Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan da takwaransa na Iraƙi Fuad Hussein sun gana a Bagadaza, babban birnin Iraƙi. ranar 14 ga watan Maris, 2024. / Hoto: Reuters

Turkiyya ta yi maraba da matakin Majalisar Tsaron Iraƙi na ayyana ƙungiyar ƴan ta'adda ta PKK a matsayin haramtacciya a ƙasar.

Iraƙi ta sanar da matakin ne a wata sanarwar haɗin-gwiwa da ta fitar ranar Alhamis bayan taro kan sha'anin tsaro tsakanin Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan da takwaransa na Iraƙi Fuad Hussein tare da tawagoginsu a Bagadaza, babban birnin Iraƙi.

An fitar da sanarwar ce a yayin da shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan yake shirin kai ziyara Iraƙi bayan watan azumin Ramadana — matakin da ake gani zai yauƙaƙa dangantakar da ke tsakanin ƙasashen biyu.

Dukkan ƙasashen sun tabbatar da cewa za a ɗauki ƙwararan matakai wajen tabbatar da cewa ziyarar da Shugaba Erdogan zai kai Iraƙi ta kasance mai cike da tarihi, in ji sanarwar.

"Mun tattauna a kan batutuwa daban-daban da suka sahfi yankinmu da kuma ziyarar da za a kawo nan gaba," a cewar ministan harkokin wajen Iraƙi a saƙon da ya wallafa a shafinsa na X.

Hussein ya ƙara da cewa, "Mun jaddada buƙatar ganin an haɗa kai a fannonin tsaro da cinikayya da makamashi da harkokin ruwa da ilimi da dukkan abubuwan da ƙasashenmu za su mora."

Ɓangarorin biyu sun tattauna kan matakan da za su ɗauka kan ƙungiyar an ta'adda ta PKK da ƙawayenta da ke amfani da iyakokin Iraki wajen kai hari a Turkiyya.

AA