Kisan da Isra'ila ta yi wa shugaban Hamas Ismail Haniyeh a wani harin sama a Tehran ya ƙara girgiza Gaza da Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da kuma duniyar Musulmai.
Haka kuma kisan ya ƙara dasa ayar tambaya kan wanda zai gaji shugabancin ƙungiyar ta Hamas. Mutuwarsa ta kasance wata "babbar tsawa" ga 'yan Gaza, inda wasu suke nuna rashin jin daɗinsu game da gazawar da Iran ta nuna "wurin kare shi".
TRT World ta tattauna da Yousef Alhelou, wanda wani ɗan jaridar Falasɗinu ne kuma mai sharhi kan siyasa da ke zaune a London kan tasirin da ke tattare da kisan da aka yi wa shugaban na Hamas.
TRT World: Wa kake tunani zai maye gurbin Haniyeh?
Yousef Alhelou: A zahiri har yanzu ba a san wanda zai gaji Haniyeh ba. Sai dai ana tunanin Khaled Meshaal ne, wanda ke zaune a wajen Falasɗinu. Sai dai mu jira mu gani.
TRT World: Kana ganin manyan shugabannin ƙungiyar irin su Sinwar da Deif za su matsa gaba domin sa ido kan shugabancin?
Yousef Alhelou: A'a, kwamandojin sojin ba su cika jagorancin siyasa ba. A'a, Haniyeh bai taɓa zama shugaban sojinta ba. Don haka wannan sabon abu zai kasance cikin fagen siyasa a harkar Hamas.
TRT World: Kana tunanin akwai wasu mutanen da za su iya karawa da Khaled Mashal?
Yousef Alhelou: Khalil al Hayyah.
TRT World: Shin mutuwar Hamas za ta iya jawo rikicin shugabanci a Hamas?
Yousef Alhelou: A'a, ba za ta haifar da matsala a shugabancin ba. Isra'ila ta kashe shugabannin Hamas da dama a baya da kuma wasu jagororin gwagwarmaya na Jihadin Islama na Falasdinu, PFLP (Popular Front for the Liberation of Palestine), DPFLP (Democratic Front for the Liberation of Palestine), da sauran mutane da dama.
Kashe jagororin ba zai kai ga kawar da duk wata ƙungiya ta Falasɗinu ba. Kungiyoyin Falasɗinawa za su ci gaba da wanzuwa muddin Isra'ila za ta ci gaba da mamaye kasar Falasdinu, kuma muddin Isra'ila ta kashe Falasdinawa a kullum, ba a Gaza kadai ba, har ma a Gabar Yammacin da Kogin Jordan da Isra'ila ta mamaye, ciki har da Gabashin Kudus da ta mamaye.
TRT World: Me kake tunani kan tarihin da Haniyeh ya kafa a siyasance?
Yousef Alhelou: Za a riƙa tunawa da Haniyeh a matsayin mutum mai muhimmanci, mai daraja a cikin al'ummar Falasdinu. Hatta ‘yan adawarsa Fatah, da jam’iyyar da (Mahmoud) Abbas ke jagoranta ta karbe shi a Yammacin Gaɓar Kogin Jordan da aka mamaye.
Za a rika tunawa da shi a matsayin Firaiminista na farko da ya jagoranci gwamnati lokacin da Hamas ta hau kan karagar mulki a shekara ta 2006.
Za a tuna da shi a matsayin shugaban da ya sadaukar da kansa, ya sadaukar da iyalinsa, ya tsaya ƙyam.
Haka kuma akwai maganganu da ya yi da yawa waɗanda suka yi shuhura, misali kamar lokacin da ya bayyana cewa ba zai taɓa amincewa da Isra'ila a matsayin ƙasa ba domin babu ita, wanda hakan ke nufin Birnin Kudus da Al Quds, har abada za su ci gaba da zama babban birnin Falasɗinu.
An san shi da murmushin zahiri da kuma na diflomasiyya a fuskarsa, haka kuma hakika babban rashi ne ga Falasdinawa a cikin yankunan da aka mamaye da kuma wajen Falasdinu.
Za mu tsaya mu ga wane ne zai kasance mataimaki ko kuma sabon shugaban Hamas, haka kuma dole ne mu tsaya mu ga idan Hamas da sauran ƙungiyoyin gwagwarmaya da kuma Iran da Hezbollah da Yemen da Iraƙi idan za su ɗauki fansa dangane da kisan da aka yi.