Majalisar Dinkin Duniya ta ce yakin ya raba maif yawan mazauna yankin dan karami da ke gabar teku da matsugunansu, kuma yunwa na addabar su sakamakon kawanya, a yayin da sanyi ke kara ta'azzara. / Hoto: Reuters

Tun lokacin da Isra'ila ta ƙaddamar da yaƙi kan Gaza da ta mamaye, shugabannin Isra'ila sun yi kalamai masu karo da juna kan makomar yankin na Falasdinawa bayan an gama yaƙi, inda kowa yake tambayar wanne mataki Tel Aviv za ta dauka.

A ranar 7 ga Nuwamba, Firaminista Benjamin Netanyahu ya ce "Isra'ila za ta dauki nauyin samar da tsaro a Gaza har iilla ma sha Allah."

Bayan kwanaki uku, ya sake cewa ƙasarsa ba ta da niyyar 'mamayar' ko mulkar Gaza, amma kuma "dole a raba yankin da mayaƙa, masu tsaurin ra'ayi da sake gina shi."

A ranar 16 ga Disamba kuma, Netanyahu ya sake bayyana cewa, "Ba za ba mu bayar da damar da Fatah za ta maye gurbin Hamas a Gaza ba, wannan kaucewa babbar ƙawarta Amurka ce, wadda ke fatan ganin Fatah ta karɓe iko da Gaza wanda hakan zai bayar da damar samar da kasashe biyu na Falasdinu da Isra'ila.

Masu tsaurin ra'ayi daga ministocin Netanyahu na ci gaba da kira da a sake mamaye Gaza da Hamas, kuma a samar da tsarin da zai kawar da kungiyar gwagwarmayar ta Falasdinawa gaba daya.

TRT World ta tattauna da ƙwararru guda biyu - tsohon babban jami'in Ma'aikatar Isra'ila, da tsohon jakadan Majalisar Dinkin Duniya a yankin Falasdinu da aka mamaya - don fahimtar wadanne irin sauyin gudanarwa da siyasa da tsaro za a samu bayan Isra'ila ta kawo ƙarshen yaƙin da take yi a Gaza.

"Isra'ila ba za ta jagoranci Gaza ba" in ji Kobi Michael, wanda ya taɓa riƙe muƙamin mataimakin darakta janar kuma shugaban sashen kula da harkokin Falasdinu a Ma'aikatar Isra'ila, yayin tattaunawa da TRT World.

Ya bayyana cewa ya kamata a kafa kwamitin amintattu na kasashen Larabawa da suka hada da Masar da Jordan da Hadaddiyar Daular Larabawa da Saudiyya - tare da wasu Ƙasashen Yamma irin su Ingila da Faransa da Jamus da Amurka, su jagoranci yankin na Gaza.

Michael ya kuma ce "Akwai bukatar kafa sabuwar Gwamnatin Falasdinawa a Yammacin Gaɓar Kogin Jordan da za ta dinga kula da rayuwar Falasdinawa a yankin."

Ya ci gaba da cewa "Wataƙila, a nan gaba bayan shekaru biyar ko shida wadannan yankuna na Gaza da Yammacin Gabar Kogin Jordan za su haɗe waje guda a matsayin siyasa daya da shugabanni guda, ba wai zaman su yanki daya kawai ba."

Michael, wanda babban mai bincike ne a Cibiyar Nazarin Tsaron Kasa da ke Tel Aviv, ya ce bai ga alamun a nan gaba Isra'ila za ta bayar da damar Gaza da Yammacin Gabar Kogin Jordan su hade waje guda ba."

Idan aka samu haɗewa irin ta siyasa tsakanin Gaza da aka mamaye da Yammacin Gabar Kogin Jordan, to za a iya kafa 'yantacciyar kasar Isra'ila a nan gaba, amma a yanzu kamata ya yi a mayar da hankali wajen sake kafa shugabancin Falasdinawa.

Hukuncin bai daya

Yaƙin da Isra'ila ke yi a Gaza ya shiga rana ta 73 - inda ya yi sanadiyyar mutuwar aƙalla Falasdinawa 19,435 da suka haɗa da yara ƙanana 7,729, inda sama da mutum 52,286 suka samu raunuka.

