Sojojin Isra'ila sun tursasa wa Falasdinawa fita daga Masallacin Kudus (AA)

Sojojin Isra'ila sun sake kai hari Masallacin Kudus a karo na biyu, inda suka dinga dukan Falasdinawan da ke ibada a ciki, sa'o'i bayan sun kai harin farko kan masallacin, na uku mafi tsarki a Musulunci, abin da ya jawo Allah-wadai a fadin a duniya.

Ganau sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na Turkiyya, Anadolu, cewa a ranar Laraba da daddare ne sojojin Isra'ilan suka kai hari sashen ibada na Qibli da ke cikin Masallacin Kudus din bayan idar da Sallar Asham, suka dinga harba gurneti tare da dukan Falasdinawa masu ibada a wajen.

Kazalika Kungiyar ba da agaji ta Palestinian Red Crescent Society a Birnin Kudus ta ce tawagar ma'aikatan lafiyarta sun duba Falasdinawa shida da aka jikkata a cikin masallacin, inda aka garazaya da biyu daga cikin su asibiti.

'Yan sandan Isra'ila sun shiga harabar masallacin inda suka yi kokarin korar masu ibada ta hanyar amfani da gurneti da harsasan roba, a cewar Waqf.

Ganau sun ce masu ibadar sun yi ta jifan 'yan sandan Isra'ila. Har yanzu 'yan sanda ba su komai ba kan lamarin.

Tun da fari a ranar Laraba, dakarun Isra'ila sun yi ta dukan masu zanga-zanga ba tausayi, tare da kama fiye da mutum 350 a masallacin, lamarin da ya janyo kai hare-haren sama da harba rokoki, tare da fargabar abin ka iya yin muni.

Wani Bafalasdine da ya shaida lamarin Abdel Karim Ikraiem mai shekara 74, ya ce 'yan sandan Isra'ila dauke da hayaki mai sa hawaye da gurneti sun kutsa kai cikin masallacin "ta karfin tsiya suka yi wa mata da mazan da ke ibada a wajen duka."

Wani bidiyo da ya yadu a soshiyal midiya ya nuna yadda 'yan sanda ke tumurmusa mutane a kasa a cikin masallacin.

Kungiyar Palestinian Red Crescent ta ce ta duba mutum 37 da aka jikkata, ciki har da wadanda aka sake bayan kama su.

Ministan Tsaro na Isra'ila mai ra'ayin rikau Itamar Ben Gvir, ya "nuna matukar goyon baya" ga abin da 'yan sandan suka yi.

'Masallacin Kudus iyakarmu ne da ba a ketarewa'

Abin da Isra'ilan ta yi ya jawo yin tur da Allah-wadai a fadin duniya.

Turkiyya ta yi tur da aikin Isra'ilan, inda Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya ce Isra'ila "ta ketare iyaka."

"Kutsawa cikin Masallacin Kudus zarta iyakarmu ne," ya fada, ya kara da cewa "Za mu ci gaba da goyon bayan 'yan uwanmu Falasdinawa da kare darajojinmu a kowane irin yanayi."

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres "ya kadu" da ganin hotunan yadda sojojin Isra'ila suke dukan mutane a cikin masallacin, musamman ganin cewa abin ya faru ne a lokaci mai matukar muhimmanci ga Musulmai da Kiristoci da Yahudawa, da ya kamata a ce ana zaune lafiya, a cewar mai magana da yawunsa.

Mai magana da yawun Kwamitin Tsaro na Fadar White House John Kirby, ya ce Amurka "ta damu matuka kan rikicin da ake ci gaba da yi, kuma muna rokon dukkan bangarorin biyu da su guji abin da zai kara ta'azzara lamarin."

Rikicin da ya samo asali ne tun gwamman shekaru da suka shude bayan da mamayar da Isra'ila ta yi wa yankunan Falasdinwa ya yi ta karuwa, tun bayan kafa gwamnatin Firaminista Benjamin Netanyahu.

Zuwa yanzu mamayar Isra'ila ta jawo asarar rayukan Falasdinawa 91 da Isra'ilawa 15 da kuma dan Ukraine daya.

TRT World