Mohammed bin Salman ya ce ya kamata Saudiyya ta mallaki makamin nukiliya kamar yadda Iran ta yi./Hoto: AA

Yarima mai jiran gadon sarautar Saudiyya Mohammed bin Salman ranar Laraba ya ce masarautar kasar tana aiki domin kyautata alaka da Isra'ila.

Bin Salman ya musanta rahotannin da ke cewa an samu tsaiko game da wannan batu ne saboda Isra'ila da Falasdinawa sun ki amincewa su sauya matsayinsu game da wasu abubuwa, yana mai cewa ana gudanar da "sulhu mai kyau".

"Muna fata za a kai wani matsayi da zai saukaka rayuwar Faladinawa, da kuma bai wa Isra'ila damar kasancewa mai ruwa da tsaki a lamuran Gabas ta Tsakiya," in ji yariman a hira da gidan talbijin na Fox News. "Kullum muna kara samun kusanci."

Saudiyya ta dage cewa dole ne duk wani yunkuri na daidaita alaka da Isra'ila ya hada da bai wa Falasdinu 'yanci na zama kasa mai cin gashin kanta, matakin da Isra'ila ta yi fatali da shi ya zuwa yanzu a yayin da gwamnatin kasar mai tsattsauran ra'ayi take ci gaba da gine-gine a Gabar Yammacin Kogin Jordan da ta mamaye.

Kazalika rahotanni na cewa Saudiyya tana neman Washington ta sanya hannu kan yarjejeniyar samar da tsaro, da ta hada da sayar mata da makamai na zamani da taimaka mata a shirin bunkasa makamashin nukiliya kafin ta yarda ta kyautata alaka da Isra'ila.

Isra'ila da Saudiyya suna matukar adawa da Iran, kuma bin Salman ya ce idan birnin Tehran ya samu makamin nukiliya "mu ma ya kamata mu samu."

Rahotanni sun ce bin Salman yana neman zille wa dokokin Amurka wadanda suka takaita batun mallakar makamin nukiliya inda ya ce yana so su mallaki makamin ne domin ayyukan zaman lafiya.

Isra'ila ce kadai kasar da ke da makamin nukiliya a Gabas ta Tsakiya, ko da yake ta sha nanata tabbatar da mallakar makamin ko musanta hakan.

AA