Iran, wacce ta sha alwashi yin ramuwar gayya, ta ƙaddamar da hare-hare a Isra'ila a watannin baya-bayan nan a yayin da Isra'ila tale ci gaba da yaƙin kisan ƙare-dangi a Gaza. / Hoto: TRT World

Isra'ila ta ƙaddamar da jerin hare-hare ta sama a "wuraren aikin soji" na Iran, kuma kafar watsa labaran gwamnatin Iran ta tabbatar da jin ƙarar fashewar abubuwa sannan ta ce wasu daga cikin ƙarararrakin an ji su ne daga na'urorin kakkaɓo makamai da ke Tehran babban birnin ƙasar.

Babu bayani game da ɓarnar da hare-haren waɗanda aka kai da sanyin safiyar Asabar suka yi a Iran sai dai kafofin watsa labaran ƙasar sun rawaito cewa an "ji manya ƙararraki" a Tehran da yankuna da ke gefensa sakamakon hare-hare ta sama.

Rundunar sojojin Isra'ila ta bayyana hare-haren a matsayin na "yankan-shakku da aka kai kan wuraren aikin sojojin Iran."

"Gwamnatin Iran da ƙawayenta sun riƙa kai hare-hare a Isra'ila tun 7 ga watan Oktoba 7 — a ɓangagori bakwai — ciki har da harin kai-tsaye daga ƙasar Iran," a cewar wata sanarwa daga rundunar sojoji Isra'ila.

"Kamar kowace ƙasa mai cin gashin kanta a duniya, Ƙasar Isra'ila tana da damar mayar da martani."

Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta "shiga cikakken shiri" na kare kanta. Mai magana da yawun rundunar sojojin ƙasar Rear Admiral Daniel Hagari, a wata sanarwa da ya fitar, ya yi kira ga al'ummar Isra'ila su "su sanya idanu kan abubuwan da ke wakana a kewayenku".

Ba a kai hare-hare a tashoshin nukiliya ba, in ji kafar watsa labarai ta NBC News and ABC News , wadda ta ambato wani jami'in Isra'ila yana bayyana hakan.

Kamfanin dillancin labarai na Iran Fars ya ce Isra'ila ta kai hari kan sansanonin soji da dama a kudanci da kudu maso yammacin Tehran.

Kamfanin dillancin labarai na Tasnim ya ce an kai hari a sansanin sojojin Islamic Revolutionary Guard Corps amma ba a yi musu ɓarna ba.

Yiwuwar kai hare-haren ramuwar gayya daga Iran

Iran, wadda ta sha alwashin yin ramuwar gayya, ta ƙaddamar da hare-hare biyu da makamai masu linzami a Isra'ila a watannin da suka gabata a yayin da Isra'ila take ci gaba da yaƙin kisan ƙare-dangi a Gaza tun watan Oktoban 2023. Kazalika Isra'ila ta ƙaddamar da hare-hare na mamayar Lebanon.

Harin da Isra'ila ta kai wa Iran ranar Asabar na zuwa ne jin kaɗan bayan Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ya koma ƙasarsa bayan ya kammala balaguro a Gabas ta Tsakiya inda shi da wasu jami'an Amurka suka gargaɗi Isra'ila kada ta kai harin da zai ta'azzara rikicin da ake yi a Gabas ta Tsakiya da kuma tashoshin nukiliya.

A gefe guda, na'urorin Syria na kakkaɓo makamai sun "kakkaɓo" wani makami a kusa da Damascus da sanyin safiyar Asabar, a cewar kamfanin dillancin labarai na SANA.

"Na'urorinmu na kakkaɓo makamai ta sama sun tare wasu makamai a sararin samaniyar kusa da Damascus," in ji wani saƙo da SANA ya wallafa a shafin Telegram bayan jin ƙarar "fashewa" a babban birnin Syria.

TRT World