Daga Fadi Zatari
Harin da Ƙungiyar Hamas ta kai kan Isra'ila ranar 7 ga watan Oktoba, za a ci gaba da ɗaukar shi a matsayin abin da ya sauya al'amurra a tarihin baya bayan nan, na ƙungiyar fafutikar ta Falasdinawa.
Tsarawa da kuma aiwatar da irin wannan harin a kan ƙasar da sojojinta suka fi kowaɗanne cigaban fasahar zamani a duniya, ba ƙaramin aiki ba ne, idan aka yi la'akari da ƙarancin kayan aiki da Hamas ke fama da shi.
Harin ya kawar da shaci-faɗi da kuma kallon da ake yi wa Isra'ila, a matsayin ƙasa mai ƙarfin da ba za a iya kai mata hari ba.
Harin na 7 ga watan Oktoba, ba shi ne mafarin rikicin Isra'ila da Falasdinawa ba. Akwai dalilai da suka saka ƙungiyar fafutikar ta Falasdinawa ta yanke shawarar mai cike da tarihi, ta ƙaddamar da wannan harin da ba kasafai ake ganin irinsa ba.
Daga cikinsu akwai kisan ƙare-dangi da kisan-kiyashi da Isra'ila ke yi wa al'ummar Falasdinawa, mummunan take haƙƙin bil adama da sojojin mamaya na Isra'ila ke yi, da ƙwace yankunan Falasdinawa,da kuma mafi muhimmanci, ci gaba da mamayar da Yahudawa ke yi wa Birnin ƙudus da kuma masallacin Birnin Ƙudus.
Sakamakon abubuwan da dama da suka faru a yankin da ƙasashen duniya - da suka haɗa da Boren Larabawa, da matsin tattalin arziki, da ɓullar annobar Korona da kuma yaƙin Ukraine - yadda ake watsa labarai da ya shafi Falasdinawa ya sauya sosai daga yadda aka saba gani a baya.
Alal misali, kimanin shekaru Ashirin da suka gabata kenan, da Gaza, wacce aka yi wa ƙawanya, kuma Falasdinawa sama da miliyan biyu ke rayuwa a cikinta, a wani yanayi mai cike da ƙalubale, da ya fi kama da kurkuku, ba ta samu kulawa daga kafofin yaɗa labarai na duniya ba.
Amma harin na 7 ga watan Oktoba na kwanan nan, ya farkar da kafofin watsa labarai na duniya daga barcinsu, sannan ya sake maido da batun Falasdinawa gaba-gaba a tattaunawar yankin da ta ma duniya bakiɗaya.
Ƙaruwar goyon bayan Falasdinawa
Martanin da Isra'ila ta mayar a kan harin na 7 ga watan Oktoba, ya ƙunshi mummunan ta'adi kuma mara iyaka, inda ake ci gaba da nuna damuwa a faɗin duniya, game da cewa, tana aikata kisan ƙare-dangi da kisan-kiyashi ne.
Kisan-kiyashin da sojojin Isra'ila ke yi ya haddasa nuna ɓacin rai a faɗin duniya kuma ya jawo ƙaruwar goyon bayan Falasdinawa, yayin da ake gudanar da manya manyan zanga-zanga a faɗin duniya.
Mummunan harin da Isra'ila ta ƙaddamar kan asibitin Al Ahli Arab dake Gaza, wanda ya halaka ɗaruruwan mutane, ya bayyana ƙarara yadda Isra'ila ke taka dokokin duniya ta hanyar mummunan ta'adin da take yi, wanda ya gaza banbancewa tsakanin gine-ginen fararen hula da na soji, da suka haɗa da asibitoci, da makarantu da kuma majami'u.
Biyo bayan wannan lamarin, dubun dubatan mutane sun fantsama kan tituna a birane daban daban a faɗin Turkiyya, da Masar, da Tunisia, da Jordan, da Lebanon, da Iran, da Qatar, da Indonesiya, da Pakistan, da Bangladesh, da Afrika ta Kudu da kuma Mauritania, inda masu zanga-zangar suka bayyana goyon bayansu ga Gaza.
Har ila yau, an gudanar da manya manyan zanga-zanga a biranen ƙasashen Turai dayawa, inda dubban mutane suka bayyana goyon bayansu ga Falasdinawa masu fama da wahalhalu a Gaza.
A birnin London a ka gudanar da ɗaya daga cikin zanga-zangar mafi girma a Turai, inda sama da mutane 100,000 suka hallara domin bayyana goyon bayansu ga Gaza da aka yi wa ƙawanya.
Zanga-zanga makamantan wannan na goyon bayan Falasdinawa tare da kiran a tsagaita wuta sun gudana a Jamus, da Faransa, da Italiya, da Netherlands, da Switzerland, da Sifaniya da kuma wasu ƙasashe dayawa a faɗin nahiyar.
Amma, a wasu ƙasashen Turai, an yi amfani da jami'an tsaro wajen taƙaici, da haramcin, da kuma amfani da ƙarfin Tuwo domin hana zanga-zangar goyon bayan Falasdinawan. Waɗannan lamurran sun yaɗu har ya kai ga kame da dakatarwa.
Ana gudanar da zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa a wasu ƙasashe kamar Jamus, a ƙarƙashin sa-idon ƴan sanda sosai, kuma ana samun yawan yin amfani da ƙarfin tsiya wajen hana ruwa gudu.
