A watan jiya, Vaughan Gething ya zama minista na farko a Wales, abin da ya sanya shi zama bakar-fata jagora na farko a gwamnatin wata kasa a Turai.
An haifi Gething a Zambia, mahaifiyarsa ‘yar Zambia ce, mahaifinsa kuma dan yankin Wales. Hawansa mulki ya zo a daidai lokacin da siyasar Birtaniya ke jan hankali, lokacin da marasa rinjaye suke samun damar yin shugabanci.
A karo na uku a cikin shekaru uku – A Downing Street, A Scotland da yanzu kuma a Wales – kujerar sabon shugaba ta samu sabon mahayi bakar-fata.
Duba ga mata biyu da ke shugabantar Arewacin Island ta hanyar karba-karba, wannan ya samar da arashi cewa a yanzu babu maza farar-fata da ke shugabancin kasashen Birtaniya.
Sabbin fuskoki a shugabancin siyasar Birtaniya ya nuna bunkasar dimokuradiyya, wadda a cikin ta ‘yan tsiraru marasa rinjaye ke samun damar shugabantar jama’a sama da kowanne lokaci.
Sai dai kuma, wannan na faruwa ne bayan Brexit, inda siyasar sanin-kai da launin- fata suka fafata wajen rabuwar kan jama’a. Jam’iyyu uku masu al’adu iri daban-daban sun amince da zabar marasa rinjaye saboda suna musu kallon za su warware wasu al’amura a wasu lokuta na musamman.
A 2022, Rishi Sunak ya zama Firaministan Birtaniya na farko da ya fito daga Asiya. Shi ne shugaban jam’iyyarsu bayan Boris Johnson ya sauka. Sunak ya zama kamar shi kadai ne wanda ya so daidaita al’amura a lokacin da wadda ta gabaci Jonson, Lis Trust ta ga ana tantama game da shugabancinta.
A 2023, Humza Yousaf ya zama shugaban Scotland kuma Musulmi na farko da ya zama shugaba a wata babbar kasa ta Yammacin duniya. Addini da siyasa na cin karo da juna a siyasar Scotland.
Amma wani abu mai ban mamaki shi ne yadda aka tsananta bincike kan dan takara Kirista ne ya janyo wa Yousaf samun karin dama da nasara a matsayin Musulmi dan Scotland da ra’ayinsa na rayuwa suka yi daidai da na ‘yan jami’yyarsa
A yanzu a 2024, mun ga fafatawa ta kusa da ministan tattalin arziki da kudi na Wales. Wand aya lashe zai zama Firaminista na farko da ba bakar fata ba kuma bad an luwadi ba, babbar alamar shigar da kowanne bangare harkokin siyasa.
An haifi dukkan wadannan jagorori a shekarun 1970 da 1980, a zamanin da dukkan mambobin majalisar dokoki da ministoci farare ne.
Akwai wasu ‘yan majalisa ‘yan kadan da ‘yan asalin Asiya ne a shekarun 1890 da 1920. Amma an dauki sama da shekaru 40 kafin a fara gudun hijira mai karfi zuwa Birtaniya, a nan ne aka samu zuwa Windrush daga Jamaica a 1948, kafin a samu bakake su shiga majalisar dokoki – inda a 1987 aka zabi bakaken fata uku da dan Asia duka zuwa majalisar dokokin Birtaniya.
A lokacin da Sunak da Geithing suka kammala jami’a babu bakar fata ko daya a majalisar ministoci har sai da Boateng ya zo a 2002.
An sake daukar lokaci mai tsayi bayan 1987 don kalubalantar muhawarar da ake yi kan ana samun ‘yan tsiraru marasa rinjaye a shuganacin siyasa a mazabun cikin gari sosai.
Bayan 2010, an karyata da kalubalantar muhawarar da ake yin kan cewa yankuna masu jama’a da dama ba za su amince da jagorancin ‘yan tsiraru ba, musamman a lokacin da David Cameron ya zama shugaban ‘yan ra’ayin rikau, kuma ya yi kokarin fadada jam’iyyarsa tun kafin matsaloli su taso.
Wannan ya hada da saka ‘yan Afirka da Asiya a cikin ‘yan takarar ‘yan ra’ayin rikau a dukkan fadin Ingila, mafi yawa ma a gundumomin da ke da karancin kabilu mabambanta. Shugabancin kabilu marasa rinjaye a Scotland da Wales na habaka, duk da cewa kaso 95 na jama’ar kasashen fararen-fata ne.
