An raba wa jama’a Alƙur’ani da aka fassara da harshen Dutch a ƙasar Netherlands a wani shiri na ƙarfafa gwiwar ’yan ƙasar kan su riƙa karanta littafai masu tsarki maimakon ƙona su.
Shirin yana zuwa ne wata guda bayan jagoran ƙungiyar PEGIDA wanda ke ƙyamar Musulunci ya wulaƙanta Alƙur’ani.
Galip Aydemir, shugaban Gidauniyar Masallacin Arnhem Türkiyem wanda ke haɗin gwiwa da Gidauniyar Dutch Diyanet, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu cewa suna ƙoƙarin isar da saƙo ga jama’a kan abin da ya sa addinin Musulunci da Alƙur’ani suke da daraja ga Musulmai.
Muna so a samu haɗin kai da ’yan'uwantaka tsakanin mazauna birnin Arnhem, in ji shi, inda ya ƙara da cewa: “Ya kamata a daina ƙona Alƙur’ani da sauran littafai masu tsarki, a riƙa karanta su ne.”
John Maters, wani ɗan Netherlands wanda ya samu kwafin Alƙur’anin ya yi godiya ga waɗanda suka shirya taron kuma ya soki waɗanda suka jagoranci wulaƙanta Alƙur’ani a watan da ta gabata.
“Abin da ya faru watan da ya gabata zai sa mutane su kara ƙin junansu ne. Ba na tunanin cewa sai mutumin da ya damu da addini zai fahimci cewa hakan rashin hankali ne,” in ji shi.