'Yan sanda suna ƙoƙrin kwantar da hankula a wan otek a yayin wata zanga-zangar adawa da 'yan cirani a Rotherham. ranar 4 ga watan Agustan 2024. / Hoto: Reuters

Zanga-zanga ta ɓarke a Birtaniya, mafi muni da aka gani a shekara 13 da suka wuce, inda masu tsattsauran ra'ayi suke fito-na-fito da 'yan sanda, suna kai wa masallatai hari da yin sace-sace a shaguna, sakamakon kisan wasu 'yan mata uku da aka yi a yankin Southport bayan caka musu wuƙa.

Firaminista Keir Starmer ya zargi "'yan daba masu tsaurin ra'ayi" da suka kasance "wasu 'yan tsiraru" kan tarzomar da ke faruwa a Liverpool da Lancaster da Leeds da Birmingham da Hull da Belfast da sauran su.

A ƙoƙarin daƙile jita-jitar da ake yaɗawa a shafukan sada zumunta da ke rura wutar zanga-zangar — cewa maharin Musulmi ne ɗan ci-rani — wani alkali ya ba da umarnin cewa a bayyana ko wane ne maharin.

"Cigaba da hana bayyana cikakken rahoton a wannan matakin yana da illa na barin wasu da ke yin ɓarna su ci gaba da yaɗa labaran ƙarya a cikin wani wuri," in ji alkalin Liverpool Andrew Menary.

Maharin da ya kashe 'yan matan Axel Rudakubana — wani matashi ne haifaffen Cardiff wanda iyayensa 'yan ƙasar Rwanda ne — kuma an gano shi ba ɗan ci-rani ba ne ba kuma Musulmi ba.

A hirarta da TRT World Sakatare Janar ta Ƙungiyar Musulmai ta Birtaniya Zara Mohammed ta ce lamarin ya yi wa Musulman Birtaniya tsanani ƙwarai da gaske.

"Tsoro da fargaba na ta ƙaruwa. Babu ruwan Musulmai a wannan kisan kai da aka yi a Southport, amma suna ta kai wa masallatai hari. Ina hankali a wannna lamari? Ina ga kawai irin wannan tunanin ne da aka taso da shi na nuna wariya, inda ba a ɗaukar Musulmai da muhimmanci, kuma ina ganin wannan ne ƙalubalen," ta ce.

Sai dai ana ci gaba da yaɗa farfaganda da labaran ƙarya inda ake alaƙanta hare-haren da Musulmai, kuma baƙin da aka gayyata don tattaunawa a wani shirin talabijin na masu ra'ayin mazan jiya sun yi ƙorafi a kan yadda ake ƙara samun yaɗuwar Musulunci a Birtaniya har ma bayan fayyace wane ne maharin.

Wasu daga cikin saƙonnin da waɗannan masu tsattsauran ra'ayin ke wallafawa a shafukansu na sada zumunta na ƙungiyoyi ko ɗaiɗaikun mutane sun haɗa da kalamai kamar: "Muna buƙatar a dawo mana da ƙasarmu", da "Ya isa haka."

"Duk waɗannan kalamai na ƙyamar Musulunci ne da ƙyamar 'yan ci-rani saboda suna da alaƙa," in ji Zara.

"Cewa suke Musulmai ba 'yan Birtaniya ba ne. Wai mu ba 'yan ƙasar nan ba ne, muna shigowa ne daga waje don mu ƙwace ƙasar, suna jawo faruwar munanan laifuka da bazarana. Ina jin abin da babu a cikin rahoton boren shi ne yadda ake kiran wadannan hare-hare na ƙyamar Musulunci... Musulmai da dama suna ganin babu wanda ya damu don kawai su Musulmai ne.

A ranar 1 ga watan Agusta, MCB ta yi wani taro ta intanet a kan tsaron masallaci, wanda ya samu halartar Liman Ibrahim Hussein daga Masallacin Southport, wanda ke cikin masallacin a lokacin da harin ya faru ranar 30 ga watan Yuli.

"Hukumar masallacin ta yi matuƙar damuwa da matakan tsaro kan abin da ya shafi waɗannan 'yan daba masu tsaurin ra'ayi inda suke ɓalla da fasa tagogi da ƙyauraye," a cewar Zara.

"Amma kuma suna tsoron hare-haren da ake kai wa cibiyoyin unguwanni da shaguna da gidajen kula da tsofaffi da makarantun bazara. Abin na da matuƙar ban tsoro, amma mun gaya wa kowa ya kwantar da hankalinsa, a yi aiki tare da 'yan sanda a kuma sanar da mabiya."

A wata mai zuwa ne MCB za ta gabatar da wani shiri mai taken 'Visit My Mosque' wato 'Ziyarci Masallacina', inda za a gayyaci waɗanda ba Musulmai ba don ziyartar wuraren ibada don kawar musu da duk wani shakku da suke da shi.

"Ya kamata mu kalli hakan a matsayin wani gagarumin ƙawancen aiki da za mu haɗa kai mu yi. Dole mu cigaba da ƙalubalantar duk wasu ƙarerayi masu illa. Muna buƙatar amfani da manyan kafafen watsa labarai don isar da saƙonmu, da yin magana da ƙawayenmu na sauran addinai da kuma yin aiki da ƙungiyoyin al'ummomi," in ji Zara Mohammed.

Ta kuma yi imanin cewa akwai bukatar a fayyace gaskiya a kan bayanan da ba daidai ba da ake yaɗawa a shafukan sada zumunta.

"'Yan siyasa kamar su Nigel faraga na buƙatar ɗaukar nauyin daƙile yaɗuwar labaran ƙarya. Ina ga abin da ke da bambanci a wannan karon shi ne suna amfani da WhatsApp da Telegram da Facebook da kuma Twitter — kuma abu mafi ban tsoron shi ne yadda suke saurin taruwa.

"Mun ga yadda masu tsaurin ra'ayi ke bunkasa da kuma mutane irin su Tommy Robinson, kuma duk da cewa sun sha yin irin wadannan zanga-zanga a baya, ba mu taɓa ganin mai tsananin kamar wacce ake yi yanzu ba.

TRT World