Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya sauka a birnin New York domin halartar Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 78.
Ranar Asabar shugaban na Turkiyya ya samu tarba daga wurin wakilin Turkiyya a Majalisar Dinkin Duniya Sedat Onal, Jakadan Turkiyya a Amurka Hasan Murat Mercan da kuma Babban Jami'in Turkiyya a ofishin jakadancinta da ke New York Reyhan Ozgur a filin jirgin saman John F. Kennedy.
Tawagar da shugaban kasar ya tafi da ita ta hada da mai dakinsa Emine Erdogan, Ministan Harkokin Waje Hakan Fidan, Ministan Kudi Mehmet Simsek, Ministan Makamashi Alpaslan Bayraktar, Ministan Cinikayya Omer Bolat da kuma shugaban Hukumar Leken Asiri ta kasar Ibrahim Kalin, da sauransu.
Erdogan zai gabatar da jawabi ga Babban Taron na Majalisar Dinkin Duniya ranar Talata.
Ana sa rai jawabinsa zai mayar da hankali kan matakai daban-daban da Turkiyya ta dauka, daga batun ci-gaba zuwa bayar da tallafin jinkai da kuma rawar da take takawa wurin samar da zaman lafiya a duniya.
"Kazalika za mu bayyana rawar da Turkiyya take takawa game da kalubalen da duniya take fuskanta a halin da ake ciki," in ji Erdogan a hirarsa da manema labaraI gabanin ya bar Istanbul.
Ganawa da Turkawa mazauna Amurka
Haka kuma zai gudanar da taro da Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya (MDD) Antonio Guterres da takwarorinsa a gefen Babban Taron na MDD.
Bugu da kari, Erdogan zai gana da Turkawa mazauna Amurka da kuma tattaunawa da wakilan kungiyoyin gudanar da bincike da 'yan kasuwar Amurka.
Ana sa rai fiye da shugabannin kasashen duniya150 ne za su halarci taron na bana.
Erdogan zai ci gaba da ganawa da mutane da gudanar da harkokinsa zuwa ranar Laraba.