A cikin hamada da ake samun karancin abinci da ruwa, Muslman farko da ke Medina sun soma koyon yin azumi karkashin koyarwar Annabi Muhammad S.A.W.
Musulmai da dama ne da ke fadin duniya suka shirya wa azumin watan Ramadana wanda wannan ne zai kasance bikin zagayowar watan karo na 1,398.
Idan aka koma baya zuwa shekarar 624 CE, azumin watan Ramadana na farko da aka yi an yi shi ne a birnin Madina da ke Saudiyya.
Haka kuma ranar na nuni da shekara ta biyu bayan Hijirar Annabi Muhammad S.A.W daga Makkah zuwa Madina. Sakamakon matsin lambar da ya fuskanta daga kafiran Makkah, an tilasta masa yin Hijira zuwa Madina a shekarar 622.
Bayan bin umarnin Annabi Muhammad S.A.W na yin Hijira, mabiyansa Musulman farko sun yi tunanin fara kalandar Musulunci wadda aka fara kirge daga lokacin Hijira.
Watan Ramadana na farko ga Musulmai ya fado ne a watan Maris, a lokacin bazara a inda a lokacin babu zafi sosai a kasashen Larabawa har da Madina idan aka kwatanta da ainahin lokacin zafi.
“Ya ku wadanda kuka yi imani! An wajabta muku yin azumi kamar yadda aka wajabta shi ga wadanda suka gabace ku watakila ku samu takwa,” kamar yadda ayar Allah ta fada a cikin Al-Qur’ani mai girma inda Allah ya yi umarni da yin azumi.
An saukar wa Annabi Muhammad wadannan ayoyi ne a watan Fabrairun 624 AD, ko kuma a watan Shawwal, a shekara ta biyu bayan Hijira, kamar yadda Kasif Hamdi Okur, wanda farfesa ne kan nazarin adinnin Musulunci a Jami’ar Hitit.
Ganin cewa Annabi Muhammad S.A.W da wasu Musulmai sun saba azumi a daidaikun ranaku a wasu watanni kafin saukar da wadannan ayoyi, yin azumi na kwanaki 30 ko 29 a jere ya zama wani sabon lamari ga Musulmai, kamar yadda Okur ya shaida wa TRT World.
“Akwai bayanai tun zamanin Annabi Muhamad da suka nuna cewa su kan su Musulman farko sun fuskanci kalubale kafin su saba da azumin watan Ramadan a shekarar farko,” kamar yadda ya bayyana.
Lokacin kadan kafin a saukar da ayoyin da suka wajabta yin azumin Ramadana, Musulmai sun sauya Kiblah daga Birnin Kudus zuwa Ka’aba da ke Makkah. Duka wadannan sauye-sayen sun faru ne bayan da Musulmai suka yi Hijira zuwa Madina.
Bayan sauya Kiblah da kuma soma yin azumin watan Ramadana tsawon wata guda, Musulmai a lokacin sun ji kansu daban da sauran addinai da suke zaune da su a Madina da suka hada da Kiristoci da Yahudawa, kamar yadda Okur ya bayyana.
Haka kuma azumin watan Ramadana na farko ya zo daidai da lokacin da aka yi gagarumin yakin Musulunci na farko wato yakin Badr, tsakanin Musulman Madina da kuma kafiran Makkah, kamar yadda ya ce.
Duk da cewa jumullar wadanda suka halarci yakin tsakanin duka bangarorin biyu ba su wuce mayaka 1,200 ba, a karshe Musulmai ne suka yi nasara, inda hakan ya sa Musulunci ya kara daukaka a duniya.
An wajabta yin azumi amma akwai wadanda aka saukakamawa.
Al Qur’ani mai girma wanda a kowane lokaci yana tsayawa a tsakiya domin saukakawa Musulmai ga rayuwarsu da kuma yi musu adalci, ya cire wasu nau’ukan mutane da ba a wajabta musu yin azumi ba kamar tsofaffi da marasa lafiya da mata masu ciki da yara, kamar yadda farfesan ya bayyana.
Idan baligi Musulmi yana da cikakkun hujjoji da ba zai iya yin azumi ba, zai yi ciyarwa ga mara karfi na duk ranar da bai yi azumin ba, kamar yadda Al-Qur;ani ya bayyana.
Duk da wahalar da ake fuskanta a lokacin azumi wadda jarabawa ga Musulmai, Ramadana na dauke da dumbin albarka kuma wata ne da ake samun gafara daga Allah.
“Tir ga bayin da aka shiga watan Ramadana kuma ba a gafarta musu ba,” kamar hadisin Annabi Muhammad S.A.W ya ce in ji Okur. A Musulunci, azumi ba wai nesantar da kai kadai bane daga ci da sha, amma har da kokarin tsarkake kai daga aikata zunubai, in ji Ali Celik, shugaban tsangayar nazarin addini na Jami’ar Dumlupinar wanda ya yi rubutu sosai kan Ramadana da kuma azumi.
Sakamakon hakan, Annabi Muhammad S.A.W da sahabansa na kara yawan ibadun da suke yi a lokacin azumin Ramadana.
“Musamman a kwanaki 10 na karshe, ya fi so ya yi itikafi a Masallaci,” in ji Celik. Itikafi na nufin killace kanka daga sauran jama’a, tare da sadaukar da kai wurin bauta a maimakon yin wasu abubuwan duniya domin samun al-kibla a rayuwa.”
“Yanayin yadda Annabinmu yake buda-baki yanayi ne mai sauki, ba irin na alfarma ko almubazaranci ba,” in ji Celik. Idan suka samu nau’in abinci guda daya, suna jin dadi, in ji Okur.
A lokacin buda-baki a wannan zamanin, akwai abinci iri-iri da miya da shinkafa da sauran kayan alatu da ake amfani da su a lokacin buda-baki. “Buda-bakinsu yana da sauki, suna nika dabino ne su hada shi da fulawa da ko ruwa su yi abincin su. Ko kuma su hada shi da biredi da man zaitun su yi wani abincin.” In ji shi.