An ji wata kara mai karfi kuma ana iya ganin wani hayaki yana tashi sama daga yankunan kudancin birnin Beirut na kasar Lebanon kamar yadda ganau suka ce.
An bayyana cewa an kai harin ne a kusa da hedkwatar Majalisar Shura ta Hizbullah da ke Haret Hreik.
Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta kai hare-hare a Beirut a matsayin ramuwar gayya kan harin da aka kai a Tuddan Golan da aka mamaye.
Sojojin sun yi ikirarin kai harin ne kan kwamandan da ya kai harin.
TRT World