Ruwan saman ya yi ɓarna sosai da lalata gidaje da kashe dabbobi a faɗin jihar. / Photo: AP Archive

Mutum 24 ne suka mutu sakamakon faɗuwar da tsawa ta yi a kansu, yayin da wasu kimanin 23 suka samu raunuka, sakamakon mamakon ruwan sama da aka tafka a jihar Gujarat da ke yammacin Indiya, cikin kwanaki biyun da suka gabata, kamar yadda jami'an gwamnati suka bayyana.

An yi ruwan sama kamar da bakin ƙwarya tare da tsawa da ƙanƙara a ranakun Lahadi da Litinin a jihar, inda wasu wuraren suka samu ruwan sama mai yawan milimita 144 cikin sa'o'i 24, wanda ya ƙare a safiyar ranar Litinin, kamar yadda bayanan gwamnatin jihar suka nuna.

Ruwan saman ya yi ɓarna sosai da lalata gidaje da kashe dabbobi a faɗin jihar.

Ba a tsammaci irin wannan mamakon ruwan sama ba a Gujarat a cikin watannin hunturu, kuma ruwan saman mai ƙarfi ya zo wa mutane a ba-zata.

"Za mu fara bincike nan ba da jimawa ba don tantance yawan asarar da aka yi,” in ji Ministan Noma na Gujarat, Raghavij Patel a ranar Litinin, inda ya ƙara da cewa za a biya diyya ga waɗanda abin ya shafa bisa sakamakon binciken.

Tasirin ruwan sama

Hukumar kula da yanayi ta Indiya (IMD) ta yi hasashen cewa za a ci gaba da samun ruwan sama a sassan jihar a ranar Litinin

Aƙalla dabbobi 40 ne kuma suka mutu a lamarin.

A wani saƙo da ya wallafa a dandalin sada zumunta na X, Ministan Harkokin Cikin Gida Amit Shah ya ce ya yi matuƙar baƙin ciki da mace-mace.

Gujarat ba ta saba da ganin bala'o'in ruwan sama ba. A watan Agustan shekarar 2020, mutum 14 ne suka mutu a jihar cikin kwanaki biyu kacal a wasu al’amura da suka shafi ruwan sama da kuma ambaliya.

Yayin da ambaliyar ruwa da walƙiya ke kashe mutane da yawa a Indiya a kowace shekara, masana kimiyya sun yi gargaɗin cewa hauhawar yanayin zafi a duniya na haifar da bala'in yanayi mai tsanani.

TRT World