Ana fargabar dubban Falasdinawa na kwance a ƙarƙashin ɓaraguzan gine-ginen da aka rusa. Majalisar Dinkin Duniya ta ce yaƙin ya raba mafi yawan jama'ar Gaza miliyan 2.3 da matsugunansu, kuma yunwa ta jigata yankin da sanyin hunturu ke addaba a yanzu haka.

Yaƙin ya faro ne a yayin da Hamas ta kai wani hari na ba-zata a ranar 7 ga Oktoba kan matsugunai da garuruwan Isra'ila da ke iyakarsu da Gaza.

Hamas ta bayyana cewa sun kai harin ba-zata kan babbar abokiyar adawarsu Isra'ila ne sakamakon yawan harin da ake kai wa Masallacin Ƙudus da rikicin 'yan kama guri zauna a Yammacin Gabar Kogin Jordan da kuma sake dawo da batun 'Falasdinu' kan teburin tattaunawa.

A wani yunƙuri na ɗaga murya, mayaƙan Hamas sun kutsa kai a yankuna da ke da nisan kilomita 22 daga iyakar Gaza, inda suka kashe 'yan Isra'ila 1,139.

A wasu wuraren, an bayyana cewa sun kashe sojoji 373, inda su kuma dakarun Isra'ila ke ta ƙoƙarin mayar da martani.

Bayan dawowa Gaza, sun kuma kama wasu mutanen 240, da suka hada da jami'an sojin Isra'ila da farar hula.

Daga baya an saki gwamman fursunonin yakin a madadin Falasdinawan da aka ɗaure a gidajen kurkukun Isra'ila wadanda su ma aka sallame su.

Tun wannan lokaci, Isra'ila na ta yin ruwan bama-bamai kan gaza ta sama da ta ruwa da ta ƙasa, inda a yanzu take ƙoƙarin ƙwace iko da iyakokin yankin matuƙar ta yi nasara kan Hamas, wanda mayaƙanta suka kashe sojojin Isra'ila 129 tare da yin ikirarin lalata tankokin yakin Isra'ila da dama.

Kungiyar na kuma riƙe da 'yan Isra'ila 140 inda suke yawan nuna bidiyonsu don nuna adawa da shiga yankunansu da tankokin yakin Isra'ila suka yi.

A yayin da ake ci gaba da gwabza fada, kwararru na cewa Falasdinawa da suaran kasashen duniya za su kalli duk wani yunƙurin tsaro na Isra'ila a Gaza a matsayin mamayar soji.

Jibge dakarun Isra'ila har inna naha

Michael Lynk, wanda ya yi aiki a matsayin mai bayar da rahoto na musamman na MDD kan kare hakkokin ɗan'adam a yankunan Falasdinawa da aka mamaye daga 2016 zuwa 2022, ya shaida wa TRT World cewa Isra'ila ba za ta iya kakkaɓe Hamas daga Gaza ba, saboda ba za ta so ta bar sojoji a yankin ba.

Lynk ya ce "Isra'ila na ƙara zama a yankin, yanayin tsaro na ƙara lalacewa".

Nakba ta biyu, ko raba mutane da dama da matsugunansu a 1948 - wanda shi ne abun da Isra'ila ke son cimmawa - ba su samu nasara ba, saboda Larabawa da sauran kasashen yankin sun ƙi karɓar Falasdinawa, suna kallon hakan a matsayin cin amana ga gwagwarmayar Falasdinawa, in ji Abdullah Agar, wani mai nazari kan sojojin Turkiyya yayin tattaunawa da TRT World.

Agar ya ce "Babu wata kasa a yankin da ke zama wani bangare na raba Falasdinawa da yankinsu har abada."

Lynk ya ƙara da cewa a yayin da kasashen Yamma za su iya taka rawa a Gaza bayan gama yakin, kokarin da za su yi na sake gina yankin zai janyo sabon rikici da tashin-tashina.

Lynk ya ce "Amurka da Yammacin duniya z asu iya kawo taimakon jinkai ga Gaza ta hanyar amfani da Hukumomin MDD, amma za su sanya idanu kan kasashen Gulf na Larabawa kan su bayar da kudaden sake gina Gaza."

