Kafar yada labarai ta China ta bayyana cewa, Xi Jinping yakafa tarihi inda ya sake samun damar kara wa’adi daya a kan mulkin kasar, a karkashin Jam’iyyar Kwaminisanci da ya zama mafi karfi a cikin ta tun bayan wanda ya kafa ta Mao Zedong.
Kwamitin Zaratrawa na Jam’iyyar Kwaminisanci ta China a ranar Lahadi ya zabi Xi a matsayin Sakatare Janar din ta na tsawon wasu shekaru biyar, kamar yadda Xinhua ya rawaito, wanda hakan kekarkatar da kasar zuwa ga mulkin mutum daya, bayan wasu shekaru da aka yi na shugabanci tsakanin ‘yan bokon kasar.
Nadin nasa ya biyo bayan wata tattaunawar sirri da manyan jam’iyyar suka gudanar a Beijing, wanda amincewa da Xi ya tilastawa ‘yan adawa janyewa daga neman shugabantar kasar.
A watan maris ne majalisar dokoki za ta bayyana Xi a matsayin Shugaban Kasar China a karo na uku.
Taro karo na 20 da aka kammala a ranar Asabar ya bayar da dama ga sabbin zababbun Shugabannin Jam’iyyar kusan su 200 sun sake zama a ranar Lahadi don zabar kwamitin Zartarwa--- Kwamitin Mulki Mafi Girma a China wanda Xi yake zaune a kai.
Mayar da Hankali Ga Mulki
Tun bayan zama shugaban kasar shekaru da suka gabata, Xi ya mayar da hankali kar karfin mulki sama da duk wani jagoran kasar na zamani, in banda Mao.
A shekarar 2018 ne ya cire dokar da ta takaitawa shugabanni wa’adi biyu,wanda hakan ya ba shi damar ci gaba da jagoranci har inna-naha.
Xi ya shaida yadda China ta zama kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya, fadada aiyukan soji da zama mai fada a ji a duniya, wanda hakan ya janyowa Amurka ta fara adawa da ita.
Duk da kusan yana jagoranci ba tare da kawo masa tsaiko ba, Xi na fuskantar manyan kalubaloli a shekaru biyar masu zuwa, da suka hada da kula da tattalin arzikin kasar da bashi ya yiwa katutu, da kuma adawa daga Amurka.