Yaki ya jefa mata masu ciki da masu shayarwa a cikin kunci a Gaza. Hoto: AFP    

Da idanunsa a bude, da ’yan hannayensa a dunƙule, Mohammed Kullab wanda jariri ne dan kwanaki kadan a duniya, inda ya fara rayuwa a Gaza a daidai lokacin da Isra’ila ke ragargazar yankin.

“Bai kamata a haifi mutum a wannan yanayin ba,” in ji mahaifiyarsa Fadwa Kullab, wadda ta samu mafaka a wata makarantar Majalisar Dinkin Duniya da ke Kudancin birnin Rafah da ke Gaza.

Kullab mai ’ya’ya bakwai yanzu, ta ce haihuwar Mohammed ce,“lokaci mafi tsanani a rayuwata.”

Kamar sauran wadanda suka haihu a wannan yanayi da AFP ta zanta da su a Gaza, ta ce ɗanta ya ƙi shan nononta.

“Ba na samun abinci mai kyau,” in ji Kullab, wadda ta bayyana cewa ta shayar da sauran ’ya’yanta guda shida lafiya kalau.

Ana shawartar mata masu shayarwa su sha aƙalla lita uku na ruwa a kullum, sannan su rika cin abinci mai gina jiki domin su samu ruwan nono sosai - amma a Gaza samun tsabtataccen ruwa da abinci mai kyau ƙara wahala yake yi kullum.

 Kusan biyu bisa ukun asibitocin Gaza sun kusa cika da marasa lafiya. AFP

Hare-haren Isra’ila a Gaza ya kara jefa yankin na Falasdinu da ke fama da matsanancin talauci cikin mawuyacin hali.

Sama da Falasdinawa 11,200 aka kashe, mafi yawansu kuma mata da kananan yara ne, kamar yadda Ma’aikatar Lafiya ta Gaza ta bayyana.

Kusan biyu bisa ukun asibitocin Gaza guda 36 da suke cike da marasa lafiya da aka jikkata, rashin man fetur da za a yi amfani da shi a janaretoci ya tursasa su dakatar da aiki.

Babban asibitin Gaza, Al Shifa, wanda yake cike da marasa lafiya yanzu ya fada cikin yanayi mara kyau saboda yaƙin, inda daraktan asibitin ya ruwaito cewa an binne gomman mamata a wani babban kabari a cikinsa.

Daga cikin wadanda suka rasu akwai bakwaini guda bakwai da suke samun kula musamman a sashen kula jarirai, kamar yadda Mataimakin Ministan Gaza, Youssef Abu Rish ya bayyana.

‘Zan iya rasa jaririna’

Mata da dama da suka haihu a Gaza suna cikin ƙunci, kamar Kullab wadda ta ce tana cikin damuwar kasa kare ƴaƴanta.

Ta ce ta kasa samun madarar jarirai da kuma ƙunzugunsu, kamar yadda ta bayyana a daidai lokacin da take ƙoƙarin rarrashin ɗanta da ke naɗe a cikin bargo.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce akwai mata masu juna biyu 50,000 sannan ana kiyasin samun haihuwa akalla 180 a kullum a Gaza. Hoto: AFP

Wata matar mai suna Najwa Salem mai shekara 37 ta ce jaririnta yana da cutar shawara, wadda ta bayyana alamarta da kasancewar idonsa da fatarsa sun yi launin rawaya.

Ciwon zai iya kara tsanani idan bai samu ruwan nono sosai ba, sannan ana magance rashin isassshen ruwa a jikin jariran ne ta hanyar fito da su su ga hasken rana.

Domin magance matsalar da za a iya samu, Najwa za ta so ta riƙa fita da ɗanta waje, amma ta ce tana fargabar hakan domin tsoron, “baraguzai da bama-bamai.”

A cikin ajin makarantar Majalisar Dinkin Duniyar da Najwa ke zama tare da wasu su kusan 70, ta ce tana cikin wani yanayi kasancewar tana fargabar wajen da aka mata tiyatar haihuwa ya yi gyambo.

