'Yan takarar sun tattauna kan tsare-tsaren tattalin arzikin Iran, wanda yake cikin mawuyacin hali sakamakon jerin takunkuman da Amurka da sauran ƙasashen Yamma suka ƙaƙaba wa ƙasar. / Hoto: AFP

'Yan takara shida na shugabancin Iran sun mayar da hankali kan tattalin arzikin ƙasar a muhawararsu ta farko da suka kwashe awanni huɗu suna tafkawa kai-tsaye ta gidan talbijin na ƙasar, gabanin zaɓen da za a yi ranar 28 ga watan Yuni sakamakon mutuwar Shugaba Ebrahim Raisi da 'yan tawagarsa bakwai a hatsarin helikwafta.

Muhawarar ita ce ta farko a cikin guda biyar da aka tsara gudanarwa a sauran kwanaki 10 da suka rage kafin zaɓen domin maye gurbin Raisi, na hannun-daman shugaban Addini na Iran Ayatollah Ali Khamenei wanda kafin rasuwarsa aka yi hasashen shi ne zai gaji shugaban mai shekara 85.

'Yan takarar sun tattauna kan tsare-tsaren tattalin arzikin Iran, wanda yake cikin mawuyacin hali sakamakon jerin takunkuman da Amurka da sauran ƙasashen Yamma suka ƙaƙaba wa ƙasar.

Dukkan su sun yi alƙawarin yin bakin ƙoƙarinsu wajen ganin an ɗage takunkuman tare da aiwatar da sauye-sauye ko da yake babu wanda ya yi bayani dalla-dalla kan yadda zai tunkari matsalar. Kazalika 'yan takarar sun yi muhawara kan hauhawar farashi da giɓin kasafin kuɗin ƙasar da kuma yaƙi da cin-hanci.

Za a gudanar da zaɓen ranar 28 ga watan Yuni ne a yayin da ake ƙara tayar da jijiyoyin wuya tsakanin Iran da ƙasashen Yamma game da shirin Tehran na ƙera makamin nukiliya da sauransu.

AP