Mummunar zaftarewar ƙasa ta afku a tsaunukan Papua New Guinea, in ji jami'an yankin da wasu ƙungiyoyi, kuma ana fargabar mutuwar mutane da dama.
Ibtila'in ya afku a ƙauyen Kaokalam da ke lardin Enga mai nisa a ƙasar ta Papua New Guinea da misalin ƙarfe 3:00 na daren Juma'ar nan.
Gwamnan lardin Peter Ipatas ya shaida wa kamfanin labarai na AFP cewa an samu babbar zaftarewar ƙasa da ta janyo "asarar rayuka da dukiya".
Hotunan da aka fita sun nuna yadda ɓangaren ƙasa da duwatsu suka faɗo daga tsaunuka masu tudun gaske.
An samu ramuka masu girman da motoci kan iya faɗawa, inda bishiyoyi suka faɗi.
Ana iya ganin ɓaraguzan gidajen kwano da suka baje a yankin da ibtila'in ya faru.
Ba a san adadin waɗanda lamarin ya rutsa da su ba
Mutane da dama da haɗa da maza da mata na bincika wajen suna kuka suna neman 'yan'uwansu da ƙasa ta danne.
Wasu sun zama masu aikin ceto nan-take, sun saka manyan takalma, sun ɗaura cocilan a kawunansu, sun ɗauki adduna da dogayen gatarai don taimaka wajen kwashe ɓaraguzai.
A yayin da suke motsawa, ana jin kukan yaran da ke bayan iyayensu mata.
"Zaftarewar ƙasar ta afku da misalin ƙarfe 3:00 na dare kuma sama da gidaje 100 sun baje a ƙasa. Har yanzu ba a san takamaiman adadin mutanen da suke cikin gidajen ba," in ji Vincent Pyati, shugaban ƙungiyar Ci gaban Jama'ar Yankin yayin tattaunawa da AFP.
Masu bayar da agajin gaggawa ciki har da ƙungiyar Red Cross ta Papua New Guinea da CARE sun tabbatar da samun labarin afkuwar lamarin amma suna ta ƙoƙarin samun ƙarin bayanai.
Yankin yana yawanc fuskantar mamakon ruwan sama.
A bana ma an samu ruwan sama sosai da ambaliya.
A watan Maris, aƙalla mutane 23 ne suka mutu sakamakon zaftarewar ƙasa a lardin da ke kusa da wannan.