Duk da cewa a asibiti ta haihu, ta ce dole aka sallame ta bayan kwana daya kacal “saboda suna da majinyata da yawa a asibitin.”

A waje kuma, ƙurar da ke tashi saboda hare-haren bama-bamai a yankin ta sa numfashi yana wahala, musamman ma ga jariran.

Wata mai dauke da juna biyun wata takwas, Umm Ibrahim Alayan ta ce tana fama da tari mai tsanani tun bayan da ta tsere daga yankinsu da aka tarwatsa da bam.

Tarin mai tsanani zai iya jawo mata nakuda da sauri saboda wahala, in ji ta.

“Ina cikin fargaba. Babban burina shi ne na haihu lafiya,” in ji ta, sannan ta kara da cewa, “Ina tsoron kar in rasa jaririn.”

'Yanayi mai matuƙar muni

Wani babban jami’in Asusun Majalisar Dinkin Duniya na kula da yawan jama'a wato UNPF da ke yankin, Dominic Allen ya ce mata a Gaza, “Ba su da mafaka, babu wani waje da za su samu tsaro.”

Majalisar Dinkin Duniyar ta ce sama da mata 50,000 ne suke dauke da juna biyu, sannan an kiyasta cewa aƙalla mata 180 ke haihuwa a kullum a yankin Gaza mai mutum miliyan 2.4.

“Mun kididdige cewa kusan kashi 15 na haihuwar da ake yi suna zuwa da matsaloli, inda suke bukatar kula ta musamman,” in ji Allen.

Likitoci sun ce a ranar Lahadi kadai sun yi tiyatar haihuwa guda 16 ba tare da allurar rage radadi ba. [Photo: AFP]

Yakin ya jawo “tashin hankali a yankin,” wanda kuma hakan zai, “jawo matsalolin haihuwa da za su iya jawo barin ciki,” in ji shi.

Sashen na Majalisar Dinkin Duniya ya ambato “fargabar’ da daya daga cikin matan da aka sallama bayan ta haihu da awa uku ta shiga."

An ce akwai karancin jinin da za a iya ƙara wa wadanda jini ya yanke musu, kuma babu magunguna da kayan aikin wanke rauni bayan an yanke cibiya.

Zuwa yanzu, sashen na Majalisar Dinkin Duniya ya samu damar kai agajin kayan haihuwa guda 8,000 zuwa Gaza, inda a cikin kowane ƙulli, akwai dukkan kayayyakin haihuwa da ake bukata.

Sai dai wannan zai kawo sauki ne kawai a wani bangaren, sannan Ma’aikatar Lafiyar Gaza ta ce wasu matan suna haihuwa ba tare da ungozoma ba saboda yanayin yadda asibitocin suke cike.

“Kuncin da ake ciki a Gaza ya wuce maganar ayyukan jinƙai. Al’ummar ne suke cikin bala’i,” in ji Allen.

Kungiyar agaji da ke cigaba da aiki a Arewacin Gaza a sansanin gudun hijirar Jabalia da aka kai wa farmaki, ita ce ActionAid da ke taimakon mata a asibitin Al Awda wanda yanzu haka ya kwashe kwanaki ba tare da wutar lantarki ba.

Likitoci sun ce sun yi wata mata 16 tiyatar haihuwa a ranar Lahadi ba tare da allurar rage radadi ba, da sauran magungunan da ake bukata.

“Dubban matan Gaza suna sadaukar da rayuwarsu ne wajen haihuwa, inda suke amincewa a musu tiyata ba tare da allurar rage radadi ba da sauran kayayyakin haihuwa,” in ji Riham Jafari na ActionAid.

“Matan nan sun cancanci samun kula ta musamman, da kuma cancatar haihuwa a waje mai kyau. Maimakon hakan, ana tilasta musu suna haihuwa a cikin mawuyacin hali.”

AFP