Sama da kaso 50 cikin 100 na dalibai Musulmai da ke California na fuskantar cin zarafi. Hoto/Reuters

Sama da shekara 20 bayan da aka kai harin ta’addanci na 11 ga watan Satumban 2001, ana ci gaba da nuna wariya da kuma kin jinin Musulmai a Amurka, lamarin da har ya fusata kungiyar Musulmai mafi girma da ke kasar.

“Bayan shekara 22, kin jinin Musulunci na kara kankama inda ya kara zama wani ginshiki na nuna wariya a kasarmu,” in ji Hussam Ayloush, shugaban kungiyar Council on American-Islamic Relations CAIR-CA reshen Jihar California.

Ayloush ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu cewa kusan Musulmai miliyan daya cikin miliyan biyar da aka yi kiyasin suna zaune a Amurka suna zaune ne a Jihar California, inda ya yi nuni da cewa cin mutuncin da ake yi wa Musulmai yana karuwa tun bayan 9/11.

“Sama da kaso 50 cikin 100 na dalibai Musulmai da ke California na fuskantar cin zarafi ta hanyar magana ko kuma jikinsu a makarantu don kawai Musulmai ne,” in ji Ayloush.

“Bugu da kari, akwai sunayen mutum miliyan 1.6 wadanda ke kan jerin sunayen da gwamnati ke saka musu ido inda kusan dukansu Musulmai ne, inda ake sa musu ido kan tafiye-tafiyensu ko kuma suna da suna irin na Musulmai.

“Irin cin zarafin da ya fito daga 9/11 wadda gwamnati ke da hannu a ciki ta haka ne kin jinin Musulmai ya fara,” kamar yadda ya ci gaba da cewa.

“Ana cin zarafin Musulmai a filayen jirgin sama, ana sa FBI suna bincike da kuma dasa masu leken asiri a masallatai tare da bayar da bayanai ga hukumomi kamar FBI da CIA domin su bibiyi Musulmai daga sauran kasashe kamar Syria da Libiya da Sudan.

Kin jinin Musulmai ya karu matuka nan take bayan da aka kai harin 9 ga watan Satumbar 2001, inda ya karu da kaso 1,617 daga 2000 zuwa 2001, kamar yadda alkaluma daga FBI suka nuna.

Wannan tashin gwauron zabin shi ne mafi yawa daga cikin rahotannin kin jinin Musulunci a Amurka.

“Gwamnatin Amurka karkashin George W. Bush na neman makiyin da zai bai wa masu ra’ayin ‘yan mazan jiya su kaddamar da kiyayyarsu, inda 9/11 ya zama wani ginshiki na mayar da duka Musulmai makiya,” in ji Ayloush, inda ya ce tun daga nan ake cin mutunci da cin zarafin duk wasu Musulmai.

“Yadda muke cin abinci da yadda muke saka kaya da yadda muke magana sai ya zama abin zargi,” kamar yadda ya bayyana kan kin jinin da Musulmai ke fuskanta bayan 9 ga watan Satumba.

“Idan suka yi hayar babbar mota domin daukar kaya, sai an kira FBI a kansu. Idan Musulmai ya fita wajen kasar sau da dama ko kuma suka cire kudi masu yawa domin kasuwanci, sai a dauka suna yin wani abu wanda FBI din za ta nemi ta yi bincike.

Ganin cewa ana yi wa Musulmai da yawa lakabi da ‘yan ta’adda da kuma alakanta su da Shugaban al-Qaeda Osama bin Laden, Cainkar ya bayyana cewa Musulmai sun fara gushewa daga Amurka tun bayan 9/11.

“Daga farko sun ‘fara boyewa,’ wanda hakan ke nufin suna rayuwarsu a boye sosai,” in ji Cainkar.

“Daga nan sai suka kafa kungiyoyi domin neman ‘yancinsu, inda suka kulla kawance da sauran kungiyoyi inda a hankali suka yi karfi a cikin kungiyoyi masu zaman kansu na Amurka.”

AA