Hotunan sojojin Isra'ila a lokacin da suke kutsa kai Lebanon. / Photo: Reuters

Rundunar sojin Isra'ila ta fara dakatar da jami'anta da dama da suka ce za su daina aikin soji da yaƙi a Gaza har sai gwamnati ta amince da yarjejeniyar musayar fursunoni don dawo da Isra'ilawar da aka yi garkuwa da su gida.

"Dakatar da sojojin, ciki har da manya biyar da ke matsayin jiran ko-ta-kwana, ta fara ne a 'yan kwanakin nan ta hanyar kiran waya ga dukkan waɗanda suka sanya hannu a madadinsu - ciki har da kiran da aka yi wa sojan da ke aiki a Gaza," in ji jaridar Haaretz a ranar Talata.

"Ɗaya daga cikin waɗanda suka sanya hannun ya faɗa wa wani soja cewa manyansa sun nemi ya sanya hannu a wasiƙar, amma ya ƙi yin hakan," in ji jaridar.

Wani soja kuma ya bayyana kiran wayar da 'barazana', inda wani kuma ya ce kwamandan bataliyarsu ne ya yi kiran waya mai tsayi, wanda hakan ya janyo aka dakatar da shi, in ji jaridar.

Mummunar tattaunawar Netanyahu

Rahoton na Haaretz ya ƙara da cewa a makon jiya ne sojoji 130 suka sanya hannu kan wata wasiƙa inda suka sha alwashin ba za su ci gaba da aikin soji ba har sai gwamnati ta amince da tsagaita wuta a Gaza tare da tabbatar da an yi musayar fursunonin da ke tsare.

An rubuta wasiƙar ga Firaminista Netanyahu, ministoci, da shugaban rundunar soji Herzi Halevi.

Isra'ila ta yi ƙiyasin akwai mutanenta 101 da ake tsare da su a Gaza, inda Hamas kuma ta ce an kashe mutanen a hare-haren kan mai-uwa-da-wabi da Isra'ila ta kai yankin.

Yunƙurin shiga tsakanin da Amurka, Masar da Qatar ke yi don tsagaita wuta a Gaza da musayar fursunoni tsakanin Isra'ila da Hamas ya ci tura saboda Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ƙi dakatar da yaƙi inda yake ci gaba da kawo sabbin sharuɗɗa.

Sharuɗɗan sun haɗa da karɓe iko da Hanyar Philadelphi da ke tsakanin Gaza da Masar, fita ta ƙofar Refay da hana mayaƙan Falasɗinawa dawowa arewacin Gaza ta hanyar tantance masu dawowa ta hanyar Netzarim.

Hamas ta nace cewa lallai Isra'ila ta janye gaba ɗaya daga yankin kafin ta amince da wata yarjejeniya.

Ci gaba da kisan kiyashi

Tun bayan harin 7 ga Oktoban 2023 Isra'ila ta fara kai hare-hare Gaza tana aikata kisan kiyashi, duk da kiran tsagaita wuta da Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya ya yi.

Ta kashe fiye da mutane 42,300, galibinsu mata da yara, kana ta jikkata fiye da 99,000 a yaƙin.

Hare-Haren Isra'ila ya raba kusan dukkan jama'ar Gaza da matsugunansu a yayin da ƙawanyar da aka yi musu ta janyo ƙarancin abinci, ruwan sha mai tsafta, da magunguna.

Isra'ila na fuskantar tuhumar aikata kisan kiyashi a Kotun Ƙasa da Ƙasa.

TRT World