Adadin wadanda suka rasu sakamakon wutar dajin Maui ta Jihar Hawaii a Amurka ya kai 93, kamar yadda shafin intanet na yankin Maui ya bayyana.
Rahotanni sun bayyana cewa wannan wutar dajin ita ce mafi muni da ta faru a sama da shekara 100 a Amurka, inda ake fargabar adadin wadanda suka rasu zai karu.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa irin barnar da wutar dajin ta yi ta fito fili ne kwanaki hudu bayan da wutar dajin ta lashe wani wurin hutu na tarihi wato Lahaina, inda ta kona gidaje da narkar da motoci.
Kudin da za a kashe wurin sake gina Lahaina ya kai dala biliyan 5.5, kamar yadda Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Amurka (FEMA) ta bayyana, inda ta ce akwai sama da gine-gine 2,200 da suka kone ko suka lalace, inda kuma sama da kadada 2,100 ta kone.
Gwamnan Jihar Hawaii Josh Green ya yi gargadi a wani taron manema labarai a ranar Asabar kan cewa adadin wadanda suka rasu zai ci gaba da karuwa a daidai lokacin da ake gano karin wadanda lamarin ya rutsa da su.
Karnukan da aka horar domin gano gawarwaki sun yi aiki a kashi uku ne kacal cikin 100 na wurin da ya kamata a bincika, kamar yadda shugaban ‘yan sanda na Maui, John Pelletier ya bayyana.