Rasha ta zargi Yukren da yunkurin kai hari da jirgin yaki mara matuki kan fadar Kremlin a wani yunkuri na abin da ta kira kashe shugaban kasar Vladmir Putin, lamarin da bai yi nasara ba.
Fadar Kremlin a ranar Larabar nan ta bayyana cewa an yi amfani da jiragen sama marasa matuka biyu wajen yunkurin kai hari kan gidan da Shugaba Putin yake, amma aka dakile harin.
An bayyana cewa Rasha na da hakkin ramuwar gayya.
Sanarwar da aka fitar ta kara da cewa “Jiragen yaki marasa matuka guda biyu sun kai hari Fadar Kremlin. Sakamakon matakin gaggawa da jami’an tsaro suka dauka an kawar da harin.”
Sanarwar ta ci gaba da cewa “Mu kalli wannan abu a matsayin shirin aikata ta’addanci da kokarin kisan gilla ga shugaban kasa a yayin bikin Ranar Nasara ta 9 ga Mayu, kuma a gaban manyan baki…bangaren Rasha na da hakkin ramuwar gayya a duk lokacin da aka so yin hakan.”
Amma a nata bangaren, Yukren ta bayyana cewa ba ta da alaka da wannan hari.
Sanarwar da gwamnatin Yukren ta fitar ta ce “Yukren ba ta da alaka da wannan hari na jirgin yaki mara matuki kan Fadar Kremlin. Yukren ba ta kai hari kan Kremlin ba, hakan ba zai warware wata matsalar soji ba.”
Aiki kamar ko yaushe
Wani shafin Telegram mai suna Baza da ke da alaka da jami’an tsaron Rasha ya yada wani bidiyo dauke da wasu abubuwa masu tashi sama suna tunkarar kubbar Fadar Kremlin, kuma suka fashe tare da wani babban haske.”
Sanarwar da aka fitar daga ofishin shugaban kasa kuma ta ce an harbo jiragen saman a kan iyakar Fadar Kremlin, kuma ba a samu wata asara ba.
Kamfanin dillancin labarai na RIA ya ce Shugaba Putin ba ya Fadar Kremlin a lokacin da aka kai harin saboda yana can wajen gudanar da aiki a Novo Ogaryovo da ke wajen birnin Moscow.
Sakamakon samun labarin yunkurin kai harin, Moscow ta hana tashin jiragen sama marasa matuka a kasar.