Shugabannin ƙasashen duniya 24 sun hallara a ƙasar Rasha a ranar Talata don buɗe taron kwanaki uku na ƙungiyar BRICS, na kawancen ƙasashe masu tasowa da ke fatan ganin Kremlin za ta kalubalanci "mulkin Ƙasashen Yamma".
Mecece BRICS?
Ƙasashen Brazil da Rasha da Indiya da kuma China ne suka kafa ƙungiyar ta raya tattalin arziki a shekarar 2009 inda a hukumance suka yi maraba da Afirka ta Kudu cikin ƙungiyar a sherakar 2009, kana suka faɗaɗa sunanta zuwa BRICS wanda ke nuna harafin farko na sunayen ƙasashen biyar.
BRICS dai ta kuɗuri aniyyar kalubalantar karfin ikon Amurka da wasu Ƙasashen Yamma a duniya.
Cikin sauri ta faɗaɗa bayan Iran, da Masar da Habasha da Hadadiyyar Daular Larabawa suka shiga cikin watan Janairu. Kazalika Turkiya da Azerbaijan da Malaysia da sun gabatar da takardar neman shiga.
Me ya sa BRICS ke da mahimmanci?
BRICS tana da burin faɗaɗa muryar manyan ƙasashen masu tasowa don ƙalubalantar tsarin duniya da ƙasashen yamma ke jagoranta. Mambobin da suka kafa ta sun yi kira kan a samar da tsarin adalci a duniya da kuma gyara cibiyoyin ƙasa da ƙasa kamar Majalisar Dinkin Duniya, da Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF) da Bankin Duniya.
Tare da ƙarin sabbin mambobi huɗu a wannan shekara, a yanzu ƙungiyar za ta kunshi kasashe tara kenan, wadanda ke kara taka rawa a tattalin arzikin duniya.
Ƙasahshen ƙungiyar BRICS sun ƙunshi kashi 30 cikin 100 na faɗin ƙasa a duniya, da kuma kashi 45 cikin 100 na yawan al'ummar duniya sannan da kashi 45 na yawan arzikin man fetur da ake hakowa a duniya.
A tare, suna sauƙaƙe kusan kashi ɗaya bisa huɗu na kasuwancin duniya.
Wasu muhimman batutuwa ne taron na Rasha zai fi mayar da hankali a kai?
Manyan batutuwan da ke cikin ajandar sun haɗa da matsayar Shugaban Rasha Vladmir Putin na tsarin biyan kuɗi da kungiyar BRICS ke jagoranta ga abokiyar hamayyarta SWIFT, cibiyar hada-hadar kuɗi ta ƙasa da ƙasa da aka cire bankunan Rasha daga ciki a shekarar 2022, da kuma tashe-tashen hankula da suka mamaye yankin gabas ta tsakiya.
Rasha dai ta bayyana taron a matsayin gagarumin mataki na diflomasiyya da zaitaimaka mata kulla kawance don kalubalantar "mulkin kasashen yamma".
Gabanin taron, Firaministan Indiya Narendra Modi ya yaba taron yana mai kiransa da "abokan haɗin gwiwa na musamman" tsakanin Moscow da New Delhi, ya kuma ce za a tattauna kan batutuwan da suka shafi sauyin yanayi a cikin ajanda.