Kuwait za ta buga kwafin littafin Kur’ani da aka fassara zuwa harshen kasar Sweden har guda 100,000. Za a rarraba kwafin a Sweden ne.
Kamfanin dillancin labaran Kuna ya bayar da rahoton cewa, gwamnatin kasar ta ce manufar wannan aiki shi ne jaddada ka'idoji da dabi'un addinin Musulunci na hakuri da zaman lafiya a tsakanin dukkanin 'yan adam.
Babban hukumar kula da bugu da kuma yada koyarwar Kur’ani mai tsarki da sunnonin Manzon Allah (SAW) da kuma kimiyyarsu ce ta bayyana hakan bayan wani umarnin da Firaminista Sheikh Ahmed Nawaf Al-Ahmad Al-Sabah ya bayar.
Ana ci gaba da shirye-shiryen buga kwafin Kur'anin da kuma ''rarraba su a Sweden'', a cewar shugaban hukumar buga takardu, Dr Fahad Al-Daihani.
Kona Kur’ani
Ya ce matakin da gwamnatin Kuwait ta dauka, ya yi shi ne don jaddada halayyar ''juriya'' da kuma koyarwar addinin Musulunci ta gaskiya.
Yunkurin ya biyo bayan nuna damuwa kan kan yadda ake yawan kona kwafin Kur'ani mai tsarki a wasu kasashen Turai, na baya-bayan nan shi ne wanda aka yi a kasashen Sweden da Jamus.
Abubuwan da suka faru sun haifar da bacin rai tare da Allah wadai daga al’ummomin kasashen duniya da kuma mayar da martani na diflomasiyya.
Hukumar kare hakkin bil adama ta Majalisar Dinkin Duniya na shirin kada kuri'a kan batun kyamar addini a ranar Laraba, bayan da Pakistan ta gabatar da wani kudiri da ta yi tir tare da Allah wadai da wulakanta Kur'ani da aka yi, inda ta nemi kasashen duniya da su fito don daukar matakin dakatar da irin wannan aika-aika a gaba.