Hawaye na zuba daga idanun Mohammed al Sabbagh, a daidai lokacin da yake ihu cikin rudani a wayar da ke hannunsa, yana rokon 'yar'uwarsa da ke daya bangaren kan ta ''jajirce'' yayin da ta soma karaya a karkashin baraguzan gine-gine a Gaza.
Ya yi wannan kiran ne a daidai lokacin da aka fara cigiyar yarinyar mai shekaru 15 mai suna Hala Hazem Hamada, wadda a karshe aka ceto ta a ranar Talata bayan da sojojin Isra'ila suka kashe 'yan'uwanta shida, ciki har da iyayenta.
An soma kashe-kashen ne a ranar Asabar a lokacin da sojojin Isra'ila suka dira a harabar gidansu Hala, wadanda ƴan asalin arewacin Gaza ne da suka nemi mafaka a wajen birnin Khan Younis na kudancin yankin.
Hala ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa, sojoji sun yi amfani da lasifikar wajen kiran mazauna yankin da su bar wurin, amma kafin ita da danginta su dauki matakin yin hakan, "gidan ya fara rushewa a kanmu", inda motar katafilar Isra'ila ta fara ruguza gine-ginen.
"Dakarun sun kai wa kowa hari a gidan amma ban da ni da kanwata," in ji ta. "Yar'uwata Basant ta ce da ni, "Na tsorata, ki cece ni, ba zan iya motsawa ba, baraguzan ginin nakan ƙafafu, kuma mahaifina yana kan ƙafata, ba zan iya motsawa ba."
Sai Basant ta yi shiru, ta bar Hala ita kadai tana jira lokacin da za'a kawo mata dauki.
Basant, mai shekaru 19, na daga cikin mutane shidan da suka mutu.
'Babana ya cika cikin jini da ya lullube shi'
Yayin da Hala ke jira, wani dan jaridan AFP ya dauki bidiyon Mohammed al Sabbagh yana ba ta kalaman goyon baya ta wayar tarho.
"Ki kula da kanki sannan ki jajirce, idan akwai wani abun ci kusa da ke, ki ci kafin mu isa gare ki," in ji shi.
"Na rantse da Allah, ba mu san yadda za mu kai zuwa gare ki ba... amma muna ƙoƙarin zuwa inda kike, kada ki damu, za mu zo gare ki," a cewar labarin ban tausayin da Hala ta bayar.
"Mahaifina yana lullube cikin jini, tun yana numfashi har ya zo ya daina," in ji ta.
A ranar Laraba, Hala ta ba da labarin yadda aka ceto ta, a yayin da take magana da kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP daga gadon wani asibiti da ke birnin Rafah a kudancin kasar.
“Sun fara ne da rage baraguzan tare da yanke ƙarafan gine-ginen har sai da suka fitar da ni, da suka fito da ni, sai suka ajiye ni a kan gadon marasa lafiya,” in ji ta.
Ko da yake ba ta ji mummunan rauni ba, amma jikinta na ƙoƙarin murmurewa bayan tsawon lokacin da ta kwashe ba tare da abinci ko ruwa ba, baya ga babban rashi da tashin hankali da take fuskanta.
"Na tsira, amma ina son ganin iyalina a karo na karshe," in ji ta. "Na ga 'yar'uwata da mahaifina, amma har yanzu ba a ciro su ba, har yanzu suna karkashin baraguzan, ina so in gansu akalla na yi bankwana da su."
Isra'ila ta kashe akalla mutane 30,717, akasari yara da mata, tare da raunata 72,156 ya zuwa yanzu a ayyukan kisan gilla da ta yi a Gaza wadda ta mamaye.
Yakin Isra'ila ya tura kashi 85 cikin 100 na al'ummar Gaza gudun hijira, cikin wani mawuyacin hali sakamakon karancin abinci da ruwan sha mai tsafta, da kuma magunguna, yayin da kashi 60 cikin 100 na ababen more rayuwa na yankin suka lalace ko kuma suka barnatasu , a cewar Majalisar Dinkin Duniya.