Darajar kudin kasar, wato shekel ya yi karyewar da bai taba yi ba a shekara 14, sannan ma’aunin kasuwar hannun jarin kasar ya koma kashi 10 a bana. Hoto AA      

A makon jiya ne Firaministan Isra’ila Banjamin Netanyahu ya yi hasashen samun yanayin zaman lafiya mai dorewa a yankin Gabas ta Tsakiya saboda yadda a cewarsa Isra’ila take kara samun karbuwa a yankin.

Amma zuwa yanzu kuwa, duba da yadda yakin Isra’ila da Gaza ya shiga mako na hudu, wannan kudurin da alama ya sha ruwa.

Tattara sojojin jiran ko- ta-kwana guda 360,000 da kwaso ’yan Isra’ila guda 250,000 kamar yadda kididdigar da sojojin Isra’ila suka bayar ta nuna, ya kawo cikas ga harkokin kasuwanci da dama a kasar.

An rufe wuraren cin abinci da otel-otel da dama. Kamfanonin jiragen sama sun tsagaita jigilar fasinja zuwa Isra’ila, masu yawon bude ido da dama sun fasa zuwa kasar.

An kulle wata babbar tashar iskar gas a kasar, gonaki da dama sun lalace saboda rashin ma’aikata, sannan dubban ma’aikata sun rasa ayyukansu.

Isra’ila ta rantse sai ta ga bayan kungiyar Hamas a Gaza, wadda ta kashe mata mutum 1,400, sannan ta yi garkuwa da sama da 240 a harin da ta kai Kudancin Isra’ila a ranar 7 ga Oktoba.

Hare-haren jiragen sama Isra’ila sun tarwatsa tare da kashe sama da mutum 8,000 a Gaza kamar yadda Ma’aikatar Lafiya ta sanar a Gaza.

Tattalin arzikin Isra’ila na dawowa da ƙarfi bayan yake-yaken da ta yi a baya, amma da alama wannan karon za a dauki lokaci ba a watstsake ba, watakila a dauki watanni, domin burin sojojin kasar shi ne kawo karshen Hamas, ba wai dakile mayakan ba.

Fadadar yakin shi kansa wata barazanar ce daban. Yanzu haka Isra’ila tana wasu yake-yaken guda uku ta karkashin kasa-Da Lebanon, da yankin West Bank da ta mamaye da kuma Syria.

Dadewa tana fuskantar yake-yake daban-daban a lokaci daya zai sa tattalin arzikin ya dade bai farfado ba kamar yadda suka saba gani a baya.

Sannan ko kafin a fara yakin, tattalin arzikin kasar ya riga ya fara taɓarɓarewa tun bayan yunƙurin Netanyahu na rage karfin bangaren shari’a, wanda bai samu karbuwa ba sosai.

Tallafi kadai ba zai iya gyara tattalin arzikin ba

Ma’aikatar Kudi ta Isra’ila ta bayyana tsarin tallafin inganta tattalin arziki da a ciki akwai bayar da tallafin Dala biliyan 1 ga ’yan kasuwar da yakin ya shafa.

Masu sharhi sun ce wannan ba zai yi wani kataɓus ba, sannan suka buƙaci a karkata wasu biliyoyin dalolin zuwa ga wasu hanyoyin daban na shirya sabuwar yarjejeniya zaman lafiya tsakanin masu ra’ayin Yahuduwa zalla da masu maraba da baki.

A makon nan ma, wani taron masana tattalin arziki su 3,000 sun yi kira ga Netanyahu da Ministan Kudin Isra’ila Bezalel Smotrich da “Su bi a hankali!”

“Rudanin da Isra’ila ta shiga yana bukatar tunani mai kyau ne wajen yin abubuwan da kasar ta fi bukata da kuma karkatar da kudade zuwa magance matsalolin da yakin ya haifar da taimakon wadanda yakin ya shafa da kuma gyara tattalin arziki,” in ji su a wata wasika, inda a ciki suka yi hasashen kudaden da ake kashewa a yakin zai iya cin sama da biliyoyin daloli.

Sai suka shawarci Netanyahu da Smotrich da su, “gaggauta dakatar da kashe kudadeba kan duk wani abu da bai da muhimmanci ga yakin da kuma inganta tattalin arzikin kasar-sannan abu na farko mafi muhummanci shi ne kasafta kudi domin sulhu da yarjejeniyar hadaka.”

