--- / Hoto: AA Archive

Nuna ƙyama ga Musulunci ya munana a yau, sama da yadda yake bayan kai harin 9/11, kuma dole 'yan siyasa su dakatar da yaɗa nuna ƙyamar addini, su magance nuna ƙyamara Musulunci, in ji ƙwararru da manyan jami'ai.

Wannan gargadi na zuwa ne a wajen taron kwanaki uku na Taron Diflomasiyya na Antalya, taron ƙasa da ƙasa da yake hada ministoci, jami'an diflomasiyya da manyan jami'ai daga kasashen duniya 148 a garin hutu na Antalya da ke gaɓar Tekun Bahar Rum.

A wajen wani taron tattaunawa mai taken 'Daduwar Nuna Wariya, Kyamar Baki da Musulunci', masu muhawara sun bayyana bukatar gaggawa ta magance ƙyamatar addini don tabbatar da zaman lafiya a tsakanin al'umma.

Kwararrun duk sun yarda da cewa Turai na fuskantar daduwa sosai wajen nuna kyama ga Musulunci tun Oktoban bara, a lokacin da Hamas ta kai hari kan iyakar Isra'ila wadda ita ma ta mayar da martani da munanan hare-hare soji a Gaza.

Miguel Moratinos, Babban Wakilin Majalisar Dinkin Duniya Kan Kawancen Sakafu, ya bayyana yadda lamarin ya tsananta tare da jaddada cewa "Kyamar Musulunci a yau ta fi yadda take bayan harin 9/11".

Tsana ce mataki na farko wajen kawo sauyawar tsana zuwa ga rikici, daga nan kuma zuwa yaki; dole ne mu koma ga tushen da ke janyo hakan," in ji Moratinos, yana mai nuni ga cewa ayyuka masu tunzurarwa irin su ƙona Alkur'ani da rikici na komawa su zama 'mummunar tsana'.

A tsakanin tunanin rayuwa daban-daban - "Musulunci ya zama batu a dukkan wata tattaunawa da batutuwan siyasa," in ji shi.

"Muna bukatar shirye-shirye da ayyuka don sauya ruhi da zuƙatan jama'a" don magance wadannan matsaloli.

An gudanar da muhawarar mai taken "Daduwar Nuna Wariyar Launin Fata, Kyamar Baki da Musulunci" a wajen Taron Diplomasiyya na Antalya (ADF) a Babban Dakin Taro na NEST da ke birnin Antalya na Turkiyya a ranar 1 ga Maris.

Masu tsaurin ra'ayi 'na cutar' da marasa rinjaye

Wani babban daga Kungiyar Hadin Kan Tsaro ta Turai (OSCE) ya gargadi 'yan siyasa da su guji rura wutar wannan rkici ta hanyar yin kalaman raba kawunan jama'a.

Matteo Mecacci, Daraktan Ofishin Kula da Dimokuradiyya na Cibiyar Kare Hakkokin Dan Adam d ake karkashin OSCE ya ce "Abubuwan da suke kara janyo nuna rashin aminta da nuna wariya, su ne dai abubuwan da suke kalubalantar dimokuradiyya da dokoki."

Mecacci ya jaddada muhimmancin barin batutuwan da suka shafi dokoki ga wadanda abun ya shafa, yana mai kara wa da cewar lallai kar 'yan siyasa su zama masu cusgunawa marasa rinjaye d atake hakkokinsu."

"Ba aikin dan siyasa ba ya bayyana me da sanda ya kamata ya yi.... saboda wannan na shafar 'yancin kundin tsarin mulki .... a rayu ba tare da tsoro ba."

Mecacci ya yi gargadi da cewa gazawar daukar matakan dakatar da ayyukan masu tsaurin ra'ayi na iya kaiwa ga daduwar munanan ayyukan nuna tsana da barazana ga jama'a.

'Ba a waje mai kyau muka tsaya ba'

A yayin da kwararru suka yarda kan akwai bukatar a magance matsalar nuna wariya da ke daduwa sosai a duniya, akwai kuma ittifakin cewa shugabanni ba su da niyyar yin hakan.

Da take kara bayanin kan lamarin, Sakatare Janar ta Majalisar Turai, Marija Pejcinovic Buric, ta yi karin haske kan "Raguwar aiki da doka, dakushewar dabbaka dimokuradiyya da kare hakkokin dan adam."

Buric na da ra'ayin cewa akwai isassun kayan aiki da za a dabbaka don yaki da nuna wariya, nuna kyamar baki da kyamar Musulunci, amma "Kawai ba ma dabbaka su".

Domin magance Nuna Kyama ga Musulunci da ke daduwa "Dole ne mu (fara) da kallon ta a matsayin matsala", in ji Buric, tana mai zayyana wasu matakai masu hawa uku da za a iya bi wajen magance nuna kyama ga Musulmai ta hanyar aiki da dabarun riga-kafi, kariya da gurfanarwa a gaban kotu.

Evren Dagdelen Akgun, wakilin OCSE kan Yaki da Kin Aminta da Wasu Al'ummun da Nuna Bambanci ga Musulmai, ya jaddada muhimmancin da ke akwai wajen yin kyakkyawar mu'amala da Musulmai.

"(Amma) ana hana gudanar da kyakkyawar mu'amala da Musulmai," in ji Akgun. Kuma yau, sama da koyaushe, "ba mu tsaya a waje mafi kyau ba".

TRT World