Makami mai linzami na P-270 Moskit dan asalin kasar Soviet na da karfin da zai iya lalata jirgin da ke da nisan kilomita 120/ Photo jaridar Ma'aikatar tsaron Rasha / AP

Ma'aikatar Tsaron Rasha ta ce jiragenta biyu sun yi nasarar harba wasu makamai masu linzami da ke lalata jiragen ruwa a Tekun Japan.

A wata sanarwa da ta Ma'aikatar Tsaron ta wallafa a shafinta na Telegram a ranar Talata, ta ce "An yi nasarar harba makaman gwajin a yankin abokan gaba."

Ma'aikatar ta ce an gudanar da atisayen ne a mashigin ruwan Tekun Peter da ke Tekun Japan amma ba ta bayar da cikakkun bayanai ba.

Tekun wanda ke kan iyaka da hedkwatar jiragen ruwa na Fasifik na kasar Rasha a Fokino yana da tazarar kilomita 700 daga tsibirin Hokkaido na arewacin Japan.

Ya zuwa wannan lokaci Ma'aikatar Tsaro ta Japan ba ta ce komai ba kan wannan batu. Kazalika Rundunar Sojin Ruwaa Amurka ta bakwai ba ta bukaci a mayar da martani kan lamarin ba.

Harba makaman na zuwa ne mako guda bayan da wasu jiragen yakin Rasha biyu dauke da makaman nukiliya, suka yi ta shawagi a Tekun Japan sama da sa'a bakwai, matakin da Moscow ta ce wani shiri ne.

Tun a watan Satumba Japan ta nuna rashin amincewa da atisayen sojin kasa da kasa da ake gudanarwa a tsibirin Kuril da ke karkashin ikon Rasha, guraren da Japan ta yi ikirarin nata ne.

Sannan ta nuna damuwarta kan jiragen ruwan Rasha da China da ke gudanar da atisayen harbe-harbe a kan tekunta.

Ko a bara sai da Rasha ta yi gwajin harba makami mai linzami a cikin Tekun Japan.

TRT World