A yayin da Isra'ila ke ci gaba da tarwatsa Falasdinawa ta hanyar ruwan bama-bamai a Gaza, Firamista Benjamin Netanyahu ya bayyana cewa kasarsa ba za ta taba bayar da dama ga kungiyar gwagwarmaya ta Hamas ta sake karbe iko da Zirin Gaza ba.
Netanyahu na yawan sukar Shugaban Gwamnatin Falasdinu da aka zaba Mahmoud Abbas, sannan yana kalubalantar yarjejeniyar Oslo, yarjejeniyar zaman lafiya da Amurka ta jagoranci sanya hannu a kai shekaru 30 da suka gabata kan warware rikicin Falasdinu.
Gwamnatin ta Falasdinu ta bayyana shirinta na jagorantar Gaza, a matsayin wani bangare na dabarun siyasa, da ke da manufar samun hadin kai tsakanin mazauna Yammacin Gabar Kogin Jordan da aka mamaye da kuma Gabashin Kudus, wanda zai bayar da mafitar siyasa da za ta kai ga kafa 'yantacciyar kasar Falasdin.
Amma a wani martani ga wannan ikirari na gwamnatin Falasdinu na cewa Dakarun Sojin Isra'ila ne suka kashe Falasdinawa a wajen bukin Nova ba wai Hamas ba, Netanyahu ya yi watsi da kalaman na Abbas. "Shi ma ba za mu ba shi dama ya shugabanci Gaza ba".
Kalaman nasa na bayyana yana goyon bayan gwamnatin Abbas ta jagoranci Yammacin Gabar Kogin Jordan.
Matsayin Netanyahu ya ci karo da halin kawance a koyaushe na Isra'ila, shugaban AMurka Joe Biden a baya ya bayar da shawarar gwamnatin Abbas ta shugabanci Gaza da Yammacin Gabar Kogin Jordan bayan yakin Isra'ila da Hamas.
Matsayin netanyahu -- wanda ke jagorantar gwamnati mafi hatsari da tsananin kishin Yahudawa a tarihin kasar Yahudu -- zai janyo gaza samar da sulhun siyasa ta hanyar sanya kasashen duniya su yi shiru tsit.
Manufar a koyaushe ita ce a baiwa gwamnatin Abbas damar jagorantar Yammacin Gabar Kogin Jordan, amma kuma ba tare da wani karfin zartarwa ba.
"A bangaren Isra'ila, ana sukar shugabancin kasar saboda abun da wasu masu nazari suka kira da yunkurin karfafa gwiwar Hamas da kassara gwamnatin Falasdinawa, don hana matsin lambar da ake samu ta neman a kafa 'yantacciyar Falasdinu da kafa Isra'ila," in ji tsohon jami'in diflomasiyya kuma babban mamban Cibiyar Nazari Kan Zaman Lafiya ta Amurka, Hesham Youssef.
"An raunata tare da rage karfin ikon gwamnatin Falasdinawa ta Yammacin Gabar Kogin Jordan (Bayan harin 7 ga Oktoba)"
Sannan babu batun aika sojojin kawance na kasa da kasa zuwa yankin, babu wata kasa da ke son aika sojojinta wannan yanki.
"Waye zai so ya shugabanci Gaza--daya daga cikin wuraren da ya fi tara jama'a a waje guda a duniya--da aka kuma rusa mafi yawan gine-ginensa, wajen da mambobin Hamas za su ci gaba da wanzuwa.
Yankin da sama da kaso 60 na mazaunansa ke rayuwa cikin bakin talauci d arashin samun cimaka kafin bakwai ga Oktoba? in ji James Gelvin, farfesa kan Tarihin Zamani na Gabas ta Tsakiya yayin zantawa da TRT World.
Babu wata kasar Larabawa da za ta yi abun da jama'arta ba sa so, wanda suke goyon bayan Falasdinawa sosai, in ji Gelvin.
Da zarar hankula sun koma ga halin da za a shiga bayan lammala yaki a Gaza, aka fara magance kalubalen jagoranci, sake gine-gine, da yunƙurin samar da 'yantacciyar kasar Falasdinu, bangarorin da abun ya shafa za su zama a yanayin rashin samun zabin da suke so.
