Saeed Jalili [Dama] yana kan gaba yayin da Massoud Pezeshkian yake biye da shi kamar yadda sakamakon farko na zaɓen ya nuna, amma babu wanda ake hasashen zai yi nasara kai-tsaye / Hoto: Reuters

Iran za ta gudanar da zaben shugaban kasa zagaye na biyu domin maye gurbin marigayi Shugaba Ebrahim Raisi, kamar yadda wani jami’i ya tabbatar bayan da aka kada kuri'ar farko da aka ce manyan 'yan takarar ba su samu nasara ba.

Za a gudanar da zaben zagaye na biyu a ranar 5 ga watan Yuli inda a halin yanzu za a fafata tsakanin Masoud Pezeshkian da tsohon mai shiga tsakani na nukiliya Saeed Jalili.

Mohsen Eslami, wanda shi ne mai magana da yawun hukumar zaɓen, shi ya sanar da sakamakon a wani taron manema labarai da gidan talabijin na Iran ya watsa a ranar Asabar.

Ya ce daga cikin kuri'u miliyan 24.5 da aka kada, Pezeshkian ta samu miliyan 10.4 yayin da Jalili ya samu miliyan 9.4. Kakakin majalisar ƙasar Mohammad Bagher Qalibaf ya samu miliyan 3.3. Mostafa Pourmohammadi ya samu kuri'u sama da 206,000.

An soma fitar da sakamakon zaɓen ne bayan an shafe awanni 18 ana kaɗa ƙuri'a.

Kakakin hedkwatar hukumar zaɓen ƙasar Iran, Mohsen Eslami, ya ce an kammala jefa ƙuri'a ne da tsakar dare a agogon ƙasar.

An soma kaɗa ƙuri'a ne ranar Juma'a da misalin ƙarfe 8 na safe sannan aka ce za a kammala zaɓe da ƙarfe 6 na yamma, kamar yadda kundin tsarin mulkin ƙasar ya tanada.

Sauyi a harkokin siyasar Iran

Sai dai sau uku Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida ta ƙasar, wadda take da alhakin gudanar da zaɓen, ta tsawaita lokacin jefa ƙuri'a.

'Yan takara huɗu ne suke neman shugaban ƙasar — Mohammad Baqer Qalibaf, Jalili, Pezeshkian da Mostafa Pourmohammadi — bayan rasuwar Ebrahim Raisi sakamakon hatsarin jirgin helikwafta a watan jiya.

An ƙiyasta cewa mutum kimanin miliyan 64 suka cancanci kaɗa ƙuri'a a zaɓen shugaban Iran, galibinsu kuma matasa ne. A zaɓen shugaban ƙasa na 2021, mutum miliyan 59.3 suka cancanci kaɗa ƙuri'a.

An ajiye akwatunan zaɓe kimanin 58,640 a faɗin ƙasar domin sauƙaƙa wa mutane kaɗa ƙuri'a, kuma akwatu 6,000 daga cikinsu an ajiye su ne a Tehran.

TRT World