Wannan ya yiwu ne bayan mambobin jam’iyya da masu zabe suka amince cewa ‘yan siyasa tsiraru marasa rinjaye za su iya wakiltar kowa, ba wai yi musu kallon za su zama wakilan sauran marasa rinjaye ba ne.
Shugabacin ‘yan kabilu marasa rinjaye ya zama ruwan dare a yanzu a Birtaniya – amma abin ba haka yake ba kasashen Turai da dama.
Watakila wannan na faruwa ne saboda a tarihi an ga yadda ‘yan tsiraru mara rinjaye na Birtaniya suka mayar da martini ga nuna wariyar da aka yi musu, inda suke nuna bambance-bambancen kasar na nufin karfin ta da tarihin Daular.
Tabbas, Birtaniya na da babban aikin da za ta yi kan launin fata da nuna wariya, kamar yadda rahotanni suka bayyana ana samun daduwar kyamar Yahudawa da Musulmai a kasar.
Amma kuma suna da dokoki masu karfi na adawa da nuna wariya sama da kasashen Turai da dama, inda jami’an gwamnati ke yawan zama misalin bayanan da ake tattarawa na kabilanci.
Wannan na nufin a kasashe irin su Faransa an rasa daya daga cikin muhimman abubuwan tantance nuna bambanci tsakanin mutane. Birtaniya na da sakamako mafi inganci a bangaren ilimi, kuma ana ganin daduwar ‘yan tsiraru marasa rinjaye a harkokin kasuwanci, harkokin doka da ma sauran su ciki har da siyasa.
‘Yan siyasa marasa rinjaye daban-daban na da ra’ayoyi mabambanta kan yadda za a yi Magana kan launin fata da siffanta mutane Sunak ya yi amanna cewa hanya mafi kyau it ace a yi tinkaho da Birtaniya a matsayin mai dabbaka dimokuradiyya da yaruka daban-daban, ga jama’arsa na Indiya mabiya addinin hindu.
Yousaf a Gething sun zabi su yi bayani sosai game da yadda aka magance matsalolin da suka hana samun ci gaba a baya – da kuma sharhi kan sauran matsalolin da ake da su. Gething yay aba da gudunmowar zmaanin Windrush – zamanin farko na masu gudun hijira daga kasashen Commonwelath – A Cardiff a bazarar da ta gabata, wani na cewa “Ban zo nan ba saboda na kasance mutumin da ke son yin wannan aiki, ko kuma ni ne mutum na farko da zai iya yi.”
Damar shiga siyasa da da hawa manyan mukamai, ba za su hana ‘yan tsiraru marasa rinjaye fuskantar rashin adalci ba a rayuwarsu. Kafafan sadarwa na yanar gizo sun irgiza duk wani tabbaci kan wayar da kai game da nuna wariya a tsakanin al’umma.
Ko da a ce wadanda suke da tsaurin ra’ayi na raguwa, amma kuma akwai bata-gari a bakin kofa. Mata da ‘yan tsiraru na fuskantar mafi yawan kyama da tsana a shafukan intanet.
‘Yar majalisa bakar-fata mafi dadewa a majalisar dokokin Birtaniya, Diane Abbott ta zama wanda aka fi nufa a koyaushe. Kalaman nuna tsana da ake yi mata daga wadanda suka fi tallafawa jam’yya na nuni da nuna wariya ba daga intanet kawai yake zuwa ba. Kamfanonin sadarwa na zamani sun gaza samar da tsarin magance nuna wariya kamar yadda ake tsammani.
Za a yanke hukunci kan shugabannin al’ummu marasa rinjaye a Birtaniya duba da irin kwazon da suka nuna a bakin aiki. Akwai yiwuwar a babban zabe da za a yi a nan gaba shugaban Leba Keir Sarmer ya tabbatar da babu wani sauran gidan gilashi ga fararen-fata.
A nan ne wasu mutane suke tantamar idan fuskokin kabilu da ke manyan wurare za su iya kawo wani sauyi, ko su zama masu tirjiya idan wasu suka yi amfani da su wajen bayyana an kawo karshen nuna wariya a tsakanin al’umma.
Marubucin wannan makala Sunder Katwala, darakta ne a cibiyar British Future, wata kungiya mai zaman kanta d ake ayyukan kan mutane, launin fata da gudun hijira.
Togaciya: Ba dole ba ne ra'ayin marubucin ya zama daidai da ra'ayi da ka'idojin aikin jarida na TRT Afrika.