Saɓanin haka kuma, babu irin waɗannan taƙaici ko haramcin da a ke sa wa a kan zanga-zangar goyon bayan Isra'ila.
Masu zanga-zanga da ke allawadai da zalincin da Isra'ila ke yi kan Gaza da aka yi wa ƙawanya, su ma sun fantsama kan tituna a Amurka, da Canada, da Austaraliya.
Washington DC, ya fuskanci zanga-zangar dubban masu goyon baya Falasdinawa, waɗanda suka gudanar da zanga-zanga a gaban fadar White House, suna waƙoƙin "a ƴantar da Falasdinawa" kuma suna ɗaga tutocin Falasdinu da ƙyallaye masu ɗauke da saƙonni kamar "A dena Mamayar" da kuma "Dakatar da wuta yanzu."
Sannan ita ma ƙungiyar Muryar Yahudawa Domin Zaman Lafiya ta gudanar da wata babbar zanga-zanga a birnin New York, Wanda ɗaruruwan ƴaƴan ƙungiyar suka halarta daga al'ummomi Yahudawan Amurka, waɗanda suka bayyana adawarsu da ci gaba da kai hare hare da Isra'ila ke yi a Gaza.
Har ila yau, adawa da munanan hare haren bamabamai a Gaza da Isra'ila ke ci gaba da yi, ya haifar da manyan zanga-zanga a Latin Amurka.
Dubban masu goyon baya Falasdinawa sun shiga zanga-zangar a Brazil, da Venezuela, da Argentina da kuma Chile.
A wani yunƙuri na nuna goyon baya, ƴan rajin kare haƙƙin bil adama a yankin, sun ƙaddamar da kamfen, da tarurruka, da tattaunawa da kuma ganawa ta kafofin sada zumunta, kuma an ɗaga tutar Falasdinawa a garuruwa da dama a faɗin Latin Amurka.
Zanga-zangar da aka gudanar a faɗin duniya gwanin sha'awa sun nuna ƙarara irin goyon bayan da duniya ke yi wa batun Falasdinawa da kuma goyon baya ga al'ummar Falasdinawa a fafutikarsu ta sama wa kansu ƙasa mai ƴanci, yayin da dayawa suka yi mummunar suka ga hare hare ta sama da Isra'ila ke kai wa kan farar hula a faɗin Gaza.
Ƙarin wayewar kai game da abin da ke faruwa a yankunan da aka yi wa mulkin mallaka
Martanin da Isra'ila ta mayar a kan harin da ƙungiyar Hamas ta kai mata ranar 7 ga watan Oktoba mugun ta'adi ne, na mai kan uwa da wabi kuma barkatai, sannan ba ya tantance wa tsakanin inda ya halatta su kai hari da kuma sauran gine-gine kamar asibitoci da makarantu da kuma gidajen jama'a.
Komai da kowa hare haren bamabaman Isra'ila da kuma rufe iyakoki ta sama da ƙasa da ruwa ya shafe shi, abin da ya sa dayawa daga cikin masu goyon bayan Isra'ila ke jan-ƙafa wajen halatta abin da take aikatawa - abin da ya haifar da mummunan rasa ran dubban fararen hula da ba su ji ba ba su gani ba. ,har da ƙananan yara da mata.
A dandalin sada zumunta, dubban ƴan ƙasashen yammacin duniya da Amurkawa, har da al'ummar Yahudawa, waɗanda suke nesanta kansu da Isra'ila ƙarara, da kuma munanan manufofinta kan Falasdinawa ne ke yaɗa fayafayen bidiyon.
Bugu da ƙari, fefen bidiyo da ke nuna Yahudawan Amurka da Turai suna shiga zanga-zanga - galibi a karon farko - na goyon bayan ƴancin Falasdinawa suna samun tagomashi a kafafen sadarwa na zamani.
Daga ƙarshe, farfagandar Isra'ila ta dogara ne da ƙarerayi da munaƙisa, kuma yaudararta da ta fito fili a kwan-gaba-kwan-baya da yin baki biyu a maganganunta masu wahalar sha'ani.
Waɗannan abubuwan sun sa zai yi wahala ainun wani ya aminta da abin da Isra'ila take aikatawa, har ma da maganganunta da ayyukanta na kisan kiyashin.
A maimakon haka, hannayen Isra'ila jagab suke da jinin dubban Falasdinawa da ba su ji ba ba su gani ba.
Duk wannan ana gudanar da shi ne ta hanyar amfani da tsofaffin lafuzan nan dai na daɗin baki na "ba wani sai mu", inda Isra'ila da ƴan Isra'ila ne kaɗai ake wa kallon halattatun "wayayyun halittu", waɗanda suke da ƴancin wanzuwa yayin da ake ƙasƙantar da Falasdinawa sannan a kira su da sunan "dabbobin bil adama" - ƙidahumai, marasa tausayi "da sauransu" waɗanda suka cancanci hukunci mai tsanani ko mutuwa.
Mawallafin, Dr.Fadi Zatari, Mataimakin Farfesa ne a sashen nazarin kimiyyar siyasa da ke Jami'ar Zaim, Turkiyya.
Hattara Dai: Ra'ayoyin da mawallafin ya bayyana ba dole ba ne su zo daidai da ra'ayoyi, hange ko manufofin TRT Afrika.