Wata ƙungiyar 'yan Isra'ila tana neman "matsin lambar ƙasashen duniya na gaske kan Isra'ila domin ta tsagaita wuta nan-take a Gaza", inda ta yi kira da ƙasashen duniya su goyi bayan manufarta ta tsagaita wuta. Tuni 'yan ƙungiyar fiye da 2,400 suka sanya hannu a kan wata takarda da ke neman a tsagaita wuta.
A sanarwar tasu, wadda suka aika ga Majalisar Ɗinkin Duniya, Amurka, Tarayyar Turai, Tarayyar Ƙasashen Larabawa da "dukkan ƙasashen duniya", sun yi kira na bai-ɗaya domin a yi amfani da dukkan wata matsa lamba da takunkuman kan Isra'ila har sai ta tsagaita wuta nan da nan a Gaza.
Sanarwar ta ci gaba da cewa: "Da yawanmu masu adawa da mamaya ne, saboda a samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin nan... Abin takaici, mafi yawan 'yan Isra'ila na goyon bayan ci gaba da yaƙi da kisan ƙare-dangi, kuma da alama babu wani sauyi da za a samu daga cikin gida. Ƙasar Isra'ila na kan turbarkashe kanta da kuma da tushen rusau da bala'i a kowace rana."
Ƙawancen na muhawara da sukar gwamnatin Isra'ila, inda suka ce Tel Aviv "sun bar 'yan ƙasa da aka kama, sun kuma kashe wasu... sun kuma yi watsi da makomar dukkan 'yan ƙasar."
Kazalika, sanarwar ta ce 'yan Isra'ila da dama na da irin wannan ra'ayi amma sun yi shiru saboda tsoron kada 'yan siyasa su kyare su.
Babu alamun kawo ƙarshen balahirar da ake ciki
Mahukuntan Tel Aviv sun kashe Falasɗinawa fiye da 42,000 tare da jikkata fiye da 100,000 a sama da shekara ɗaya da suka kwashe suna kai hare-hare a Gaza. Amma ƙwararru da masu nazari sun ce wannan wani ɗan adadi ne na gaskiyar abin da ya afku game da mutuwar Falasɗinawa da ake cewar ya kai kusan mutane 200,000.
Ana kuma tunanin akwai Falasdinawa kimanin 10,000 da ɓaraguzan gine-gine suka danne. An kuma yi garkuwa da wasu fiye da 10,000 tare da kai su zuwa gidajen kurkukun Isra'ila inda ake cutar da su.
"A kowace rana ana nisantar yiwuwar cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta da yin sulhu," in ji ƙawancen.
A jawabin ƙarshe da suka yi, 'Yan Isra'ila don Matsin Lambar Ƙasa da Ƙasa sun bayyana wasu 'yan ƙasashe da a baki kawai suka dinga batun neman tsagaita wutar ba tare da ɗaukar matakan gaskiya ba don cim ma wannan manufa.
"Shugabannin ƙasashe da dama na yawan maimaita magana kan ta'addancin da suke kallo ana yi, amma ba sa ɗaukar wani matakin a zo a gani a aikace don kawo ƙarshen yaƙin. Kawai mun dinga ganin maganganu ba aiki."