Antonio Guterres ya yi alla-wadai da ƙazancewar rikici a Gabas ta Tsakiya. / Hoto: Reuters

Ƙungiyar Tarayyara Afirka, haɗe da gamayyar ƙasashe 104 mambobin Majalisar Ɗinkin Duniya, sun yi tir da matakin da Isra'ila ta ɗauka na ayyana Babban Sakataren MDD Antonio Guterres a matsayin "wanda ba ta maraba da shi."

Gamayyar ta bayyana ƙaƙƙarfan goyon baya ga Guterres a wata sanarwa da ta fitar ranar Juma'a.

Sanarwar, wadda ƙasashen suka saka wa hannu, ciki har da Turkiyya, sun soki matakin da Ministan harkokin Waje na Isra'ila Yisrael Katz ya sanar, kuma sun jaddada cewa yi wa Guterres wannan laƙabi na "wanda ba a maraba da shi" zai lahanta ayyukan MDD.

"A Gabas ta tsakiya, wannan zai ƙara jinkiri wajen kawo ƙarshen rikici, da kafa tsayayyiyar hanyar assasa ƙasashe biyu, inda ƙasar Falasɗinu da Isra'ila za su yi rayuwar maƙwabtaka cikin lumana da tsaro, daidai da ƙudurorin MDD," cewar sanarwar.

Cikakken ƙwarin gwiwa

Sanarwar ta ce ƙasashen 104 sun jaddada goyon bayansu da kuma ƙarfin gwiwa kan jagoran MDD da ayyukan da yake.

"Muna da ƙarfin gwiwa kan sadaukarwarsa kan zaman lafiya da tsaro, da nuna kishi kan dokokin duniya, ciki har da ɗaukaka matsayin dokokin jin-ƙai, da sauran ƙudurorin Majalisar Ɗinkin Duniya dangane da yanayin da ake ciki a Gabas ta Tsakiya".

Sanarwar ta kuma nemi a girmama jagorancin MDD da ayyukanta.

"Muna kira ga duka ɓangarori su kaucewa ayyukan da za su raunanan babbar rawar Majalisa Ɗinkin Duniya wajen warware rikici, kuma su tallafa wa shirye-shiryen da ke taimaka wa zaman lafiya mai ɗorewa a Gabas ta sakiya," cewar sanarwar.

Haramta shiga

A kwanan nan Isra'la ta ayyana Guterres a matsayin "wanda ba a maraba da zuwansa" kuma ta haramta masa shiga ƙasarta. Matakin ya biyo bayan neman da Guterres ya yi na tsagaita wuta nan-take a Gabas ta Tsakiya.

Isra'ila ta zargi Guterres da gazawa wajen ambatar sunan Iran, ko fitowa fili ya soki gwamnatin Tehran kan hannunta a hare-haren roka na kwanan nan.

Guterres ya yi tir da ta'azzarar rikici a Gabas ta Tsakiya kuma ya nemi a gaggauta tsagaita wuta, amma kai-taye bai ambaci rawar da Iran ta taka ba.

TRT Afrika