Ta ƙyanƙyashe ƙwanta na ƙarshe a shekarar 2021 inda aka yi hasashen da ƙyanƙyashe ƙwayaye fiye da 30 a tsawon rayuwarta. / Hoto: Reuters

Wata tsuntsuwa wadda masana kimiyya suka yi amanna cewa ita ce mafi tsufa a duniya ta saki ƙwai, kamar yadda masana suka tabbatar.

Hukumar Kula da Kifaye da Namun Dawa ta Amurka ta ɗauki hotonta a wani gandun tsuntsaye da dabbobi da ke tsibirin pacific ta ɗauki hoton tsuntuswar a lokacin da take zagaye da ƙwan nata.

Masana kimiyya sun soma kula da tsuntsuwar ne tun a shekarar 1956 a lokacin da take da shekara biyar.

Ta ƙyanƙyashe ƙwanta na ƙarshe a shekarar 2021 inda aka yi hasashen ta ƙyanƙyashe ƙwayaye fiye da 30 a tsawon rayuwarta.

AA