Isra'ila ta tsare ƙarin ɗaruruwan Falasɗinawa bayan ƙaddamar da yaƙin Gaza ranar 7 ga watan Oktoban 2023. / Hoto: AA

1223 GMT —Falasɗinawa sama da 9,600 na tsare a gidajen yarin Isra'ila

Falasɗinawa aƙalla 9,623 ne suke tsare a gidajen yarin Isra'ila daban-daban, kamar yadda alƙaluma suka nuna.

An tsare Falasɗinawa 3,379 ba tare da an tuhume su da aikata wani laifi ba a dokokin Isra'ila sannan an bayyana Falasɗinawa 1,402 a matsayin waɗanda aka tsare ba bisa ƙa'ida ba, a cewar ƙungiyar kare hakkin ɗan'adam ta Isra'ila HaMoked, wadda ta ambato wasu alƙaluma daga Hukumar Gidajen Yarin Isra'ila.

"Wulaƙancin da Isra'ila take yi wa waɗannan mutane ya keta haƙƙoƙinsu na mutuntaka da samun ilimi da makamantansu, sannan ya saɓa wa dokokin ƙasashen duniya," in ji HaMoked.

1001 GMT — Adadin Falasɗinawa da Isra'ila ta kashe a Gaza ya kai 37,900

Isra'ila ta kashe Falasɗinawa sama da 37,900 sannan ta jikkata kimanin 87,060 tun da ta ƙaddamar da hare-hare Gaza ranar 7 ga watan Oktoba, a cewar Ma'aikatar Lafiya ta Gaza.

Isra'ila ta kwashe watanni takwas tana luguden wuta Gaza inda ta ɗaiɗaita yankin. / Hoto: AFP

0705 GMT — Daraktan Asibitin Al Shifa na cikin Falasɗinawa 50 da Isra'ila ta sako

Rundunar sojojin Isra'ila ta saki daraktan Asibitin Al Shifa da ke Birnin Gaza bayan ya kwashe fiye da watanni bakwai a tsare sakamakon samamen da sojoji suka kai asibitin a watan Nuwamba da ya wuce.

Dr. Mohammed Abu Salmiya na cikin Falasɗinawa 50 da aka saka a faɗin iyakar gabas ta tsakiya da kudancin Gaza.

An kama shi ne ranar 23 ga watan Nuwamba tare da ma'aikatan kiwom lafiya da dama da ke tafiya a kan Titin Salah al Din daga Birnin Gaza zuwa kudancin yankin bayan sojojin Isra'ila sun kai hari Asibitin Al Shifa.

Bayan sakinsa, ya bayyana halin da gidan yari yake ciki a matsayin "mafi muni a tarihin Falasɗinu, inda ake fama da ƙarancin abinci da fuskantar wulaƙanci."

Ya jaddada buƙatar ɗaukar matakin gaggawa na kuɓutar da dukkan Falasɗinawa da ke tsare a gidajen yarin Isra'ila, yana mai cewa ba a taɓa fuskantar wahala irin wannan ba tun daga lokacin Nakba.

An kai mutanen da aka sako Asibitin Al Aqsa Martyrs da ke Deir Al Balah da Asibitin Nasser da ke Khan Younis. / Hoto: AFP

0716 GMT — Sojojin Isra'ila sun ce sun kai hari kan yankunan Hezbollah ta kudancin Lebanon

Rundunar sojojin Isra'ila ta ce ta kai hari ta sama da kuma luguden wuta da makaman atilari da daddare a yankunan da Hezbollah ke da ƙarfi a garuruwan kudancin Lebanon.

Wata sanarwa da rundunar ta fitar ta ce: “Da daddare, sojoji sun kai hari a yankunan da Hezbollah suke a kudancin Lebanon, inda suka lalata kayan sojinsu a yankin Kfarkela da na'urorinsu a yankunan Houla, El Biyada, da Rab El Thalathine na kudancin Lebanon.”

“An kai hari da makaman atilari don kawar da duk wata barazana a yankin Al Dahira da ke kudancin Lebanon,” a cewar sanarwar.

Kawo yanzu, Hezbollah ba ta ce komai game da sanarwar ba

0159 GMT — Falasɗinawa sun yi watsi da buƙatar kafa rundunar duniya don tafiyar da harkokin Gaza

Ofishin shugaban ƙasar Falasɗinu ya fitar da wata sanarwa da ke watsi da buƙatar kafa wata runduna ta duniya don gudanar da harkokin Gaza kamar yadda Isra'ila ta yi kira a yi.

“Babu wata ƙasar duniya da take da hurumin sanya ƙafafunta a Yankin Falasɗinu, kuma al'ummar Falasɗinu ne kawai suke da ikon tafiyar da harkokinsu,” in ji Nabil Abu Rudeineh, kakakin fadar shugaban Falasɗinu.

Ranar Lahadi, Hukumar Watsa Labarai ta Isra'ila ta ambato wata majiya da ba ta faɗi sunanta ba tana cewa sojojin Isra'ila za su ci gaba da zama a Gaza har sai an kafa wata rundunar ƙasashen duniya domin maye gurbinta, lamarin da zai ɗauki watanni da dama kafin ya tabbata.

TRT Afrika da abokan hulda