"Wannan zai zama babbar gabar tashin hankali tsakanin Amurka da Larabawan Gulf, wanda z asu yi ta mamakin me ya sa z aa ce su bayar da kudaden sake gina Gaza da Isra'ila ta rusa."

"Asali dai kamata ya yi Majalisar Dinkin Duniya ta dauki alhakin sanya idanu wajen sake gina yankin Gaza," in ji shi, ind aya kuma kara da cewa Larabawa ko Kasashen Musulmai za su so su samar da jagoranci ko tsaro a wannan waje, saboda za a iya kallon hakan a matsayin wani bangare na gwagwarmayar Amurka.

Da yake bayyana cewar rusau din yankin Gaza ya zama kama madubin abun da aka gani a Rakka da ke Siriya da Falluja a Iraki, Michael ya kuma ce za a dauki tsawon lokaci da kashe kudade da yawa wajen sake gina yankin.

"Za a dauki shekaru da yawa wajen sake gina yankin Gaza" in ji shi, yana mai karawa da cewa kwamitin kasashe amintattu ne za su dauki nauyin sake gina."

Ya ce "Muna magana ne game da yanayi mai wahala, aiki da zai lashe kudade da yawa, kuma mutane za su zama karkashin yanayi mara kyau na tsawon lokaci."

Babu alamun samun zaman lafiya

Isra'ila ta janye dakarunta da 'yan kama guri zauna daga Gaza a 2005, amma ta ci gaba da kawanya ga yankin ta hanyar rufa sararin samaniyarta, iyakar teku, rajistar sabbin haihuwa da tsallaka iyaka, sai dai iyakar shiga Masar kawai.

Ƙawanyar da aka yi wa Falasdinu ta sanya Isra'ila hana kai kayan marmari busassu, kayan kwalan da makulashe, tufafi, litattafai, tukwane, kayan wasan yara da ma kayan gudanar da buki.

Hamas ta karbe iko da iyakokin tekunta daga Gwamnatin Falasdinu a 2007, bayan an yi mata kawanya tare da hana ta gudanar da shugabanci duk da lashe zaben da ta yi a shekarar da ta gabaci wannan.

Tun wannan lokaci, Isra'ila da Masar suka sanya kawanya mai kassara mutane a Gaza.

Wannan rikici na Gaza da ake ci gaba da yi na iya sabunta yunkurin da duniya ke yi na ganin an warware rikicin ta hanyar kafa kasashe biyu, amma jami'an gwamnatin Isra'ila sun ki nuna goyon bayan wannan mataki.

Asali ma, Firaminista Netanyahu ya yi kurarin cewa a shekaru 16 da ya yi a kan mulki, ya hana tabbatuwar burin kafa 'yantacciyar kasar Falasdinu, inda ya tunzura tsohon jakadan Amurka a Isra'ila, Martin Indyk wanda ya kira Netanyahu da mai yin karya ga shugabannin duniya a tsawon wadannan shekaru.

Indyk ya ce "Wato duk alkawuran da ya dinga yi wa shugabannin duniya game da kafa kasashe biyu karya da yaudara ce."

Akwa babban kalubale a gabas ta Tsakiya wajen samar da zaman lafiya, a lokaci da shugabanni masu tsaurin ra'ayi suke shugabantar Isra'ila.

"Za a iya samun zaman lafiya ne kawai idan sabon shugabancin falasdin zai mayar da hankali kacokan da yin aiki tukuru don tabbatuwar 'yantacciyar kasar Falasdin," in ji Michael jami'i a Cibiyar Nazarin Harkokin Tsaron Kasa.

Sai dai kuma Lynk, tsohon babban jami'in MDD, na kallon babu alamu ko hasken samun zaman lafiya tsakanin Isra'ila da Falasdin bayan gama wannan yaki.

Ya ce "akwai babbar adawa a fagen siyasar Yahudawa kan samar da 'yantacciyar kasar Falasdin."

"Kuma gwamnatin Biden ba za ta so zuba jari sosai wajen matsin lamba kan Isra'ila ta janye daga yankunan Falasdinawa da ta mamaya ba, musamman a shekarar da za a gudanar da zaben shugaban kasar."

TRT World