Matsayin Isra'ila game da gwamnatin Falasdinawa da ke Yammacin Gabar Kogin Jordan da Hamas na dagula al'amura kan waye zai jagoranci yankin Gaza da ke cike da jama'a bayan an gama yakin.
Hamas ko gwamnatin Falasdinawa da ke Yammacin Gabar Kogin Jordan?
Babban bambancin da ke tsakanin manyan masu taka rawa a siyasar Falasdinu, gwamnatin PA da Hamas shi ne, yadda kowanne bangare yake tunkarar matsala d abukatun Falasdinawa.
Gwamnatin Yammacin Gabar Kogin Jordan ta fi bayar da muhimmanci hadin kai da Isra'ila, inda Hamas kuma take daukar matakan amfani da karfin soji.
Goyon bayan da ake baiwa gwamnatin PA a Yammacin Gabar Kogin Jordan ya ginu a doron alakar ba ni in ba ka da Isra'ila, duk da dai wani bangare nasu na daukar makami a yankin.
A yayin da PA ke jagorantar Falasdinawa a Yammacin Gabar Kogin Jordan, ana mata kallon mai rauni kuma mara tasiri.
Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ya bayar da shawarar yiwuwar 'Sake Dawo da Karfin PA' zuwa Gaza lokaci mai zuwa.
Sai dai kuma, Gelvin na kallon wannan ba abu ne da zai tabbata ba.
Ya ce "Idan 'ya Isra'ila da Amurkawan da ke goya musu baya suka gaza gano haka a kan lokaci, watakila amsa daya ita ce ko dai Isra'ila ta bijirewa Amurka ta ci gaba da daidaita Gaza, ko kuma ta fice daga yankin baki daya, saboda ta gama karar da al'ummar arewacin Gaza."
Ta hakan, 'yan Isra'ila za su iya kaucewa yanayin da Labanan ta taba fadawa na mamayar kasashe tsawon shkaru 20, sannan su kyale rikicin Gaza ga kasashen duniya."
Warware Rikicin Ta Hanyar Kafa Kasashe Biyu??
Akwai imanin cewa masu tsaurin ra'ayi da ke kewaye da Netanyahu ne suke ingiza ganin ba iya Hamas kawai za a karar ba, har da dukkan al'ummar Falasdinawa.
Ministan Leken Asiri Gila Gamliel, duk da rasa ikon aikinta na leken asiri, ta rubuta wata makala a jaridar jerusalem Post inda take tattauna yiwuwar gudun hijirar Falasdinawa daga Gaza.
Wata kuri'ar jin ra'ayin jama'a da Cibiyar Mitvim Mai Binciken Manufofin Kasashen Waje da na Yankuna ta gudanar a watan Nuwamba, ta bayyana ra'yoyi daban-daban game da yakin Falasdin da halin da Isra'ila ke ciki.
Kaso saba'in na wadnad asuka amsa tambayoyin na goyon bayan a warware rikicin ta hanyar kafa kasashe biyu na Falasdin da Isra'ila.
Kaso ashirin da biyar kuma na da ra'ayin lallai Isra'ila ta janye daga yankin Yammacin Gabar Kogin Jordan kawai ba tare da kulla wata yarjejeniya da Falasdinawa ba.
Kaso biyar ne kawai suka amince da a ci gba da gwabza yaƙi, suka bayyana ra'ayi irin na Firaminista Netanyahu, sannan kaso 28 sun maince da mamaya, suna nuna bukatar fadada kasar Isra'ila a yankunan da ba nata ba.
Kaso 52 kuma na da ra'ayin lallai Isra'ila ta janye daga dukan yankunan Falasdinawa. Ficewar na iya daukar salo daban-aban, ko ta hanyar tattaunawa ko ba tare da hakan ba, kamar yadda ta yi a Gaza a 2005.
Ƙwararru na bayyana cewa wannan ce kawai hanyar samun mafita.
"Ba za a iya warware wannan rikici da karfin soji ba, kuma idan ana son warware shi ta hanyar siyasa, dole sai Isra'ila ta fita daga Gaza da ke karkashin ikon Falasdinu," in ji Storer H. Rowley, wani kwararre kan Gabas ta Tsakiya kuma editan jaridar Tribune.
Rowley ya fada wa TRT World cewa "Dole ne wadanda za su maye gurbin gwamnatocin Hamas da Netanyahu su kasance masu son warware rikicin ta hanyar kafa kasashe biyu."