Kimanin mutum miliyan 120 ne yaƙi da tashe-tashen hankula da kuma cin zarafi suka tilasta wa barin matsugunansu, a cewar Majalisar Dinkin Duniya inda ta bayyana adadin mafi yawan 'yan gudun hijira da aka taɓa samu a matsayin ''mummunan yanayi na halin da duniya ta tsinci kanta a ciki''.
Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (UNHCR) ta ce adadin mutanen da aka tilasta wa yin gudun hijira a duniya ya wuce misali, inda rikice-rikice a wurare kamar Gaza da Sudan da kuma Myanmar suka kara yawan mutanen da suka rasa matsugunansu.
A yanzu haka adadin mutanen da suka rasa matsugunansu a duniya ya yi daidai da yawan mutanen Japan, in ji sanarwar.
''Yaki na ɗaya daga cikin manyan dalilan da suka sanya mutane ƙaurace wa matsugunansu,'' kamar yadda Shugaban 'yan gudun hijira na Majalisar Dinkin Duniya Filippo Grandi ya shaida wa manema labarai a ranar Alhamis.
A ƙarshen shekarar da ta wuce, mutum miliyan 117.3 ne suka rasa matsugunansu, a cewar rahoton UNHCR.
'Ya zuwa ƙarshen watan Afrilun bana, adadin ya ƙaru, inda MDD ta ƙiyasta cewa mutum miliyan 10 a duniya ne suka yi gudun hijira.
An samu ƙarin mutum miliyan 110 a cikin shekara ɗaya sannan a tsawon shekaru 12 adadin ya yi ta ƙaruwa -- kusan ninki uku daga shekarar 2012 a sabbin rikice-rikice da kuma gaza warware wasu da aka dade ana fama da su, in ji UNHCR.
Grandi ya shaida wa kamfanin dilancin labaran AFP cewa ya kaɗu matuƙa da yawan mutanen da suka rasa matsugunansu a lokacin da ya karɓi aikin shekaru takwas da suka gabata.
Tun daga lokacin adadin ya yi ta ƙaruwa ''fiye da ninki biyu'', in ji shi yana mai bayyana hakan a matsayin ''mummunan yanayi na tuhumar halin da duniya ta tsinci kanta a ciki''.
Adadin zai yi ta ƙaruwa
Grandi ya yi nuni kan yawan tashe-tashen hankula da kuma yadda sauyin yanayi ke yin tasiri kan hijirar mutane da kuma rikice-rikicen al'umma.
A bara, UNHCR ta ayyana yanayin gaggawa 43 a fadin ƙasashe 29 - fiye da ninki huɗu daga wanda aka saba gani a shekarun baya, kamar yadda ya shaida wa manema labarai.
Musamman, Grandi ya bayyana ''yadda ake take dokokin kasa da kasa a yayin rikice-rikice kana ''a mafi yawan lokuta manufar ita ce tsorata al'umma''.
'Ko shakka babu hakan na ba da gudunmawa mai yawa wajen yin hijirar mutane.''
"Sai dai idan watakila an samu sauyi a fagen siyasar duniya, amma abin takaicin shi ne, adadin na ƙara yawa a zahiri," in ji shi.
Daga cikin mutum miliyan 117.3 da suka rasa matsugunansu a ƙarshen shekarar 2023, mutum miliyan 68.3 sun rasa matsugunansu ne a ƙasarsu ta asali, in ji rahoton na ranar Alhamis.
Adadin 'yan gudun hijira da sauran mutane da ke buƙatar kariyar kasa da kasa ya karu zuwa mutum miliyan 43.4, a cewar rahoton.
UNHCR ta yi fatali da batun da cewa dakkan 'yan gudun hijira da sauran baƙin haure suna ƙaura zuwa ƙasashe masu arziki.
"Yawancin 'yan gudun hijirar suna samun mafaka ne a ƙasashen da ke makwabtaka da nasu, inda kashi 75 cikin 100 na zama a kasashe masu karamin karfi da matsakaita wadanda a tare suke samar da ƙasa da kashi 20 na kudaden shiga na duniya," in ji rahoton.
'Iftila'in ɗan'adam
Yaƙin basasar Sudan na zama yanayi mafi girma da ya ƙara haifar da yawan adadin mutanen da suka yi gudun hijira.
Tun lokacin da yaƙi a Sudan ya barke a watan Afrilun 2023 tsakanin janar biyu a ƙasar da ke gaba da juna, ya raba fiye da mutane miliyan tara da muhallinsu, 'ya zuwa ƙarshen shekarar 2023 'yan Sudan mutum miliyan 11 ne suke gudun hijira, in ji UNHCR.
Har yanzu adadin na ɗaɗa karuwa.
Grandi ya yi nuni kan mutane da dama wadanda har yanzu suke kan gudun hijira zuwa makwabciyar ƙasar Chadi, wadda ta karbi 'yan Sudan kimanin mutum 600,000 a cikin watanni 14 da suka wuce.
"A kowace rana daruruwan mutane ne suke tsallaka wa daga ƙasar da ke fama tashin hankali zuwa ɗaya daga cikin kasashen mafi fama da talauci a duniya," kamar yadda Grandi shaida wa AFP.
A Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo da Myanmar, akwai miliyoyin mutane wadanda suka rasa matsugunansu a bara sakamakon kazamin fada aka yi ta gwabzawa.
Kazalika a Gaza, Majalisar Dinkin Duniya ta yi kiyasin mutane miliyan 1.7 -- kashi 75 cikin 100 na al'ummar kasar -- sun rasa matsugunansu sakamakon yakin Isra'ila da ya fara a watan Oktoban 2023.
Game da yakin da ake ci gaba da yi a Ukraine tun bayan mamayar Rasha a watan Fabrairun 2022, Majalisar Dinkin Duniya ta kiyasta cewa kusan mutane 750,000 ne suka rasa matsuguninsu a cikin ƙasar a bara, inda a ƙarshen shekarar 2023 jimullar mutane miliyan 3.7 ne suka rasa matsuguninsu .
Adadin 'yan gudun hijirar Ukraine da masu neman mafaka ya karu daga mutum sama da 275,000 zuwa mutum miliyan shida, in ji rahoton.
Har yanzu Syria ita ce ke kan gaba a cikin ƙasashen da suke da matsalar 'yan gudun hijira a duniya, inda aka tilastawa mutane miliyan 13.8 barin matsugunansu a ciki da wajen ƙasar, in ji rahoton UNHCR.