Yajin aikin gama-gari ya karaɗe dukkan sassan Isra'ila, da manufar ƙara matsa lamba ga Firaminista Benjamin Netanyahu kan ya amince a tsagaita wuta nan take da kuma aiwatar da musayar fursunoni da ƙungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas.
Histadrut, ko Tarayyar ƙwadago ta Isra'ila ce ta ƙirƙiri gudanar da yajin aikin a ranar Litinin don kara isar ga kukan jama'a kan musayar fursunoni da ake tsare da su a Gaza.
Tashar watsa labarai ta gwamntin Isra'ila KAN ta ce yajin aikin ya yadu a dukkan fadin kasar bayan zanga-zanga mai karfi a yammacin da ya gabata.
'Yan kasar Isra'ila sama da rabin miliyan ne suka fita kan titunan birane irin su Tel Aviv, suna buƙatar da a dauki mataki nan da nan.
Damuwar da ta addabi kowa
Yajin aikin na kwana guda, wanda ya biyo bayan gano gawarwakin wasu 'yan Isra'ila da aka kama a Gaza, na bayyana tsananin damuwar Histadrut da kuma sauran jama'ar kasar, kan yadda gwamnati ke shakulatin ɓangaro da batun fursunonin yakin.
A martanin da ta mayar, gwamnatin Isra'ila ta kai ƙorafi Kotun Ƙoli don hana gudanar da zanga-zangar, kamar yadda jaridar Haaretz.
Yajin aikin ya kuma shafi harkokin sufuri a ƙasar, inda ka datakar da tashi da saukar jiragen sama a filin jirgin sama na ƙasa da ƙasa na Ben-Gurion na tsawon awanni biyu a ranar Litinin.
Dakatarwar daga karfe 08:00 zuwa 10:00 na safe, za ta yi tasiri kan tafiye-tafiye a tsawon makon nan.
Mahukuntan harkokin sufuri sun yi gargadi da cewa rufe filin jiragen saman na wani ɗan lokaci na iya kawo sauya lokutan tashin jirage har zuwa awanni 72.
An kashe su yayin hare-haren Isra'ila ta sama
Majiyoyin Histadrut sun yi nuni da cewa za a iya ci gaba da rufe filin jiragen saman na wasu awanni da dama, duk d a cewar ba a dauki matakin ƙarshe ba.
An yi hasashen cewa har yanzu Hamas na ci gaba da rike da sama da fursunonin yaƙi 100 a Gaza, kuma tuni aka kashe wasu daga ciki sakamakon hare-haren bam kan mai uwa da wabi da Isra'ila ke kai wa.
Hare-Haren da Isra'ila ke ci gaba da kai wa Gaza ya yi ajalin Falasdinawa sama da 40,700, mafi yawan su mata da yara ƙanana, da jikkata sama da 94,100, kamar yadda mahukuntan lafiya na yankin suka sanar.
Ci gaba da ƙawanya ga yankin ya janyo tsananin karancin abinci da tsaftataccen ruwan sha da magani, inda aka bar yankin a cikin mummunan yanayi.
Isra'ila na fuskantar zargin aikata kisan kiyashi a Kotun Kasa da Kasa, wadda ta bayar da umarnin da a dakatar da kai hare-hare kan garin Rafah na kudancin Falasdinu, inda sama da Falasdinawa miliyan guda suka nemi mafaka kafin a afka wa yankin a ranar 6 ga Mayu.