Isra'ila na ci gaba da kashe Falasɗinawa a Gaza waɗanda akasarinsu yara ne da mata / Photo: AA

1732 GMT — Sojojin Isra’ila sun ce suna ci gaba da kutsawa Rafah da tsakiyar Gaza

Sojojin Isra'ila na ci gaba da kutsawa cikin birnin Rafah da ke kudancin Gaza da kuma yankunan tsakiyar yankin a ci gaba da fafatawa da kungiyoyin gwagwarmayar Falasdinu.

A cikin wata sanarwa da sojojin Isra'ila suka fitar, sun ce rundunarsu da ke Givati, wadda ke ƙarƙashin runduna ta 162, sun yi arangama da 'dakarun Falasdinawa a Rafah, inda suka yi ikirarin kashe da dama daga cikinsu, ba tare da bayar da takamaiman adadinsu ba.

A cewar wakilin kamfanin dillancin labarai na Anadolu a birnin da ke kan iyakar Gaza da kasar Masar, tun da sanyin safiya sojojin Isra'ila sun yi ta luguden wuta a unguwar Tel al Sultan da ke yammacin Rafah.

A tsakiyar Gaza, sojojin Isra'ila a runduna ta 99 su ma sun ci gaba da kai hare-hare a yayin da jiragen yaki da manyan makaman atilare suka ci gaba da buɗe wuta a yankin

0717 GMT — Harin Isra'ila ya kashe Falasɗinawa da dama a Nuseirat

Wani hari ta sama da Isra'ila ta kai sansanin gudun hijira na Nuseirat da ke tsakiyar Gaza ya kashe Falasɗinawa da dama, kamar yadda kafafen watsa labarai na ƙasar suka tabbatar.

Akwai mutane da dama da suka jikkata sakamakon wannan harin, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na WAFA ya tabbatar.

Majiyoyi daga ɓangaren kiwon lafiya sun bayyana cewa harin ta sama da Isra'ilar ta kai ya shafi sassa da dama a daidai lokacin da Musulmai ke ci gaba da bikin Babbar Sallah.

0331 GMT — Sojojin Isra'ila sun ce sun kai hari kan Hezbollah a kudancin Lebanon

Sojojin Isra’ila sun ce jiragensu sun kai hari wasu wurare da mayaƙan Hezbollah suke a kudancin Lebanon.

Wata sanarwa da sojojin suka fitar ta ce jirgin yaƙin ya kai hari kan wani ginin Hezbollah na soji da ke yankin Aitaroun.

Sanarwar ta kuma ce sun kai hari kan wani ginin soji a ƙauyen Ayta ash Shab da kuma Chaqra da ke kudancin Lebanon.

0315 GMT — Dubban 'yan Isra'ila sun fito zanga-zangar ƙin jinin gwamnatin Netanyahu

Dubban ‘yan kasar Isra’ila sun taru a kan tituna kusa da majalisar dokokin kasar a birnin Kudus domin nuna adawa da gwamnatin Firaminista Benjamin Netanyahu tare da neman a gudanar da zaben da wuri tare da musanya fursunoni da kungiyar Hamas.

Masu zanga-zangar sun cika titunan da ke kusa, dauke da tutocin Isra'ila da kuma hotunan fursunonin Isra'ila da ake tsare da su a Gaza. Wasu alamu da suka rinƙa ɗagawa sun nuna Netanyahu an yi masa alamar “X” da launin ja. da kuma rubutun “Mugun Aljani” a cikin harshen Hebrew da Ingilishi.

Masu zanga-zangar sun yi ta rera taken "A kawo ƙarshen gwamnati mai yaudara," "Zabe a yanzu," "Maciya amana" da "Kunya," kamar yadda wakilan Anadolu wasu gani a lokacin da suka sa ido a kafafen yada labaran Isra'ila wadanda suka yaɗa zanga-zangar kai tsaye.

TRT Afrika da abokan hulda