Mohammed Deif wani nakasasshen mayaki ne da aka haifa a sansanin ’yan gudun hijira da ke birnin Gaza. Hoto: AP Archive

Deif, jagoran rundunar Qassam, wadda ita ce bangaren soji na Kungiyar Hamas ce kan gaba wajen kai hare-haren ba-zata da kungiyar ta Falasdin ta kai wa Isra’ila.

Hare-haren da Hamas ta kai ta sama da ta kasa da ta ruwa a Isra’ila sun jawo hankalin mutane ya koma kan Mohammed Deif, wanda wani nakasasshen mayaki ne da aka haifa a sansanin ’yan gudun hijira da ke birnin Gaza a kasar ta Falasdin.

Tun a shekarar 2002 ce Deif yake jagorantar bangaren sojin na Hamas, wato rundunar Qassam.

Akalla sau bakwai yana tsallake rijiya da baya a yunkurin da kasar Isra’ila take yi na kashe shi, inda daga cikin hare-haren da aka kai masa din aka kashe matarsa da ’ya’yansa, ciki har da jariri. Haka kuma ya rasa idonsa guda daya, da hannu daya da kafa daya.

Kamar Sheikh Ahmed Yassin, wanda shi ma wani nakasasshen jagora ne na Hamas da harin jirgin saman Isra’ila ya kashe a shekarar 2004, shi Deif mai shekara 57 ya kasance yana jagorantar Rundunar Qassam din a keken guragu na tsawon shekara 20.

“Yana da kirki sosai,” in ji Ghazi Hamad, daya daga cikin manyan Hamas a lokacin da yake siffanta Deif, wanda sunansa ke nufin bako a harshen Larabci saboda kasancewarsa mai yanayi da makiyaya na yawan yin kaura domin guje wa Isra’ila.

Hamad ya hadu da Deif ne a karshe-karshen shekaun 1980s, sannan suka zama abokai lokacin da aka fara fafutikar Intifada ta farko-Fafutikar kwato ‘yancin Falasdinawa.

A gidan yari, sai Deif “ya rika yi mana zanen barkwanci domin mu dariya,” inji Hamad. Amma dai Deif ya nuna alamar yana da manufa, “Farkon rayuwarsa a Hamas, ya fi mayar da hankali a kan harkokin soji,” kamar yadda Hamad ya bayyana wa Financial Times.

Bayan hare-haren da Hamas ta kai wa Isra’ila, wadda rabon ta da ga irin su tun a yakin

Baraguzan Masallacin Yassin wanda harin sama na Isra'ila ya rusa. 

Larabawa da Isra’ila a shekarar 1973, sai muradun Deif suka kara bayyana.

“Duba da yadda ake zaluntar mutanenmu, da danne mana hakki da kwace mana yanki da kin yin biyayya ga dokokin duniya, da kuma duba da yanayin goyon bayan Amurka da wasu kasashen Yamma, mun yanke shawarar a yi ta, ta kare kawai.

Da hakan ne makiyi zai gane cewa an wuce lokacin da zai yi zalunci, ba tare da an mayar masa da martani ba,” kamar yadda sanarwar jagoran Rundunar Qassan din ta bayyana.

Me yake yi?

Kamar sauran ’yan Kungiyar Hamas, Deif ya dade yana kira da a kai wa Isra’ila hari.

A hare-haren da Rundunar Qassam din ta jagoranta, kungiyar ta Falasdinawa ta samu nasarar kamawa tare da tsare gomman sojojin Isra’ila, wanda ake tunanin har da mai mukamin Manjo Janar a ciki.

Ba kamar sauran jagororin kasar Falasdin din ba, shi Deif ba ya sha’awa kuma ba ya shiga cikin rikicin shugabancin kasar, inda shi ya fi mayar da hankalinsa a kan yaki da Isra’ila, kamar yadda masana suka bayyana.

A karshe-karshen shekarar 2010, Deif ya rubuta wata makala inda a ciki ya bayyana wasu daga cikin muradun kungiyar kamar yadda shi yake so, inda a ciki ya ce, “Kasar Falasdin za ta cigaba da zama mallakinmu, ciki kuwa har da Kudus da Masallacin Kudus da biranenta da kauyukanta tun daga tekun maliya zuwa tekun Jordan, tun daga Arewa zuwa Kudu. Ke (Isra’ila) ba ki da hakkin mallakar ko inci daya a ciki.”

Daga cikin abubuwan da suke jawo kai hare-haren Hamas a Isra’ila na kwanan-nan, akwai rikicin baki da ’yan gari a Masallacin Kudus, wanda shi ne wuri na uku mafi daraja a wajen Musulmi.

Shekarun bibiya

Har yanzu babu cikakken bayani a game da Deif. Daga cikin abubuwan da ba a sani ba a game shi har da iyayensa da kuma yaya kuruciyarsa ta kasance.

Daga cikin alamomin kasancewarsa mai tsananin sirri akwai rashin samun hotonsa mai kyau har yanzu. Sashen leken asirin Isra’ila ya yi amannar cewa asalin sunansa Mohammed Diab Ibrahim al-Masri.

Duk da cewa suna shan suka na gaza ganowa tare da dakila lokacin da Hamas ke shirye-shiryen kai hare-hare, sashen na leken asiri ya bayyana cewa ‘yan uwan Deif suna cikin mayakan Falasdin na Fedayeen, wadanda a shekarun 1950s suka fafata da Isra’ila.

Kamar wasu jagororin Falasdinawa da dama wadanda suka shiga cikin fafutikar kwatar ‘yancin kasar tun daga jami’a, shi ma Deif ya fara alaka ne da kungiyar Hamas tun daga Jami’ar Musulunci ta Gaza.

A farko-farkon shekarun 1990, Deif da wasu, ciki har da asalin wadanda suka kirkiri kungiyar ta Hamas sun yi alhinin yarjejeniyar da Shugaban Kungiyar Kwatar ‘Yancin Falasdinawa wato Palestinian Liberation Organisation (PLO), Yasser Arafat ya shiga a birnin Oslo, inda ya amince da barin wasu yankunan na Falasdin ga kasar Isra’ila.

Deif ya shiga Rundunar Qassam ce wadda aka kirkira jim kadan bayan yarjejeniyar ta Oslo a karkashin jagorancin Yahaya Ayyash da Adnan al-Ghoul wadanda suka kasance biyu daga cikin manyan masu tsare-tsaren Kungiyar Hamas kafin kasar Isra’ila ta kashe su.

Deif ya shiga cikin tsare-tsaren rundunar da dama ciki har da hare-hare da suka yi sanadiyar mutuwar sojojin Isra’ila da dama a cikin kasarsu. Haka kuma Deif yana cikin wadanda suka jagoranci hare-haren da Falasdinawa suka kai wa Isra’ila a fafatikar Intifada ta biyu a tsakanin 2000 zuwa 2005.

TRT World