Trump ya bar kotun bayan alƙali ya same da shi laifuka a tuhume-tuhume 34 da suka shafi shrga ƙarya. / Hoto: Reuters

Wata kotu a Amurka ta samu tsohon shugaban ƙasar Donald Trump da laifi a kan tuhume-tuhume 34 waɗanda ke da nasaba da shirga ƙarya a harkokin kasuwancinsa domin ɓoye toshiyar-baki da ya bayar game da alaƙarsu da fitacciyar mai fitowa a finafinan batsa wato Stormy Daniels a lokacin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasar a 2016.

Jim kaɗan bayan masu taimaka wa alƙali yanke hukunci na kotun ta birnin New York sun sanar da hukuncin, sai aka riƙa samun martani daga 'yan siyasa na jam'iyyu daban-daban da masu fafutuka da kafofin watsa labarai.

Donald Trump

Bayan yanke hukuncin, Donald Trump ya ce ba shi "da laifi", sannan ya bayyana hukuncin a matsayin "abin kunya".

"Wannan hukunci na cike da maguɗi kuma abin kunya ne. Mutane ne za su yanke hukunci na haƙiƙa ranar 5 ga watan Nuwamba. Kuma sun san abin da ya faru, sannan kowa ma ya san abin da ya faru a nan," in ji Trump a yayin da yake barin kotun.

Ya ƙara da cewa, "Ba ni da laifi, amma babu komai. Ina fafutuka ne a kan ƙasarmu. Ina fafutuka a kan kundin tsarin mulkimu."

Shugaba Joe Biden

Shugaba Joe Biden ya yi martani ne ta hanyar yin tsokaci game da zaɓen shugaban ƙasar da ke tafe a watan Nuwamba, yana mai cewa, "Hanya ɗaya ta hana Donald Trump komawa ofishin shugaban ƙasa wato Oval Office ita ce: akwatunan zaɓe."

Shugaban Majalisar Wakilai Mike Johnson

Shugaban Majalisar Wakilan Amurka Mike Johnson Mike Johnson, wani babban mai goyon bayan Trump, ya yi ƙorafi kan hukuncin kotun, yana mai cewa "A yau an yi abin kunyar da bai taɓa faruwa ba Amurka."

"Wannan batu ne na siyasa zalla, ba lamari ne na shari'a ba. Gwamnatin Biden tana amfani da kotuna domin cim ma muradu na siyasa, kuma hukuncin da aka yanke a yau ya nuna cewa jam'iyyar Democrat za ta yi duk abin da za ta iya don murƙushe 'yan adawa," in ji Johnson a saƙon da ya wallafa a shafinsa na X.

TRT World