Karin jiragen ruwan hudu sun bar tashoshin jiragen ruwan Yukren, karkashin yarjejeniyar fitar da hatsi ta İstanbul, in ji Ministan Tsaron Turkiye.
Sanarwar ta ranar Asabar, wadda ba ta bayyana inda jiragen ruwan suka taso ba, kawai ta ce an shirya tashin jiragen ruwa daga Yukren.
Kwana daya kafin hakan, jiragen ruwa tara ne suka bar tashohin jiragen ruwan Yukren.
Bayan fara yakin Yukren da Rasha a watan Fabrairu ne aka rufe tashoshin jiragen ruwa uku na Yukren dake gabar tekun Bahar Maliya.
Bangarorin na ci gaba da tattaunawa don ganin an kara wa’adin fitar da hatsi daga Yukren zuwa sama da ranar 19 ga Nuwamba da aka amince da farko, inda za kuma a saka har da fitar da hatsin Rasha da takin zamanin da take samarwa.
An samar da kwamitin hadin gwiwa tsakanin kasashen uku da Majalisar Dinkin Duniya, inda suke sanya idanu kan tafiyar jiragen ruwan a İstanbul. An sanya hannukan yarjejeniyar kwanaki 120.
‘Ba bun da zai hana a kara wa’adin’
Shugaban Kasar Turkiye Recep Tayyip Erdogan ya bayyana fatan da yake da shi game da wannan yarjejeniya.
A lokacin da yake dawowa daga Azabaijan, Shugaba Erdogan ya fadawa manema labarai cewa, “Babu tsaiko game da kara wa’adin fitar da kayan, kamar yadda na gani yayin tattaunawa ta wayar tarho da Shugaban Kasar Yukren Vladimir Zelensky da kuma ganawar da na yi da Shugaban Rasha Vladimir Putin, amma a yanzu dai idan ma aka samu wani cikas, babu abun da zai hana m magance shi.”
Wasu kwararrun Rasha na bayyana cewa takunkuman Yammacin Duniya sun hana fitar da hatsin Rasha da takin zamaninta duk da wannan yarjejeniya da aka kulla.
Tun lokacin da jirgin farko karkashin yarjejeniyar ya kama hanya a ranar 1 ga Agusta, sama da jiragen ruwa 365 dauke da hatsi sama da tan miliyan 8 sun bar tashoshin jiragen ruwan Yukren.