Nicaragua ta yanke alaƙa da Isra'ila. / Hoto: AP

Nicaragua ta ce ta yanke alaƙa da Isra’ila don nuna goyon baya ga Falasɗinawa.

Gwamnatin ƙasar ta ce an yanke duk wata dangantaka ta diflomasiyya bayan wani matakin bai-ɗaya da Majalisar Dokokin ƙasar ta ɗauka.

Ta ja hankali kan wahalar da Falasɗinawa suke sha saboda hare-haren Isra’ila, sannan ta ce Nicaragua za ta ci gaba da goyon bayan Falasɗinawa da gwamnatinsu, waɗanda ake “rusa su ake kuma nuna musu dabbanci.”

Bayan Allah wadai da ta yi kan kan “kisan ƙare-dangin” da Isra’ila ke yi da miyagun manufofinta kan Falasɗinawa, Nicaragua ta kuma bayyana damuwa kan abin da Isra’ila ke yi a Lebanon da barazana ga Syria da Yamen da Iran. Ta kuma yi gargaɗi cewa matakin na Tel Aviv zai iya dagula zaman lafiyar yankin da ma gaba da shi.

Muguntar Isra’ila

Falasɗinu ta yi maraba da matakin na Nicaragua da ta yanke hulɗar jakadanci da Isra’ila.

Matakin na nuna “dattakon Nicaragua a matsayinta na mamba ta ƙasashen duniya da suke ɗaukan matakai na gaske don tsayar da kashe-kashen da ake ci gaba da yi wa Falasɗinawa da sauran ƙasashe a yankin,” kamar yadda Ma’aikatar Harkokin Wajen Falasɗinawa ta bayyana a cikin wata sanarwa.

Ma’aikatar ta jaddada cewa, matakin “wani martani ne kan kisan da Isra’ila ke ci gaba da yi, da rushe-rushe da rashin imanin da take nuna wa Falasɗinawa a wani gagarumin mataki na ƙare-dangi da aka shafe fiye da shekara guda ana yi.

Ta kuma bayyana fatan cewa matakin na Nicaragua zai zama abin koyi ga ƙasashen da ake ƙawance da su, wanda suma za su ɗauka don martani ga kisan ƙare-dangin da Isra’ila ke ci gaba da yi wa Falasɗinawa.”

TRT World