Smotrich, wanda jagora ne na masu barka da baki ya bayyana a gidan rediyon sojin Isra’ila a makon jiya cewa, “Duk wani abu da bai shafi yakin ba, kuma bai shafi inganta tattalin arzikin kasar ba, za a dakatar da shi,” inji shi, amma har yanzu akwai shakku a batun.

Kididdigar harkokin kudi ta nuna akwai matsala. Darajar kudin kasar, wato shekel ya yi karyewar da bai taba yi ba a shekara 14, sannan ma’aunin kasuwar hannun jarin kasar ya koma kashi 10 a bana.

Bangaren harkokin fasahar harkokin kasuwancin zamani, wanda shi ne jagaban tattalin arzikin Isra’ila ya fara tabarbarewa ne tun kafin a fara yakin.

Cibiyar Fitch Ratings da Cibiyar Moody’s Investors Service and S&P duk sun yi gargadin cewa idan yakin ya cigaba, zai kawo cikas ga kokarin kasar na biyan basussukan da take yi.

Babban Bankin Isra’ila ya dawo da hasashen habaka tattalin arzikin kasar zuwa kashi 2.3 maimakon kashi 3- idan ma an samu nasarar dakile yakin ke nan a Kudancin kasar.

Babban Bankin kasar ya kasafta Biliyan $30 domin daga darajar kudin kasar ta shekel.

A wani taron manema labarai a wannan makon, Gwamnan Babban Bankin kasar Amir Yaron ya nanata juriyar tattalin arzikin kasar da ya bayyana da, “Mai fadi da karfi.”

“Tattalin arzikin Isra’ila ya san hanyoyin za yake bi wajen dawowa da karfi a duk lokacin da aka samu matsala a baya, ina da yakinin wannan karon ma hakan zai faru,” in ji Yaron.

Kasar ta fara yakin ne da Biliya $200 a Asusun Ajiya na kasashen waje. Sannan gwamnatin Biden ta bukaci majalisa ta amince da dadin tallafin dala biliyan 14 domin agajin gaggawa a Isra’ila, wanda ya kunshi tallafin kayayyakin yaki, bayan na dala biliyan 3.8 da take samu duk shekara.

Hauhawar farashi

A farkon yakin, Isra’ila ta bukaci kamfanin Chevron ya dakatar da aiki a ma’aikatar iskar gas ta Tamar domin rage barazanar kai harin rokoki yankin.

Masanin makamashi, Amit Mor ya kiyasta cewa daina aikin kamfanin zai sa kasar ta yi asarar harajin dala miliyan 200 duk wata.

Idan kungiyar Hezbollah ta Lebanon ta shiga yakin da karfinta, hakan zai shafi aikin sauran ma’aikatun iskar gas guda biyu na kasar, ciki har da mafi girmansu, kamar yadda Mor ya bayyana. Amma kuma ba ya tunanin yakin zai cigaba da shafar aikin hako iskar gas din.

“Dukkan masu gwazba yakin sun san akwai kasada babba a cikin hakan," in ji shi.

Tun kafin a fara yakin, Isra’ila-wadda kasa ce mai karfin kasuwanci da kasashen da take hammayar tattalin arziki da su kasashen Yammacin Turai- ta fara tangal-tangal.

Baitul malinta, wanda a baya yake samun kudaden shiga daga harkokin masu zuba jari a kasuwancin zamani, ya samu koma baya ne tun bayan yunkurin rage karfin bangaren shari’ar kasar.

Gwamnatin kasar ta ce alkalan kasar, wadanda ba zaben su ake yi ba, sun samu karfi mai yawa, amma kuma masu kushe hakan na ganin su alkalan ne kadai suke iya taka wa ’yan siyasa birki.

Haka kuma fargabar yanayin tafiyar da gwamnatin Isra’ila da hauhawar farashin kayayyaki da yadda aka samu koma baya a zuba jari a harkokin kasuwancin zamani na bara ya taimaka wajen kawo cikas ga tattalin arzikin kasar.

Hukumar Habaka Kirkire-kirkire ta gwamnatin kasar ta bibiyi sababbin kamfanoni a lokacin da ake tsaka da yakin, inda ta gano suna fama da cikas wajen samun jari da kuma matsalar tafiyar yawancin ma’aikatansu aikin sojin ko- ta-kwana.

“Suna cikin abubuwan da suke barazana ga wasu daga cikin kamfanonin kasuwancin zamani na kasar,” kamar yadda Babban Jami’in, Gudanara Dror Bin ya bayyana.

“Kamfanoni da dama na fuskantar barazana rufewa nan da wasu ’yan watanni masu zuwa,” in ji Bin.

AP