Wani dan bindiga ya bude wuta a wani rukunin shaguna a arewacin birnin Dallas da ke Jihar Texas ta Amurka.
Hukumomi a kasar sun tabbatar da cewa dan bindigan ya harbe mutum takwas amma ‘yan sanda sun harbe shi inda ya zama na tara.
Mutane da dama sun samu rauni kuma tuni aka kai su asibitoci da ke kusa, kamar yadda suka tabbatar.
“Mun samu mutum bakwai da suka rasu a wurin da lamarin ya faru. Mun kai mutum tara asibiti... Cikin wadanda muka kai, tuni biyu suka rasu,” in ji shugaban hukumar kashe gobara na Allen da ke Dallas, Jonathan Boyd.
Wasu daga cikin wadanda suka rasu har da kananan yara da ba su wuce shekara biyar ba, kamar yadda kafar watsa labarai ta CNN ta ruwaito.
Dan bindigan, wanda hukumomi suka ce suna kyautata zaton ya yi gaban kansa, wani dan sanda ya harbe sa a lokacin da ya soma harbi bayan ya fito waje daga rukunin shagunan, kamar yadda shugaban ‘yan sanda na birnin Brian Harvey ya bayyana a taron maneman labarai.
Jami’an tsaro da farko sun yi zaton akwai dan bindiga na biyu a rukunin shaguna na Allen Premium Outlet mai nisan kilomita 40 daga Dallas, kamar yadda CNN ta ruwaito.
‘Yan sanda sun ta bincike a cikin rukunin shagunan, inda hotuna da kuma bidiyo da jirgi mara matuki ya dauka daga wurin sun nuna yadda kwastamomi da ma’aikatan shaguna suke gudu zuwa wurin ajiye motoci.
Bidiyo daga kafafen watsa labarai na Amurka sun nuna ‘yan sanda na ta gaggauta fitar da masu siyayya daga rukunin shagunan, da kuma jerin motocin ko-ta-kwana a ajiye a kofofin shiga wurin.
Ana iya ganin jini a hanyar da jama’a ke tafiya da kuma fararen kyallaye sun lullube wasu abubuwan da ake zaton gawarwaki ne.
Bidiyon da ya karade shafukan sada zumunta wanda kemarar cikin mota ta dauka ya nuna yadda mutumin ya fito daga cikin motarsa a wajen rukunin shagunan sa’annan ya soma bude wuta kan jama’a.
An ji ya yi harbi fiye da sau talatin a lokacin da motar da ke daukar bidiyo take dauka inda direban motar kuma ke kokarin tsira.