaza tun daga ranar 7 ga watan Oktoban 2023, ya karu zuwa 44,786 sannan adadin wadanda suka jikkata ya karu zuwa 106,188.

0705 GMT — Isra'ila ta yi luguden wuta a sansanin 'yan gudun hijira na Nuseirat da ke Gaza

Dakarun Isra'ila sun kashe Falasɗinawa bakwai, ciki har da wata mata da 'ya'yanta uku tare da jikkata gommai a hari ta sama da suka kai da sanyin safiya a sansanin 'yan gudun hijira na Nuseirat da ke tsakiyar Gaza.

A wata sanarwa da ta fitar, rundunar kare fararen-hula ta yankin ta ce tawagarta ta gano gawawwakin mutanen bakwai a gidan iyalan "Khalifa" da ke sansanin na Nuseirat.

Wata majiya daga asibitin al-Awda ta ce an kai mutanen, ciki har da wata mata da 'ya'yanta, asbitin tare da waɗanda suka jikkata.

Kazalika harin na Isra'ila ya rusa gidan tare da lalata gidajen da ke maƙotaka, a cewar wasu ganau da suka yi hira da kamfanin labarai na Anadolu.

Ƙarin bayani 👇

2300 GMT — Isra'ila ta kashe Falasɗinawa 25 a arewacin Gaza

Sojojin Isra'ila sun kashe iyalan Falasɗinawa biyu bayan sun yi luguden wuta a gidansu a garin Beit Hanoon da ke arewacin Gaza.

"Sojojin Isra'ila sun yi luguden wuta a wani gida da iyalai biyu 'yan ƙabilar Al-Kahlout, inda mutum 25 suke zaune, inda ginin ya rufta akansu," a cewar ɗaya daga cikin 'yan'uwansy mai suna Abdel Rahman Al-Kahlout.

"Isra'ila ta sake gudanar da kisan kiyashi, inda ta kashe iyalai biyu gaba ɗaya," in ji shi.

Ya ƙara da cewa har yanzu gawarwakin suna ƙarƙashin ɓaraguzai saboda hatsarin da ke tattare da zuwa ɗebo su.

TRT World